ABUBUWA 10 DA MATA KE SO
GOOD MORNING/NIGHT TEXTS.
Ko wace Mace tana son namiji wanda zai ke tashi da ita a zuciyar shi kuma yana tinawa da ita yayin da zai kwanta da Shauƙi. Turawa mace Saƙo Da Safiya yana ƙara mata ƙarfin Shauki da soyayyar ka acikin zuciyar ta.
HIRA MAI TSAWO (DEEP LONG CONVERSATION.)
Zuciya Tasan Inda yakamata a aje ta. Ko wace Mace tana son namijin da zak so ta da gaske kamar yadda zata so shi da gaske. Jimawa Kuna Hira Ta Waya ne ko ta zahiri wata hanya ce da zata baku damar fahimtar junan ku sosai, tanan ne zaku san menene kuke so menene bakwa so, sannan Yana ƙara muku Shauƙin soyayya, sannan tanan zaku gane irin ƙarfin soyayyar da kuke wa junan ku.
IDAN TAYI KWALLIYA KA ÆŠAUKE TA HOTO, KO KU ÆŠAU HOTON TARE.
Wannan yana da muhimmanci saboda kowannen mu yana son mutumin da zai so shi kuma yana mishi abunda zai saka shi nishaÉ—i. Hoto yana bada Gudummawa sosai acikin soyayya saboda yana bada damar tinawa da lokacin farin ciki. Taking pictures is very important to make her feel loved.
SURPRISES (KYAUTAR BAZATA)
Duk Ƙanƙantar Abu mai daɗi ko mai kyau Yana da amfani a soyayya. Dan ƙaramin abu idan ka bawa mace zai sa taji daɗi sosai. Kuma zai sakamata Shauƙin tinawa dakai Sosai domin mace bata mantuwa da garaje. Ka siya mata wani abu mai ɗaukar hankali kamar flowers, chocolates da sauran abunda ka fahimci tana son irin su wannan zai sa kana samun shimfiɗar fuska koda yaushe.
KANA TINA MATA YADDA KAKE SON TA A KO WANI LOKACI.
Muna Jin daɗi idan wasu suka faɗa mana yadda suke ƙaunar mu da irin Muhimmancin da muke dashi agaresu. Kana Faɗa mata yadda kake ƙaunar ta, Dakuma Dalilin daya saka kake ƙaunar ta shine komai.
KANA SAMA MATA LOKACI
Duk Irin Busy da zaka shiga Kayi ƙoƙarin Samun wani lokaci saboda wacce kake so hakan zai ƙara sa mata Muhimmancin ka a zuciyar ta, kuma zata ji ta ƙara son ka, hakan yana saka mace taji cewa itace kawai a zucka.
RESPECT HER (KA GIRMAMA TA)
Soyayya Yana haÉ—uwa ne idan akwai Kyakkyawar Fahimta. Idan kana son ta, ka Girmama ta, ka Aminta Da ita, dakuma iyayen ta.
Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA
RANDOM KISSES. (KANA YAWAN MATA KISS A HANNU)
Wannan wata hanya ce da zaka saka mace ta Wuni tana Tinanin ka, domin ka nuna mata matuƙar soyayya wato maƙura. Ko wace mace tana son saurayin ta yana zuwa mata da abubuwan mamaki.
KADA KA YAUDARETA KO KAYI MATA ƘARYA
Mata Suna Son Namiji mai gaskiya wanda bazai cutar dasu ba. Wanda yake tsayuwa akan magana É—aya baya canja fuska.
Karanta: 40-ROMANTIC-LOVE-TEXT-MESSAGES
KANA YAWAN MURMUSHI IDAN KA KALLE TA.
Yawan Murmushi wa mace yana saka taji cewa lallai tana burge ganin ka. Kuma zaisa ta rinƙa maka abubuwa da kake so domin kayi farin ciki.
Muna Godiya da Irin Goyon Bayan Da Kuke Bamu. Kada Ku Manta ku duba ƙasa Kuyi Subscribe.
Tags
Love Enlightenment