SIRRIKAN ZAMAN AURE DAKE KARA KARFIN SOYAYYA

SIRRIKAN ZAMAN AURE DAKE ƘARA ƘARFIN SOYAYYA

Akwai Sirrikan Zaman Aure da Ba kowa yake da sani akan su ba, amma yau zamu kawo Kaɗan daga cikin su,Domin a karanta su Cikin Natsuwa;


1. Yin adalci dole ne a wurin miji ga matan da suke da yawa wajen mazauni, tufafi, abinci da abubuwan masarufi. Amma a bangaren sadaki, walima da ƙauna, ba lallai ne ya zama dai-dai ba, ana iya samun bambanci. 
   Ƙauna da So suna samun asali ne saboda; hankalin mace, kyawun ta, kuɗin ta, ko matsayin iyayenta, da sauran su, don haka sai dai abi a hankali kar a fada cikin halaka!


    Don haka adalci dole ne a tsakanin mata da Ƴaƴa, idan mutum bazai iya yin adalcin ba, sai ya tsaya ga mace ɗaya, kamar yadda Aya ta nuna, [Nisa'i 03]. 
   Mace ɗayan ma dole ne a kiyaye mata haƙƙoƙinta, idan ba haka ba asha azaba. Sirrin Zaman Aure
2. Yin ado da kwalliya wa mace haƙƙi ne, don kada hankalinta ya karkata zuwa ga mazajen dake waje.

3. Yin wasanni, sake fuska, tattaunawa da hira Haƙƙi ne mai tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma'aurata, kamar yadda aka samo cewa Annabi (SAW) yana wasa da matayensa, yana hira dasu, yana sake musu fuska. 

4. Dole ne ayi mu'amala mai kyau ga iyalai, hakan shi zai tabbatar da ɗorewar cigaba, kwanciyar hankali da more rayuwar duniya data lahira. Idan suna da yawa zai taimaka wajen sassauta mumnunan kishi da ƙiyayya a tsakaninsu da rigingimun da babu gaira babu dalili. 
        Kiyaye waɗannan hakkoki na mata shine zamantakewa mai kyau da samun arziki da albarka, tare da farin ciki mai ɗorewa.
Previous Post Next Post