ABUBUWA 12 DA ZA KAYI KA SAMU SOYAYYAR MACE

  ABUBUWA GUDA 11 DA ZAKA YI KA SAMU SOYAYYAR MACE


Zan Lissafo Abubuwa guda 10 da ko wace mace take so, amma basa iya tambaya dan ayi musu, amma idan kana yiwa Budurwar ka, zata soka fiye da tsammanin ka.


1. Ka kira ta da Safe, ka tambayeta ya take, sannan ka faɗa mata yadda kake son ta, sannan ka mata addu'a mai daɗi.


2. Kada ka mata ƙarya: mata basa son namiji wanda yake musu ƙarya. Komai tsakanin ku ka faɗa mata gaskiya. Sannan kasan hanun ka!3. Kana nunawa abokan ka cewa kana son ta sosai, musamman a idon ta. Kana yabon ta a wurin abokan ka idan tana wurin zata ji daɗi.

4. Ka tabbatar duk wata matsala tata Kana ƙoƙari wajen magance mata, koda bakada iko kayi naka ƙoƙarin.Yadda ake sace zuciyar mace


5. Kana Nuna godiyar ka a fili idan tai maka alheri wato kyauta.


6. Kana Yawa Janyo abunda zai sa kuna jinawa kuna hira, mata suna son ana basu labarin abun dariya.


7. Kana Yawan Bata Kyauta Musamman kayan Kwaɗayi wato Ƙwalama8. Hangout with her and your friends together and hold her hand in public.

9. Ka nuna mata Baka da kowa sai ita, Kana Tina Mata Alkawarin dake tsakanin ku na soyayya da riƙon amana.


10. Kada Kana yawan fishi Idan kuna hira, ko da wasa ne zata ɗauka da gaske kake.

11. Ka nuna mata idan tana tare dakai Tana cikin tsaro da kuma gata, komai zaka iya yi mata.

Muna Godiya.
Previous Post Next Post