YADDA ZAKA ZABI MATAR AURE


YADDA ZAKA ZABI MATAR AURE

Akwai hanyoyi da dama da ake zabin matar aure domin yin rayuwa, ga kadan daga cikin su kamar haka:

Yin dacen samun abokiyar rayuwa me nagarta babbar nasarace a Wannan zamanin da muke ciki.

Idan ka samu kuwa matukar zata soka irin sonda kake mata ko fiyeda haka tabbas abokiyar zama ce, abunda ya rage shine ka rike ta da kyau.
Matukar zata faranta maka rai toka riketa hannu bibbiyu 

Duk Budurwar dazaka furta mata kalmar so, kaima ta maidama da furucin kauna Abokina ka riketa da muhimmanci, Zamanin mu ya canja samun kamar su wuya gareshi. 

Yadsa zaka Zabi Matar Aure

Abokina idan Allah ya baka mace mai tsoron Allah wacce zata kusanto ka da alkairi sannan ta nisanta ka da sharri tabbas wannan itace matar aure.

Duk budurwar dazata baka kulawa ta musamman sannan tayi abunda kakeso, tabar abunda bakaso to wlh irinsu sunada wuyar samu ka Rike abarka da kyau. Mace Abokiyar rayuwa ce ni'imace kuma haske ce dake haska rayuwar duk namiji.

Dacewa a soyayya shine kasami mace tagari, wacce tasan mutumcin ka tasan nata mutumcin wacce zata karema mutumcin ta da naka ako yaushe. 


Sannan kasani mace yar'adam ce kuma tana kuskure duk lokacin da tayi ba daidaiba kayi mata uzuri ka fahimtar da ita ta hanyar dazata fahimceka.


Muna baka shawari idan zaka zabi mata, to ka zabi mai addini yafi domin haka addinin mu yayi mana umarni.

Wannan nasiha ce akan Soyayya, duk mai Ζ™arin bayani mu hadu a comment, muna Godiya Agareku masoyan wannan shafi www.Qauna.com.ng Muna Alfahari daku.

Previous Post Next Post