YADDA ZAKA DASAWA MACE SOYAYYA A ZUCIYAR TA

0
HANYOYIN DA ZAKA DASAWA MACE SOYAYYAR KA A ZUCIYARTA

Aure, ya zama tamkar wasan yara a wajen Malam Bahaushe saboda rashin martaba shi da ba ayi. 

Sau tari zaka samu da an fara zaman soyayyar take gushewa saboda ma’auratan na kasa kiyaye wasu ginshiÆ™an soyayya da ke ha6aka Æ™auna a zuÆ™atan juna.

Da zaran an fara samun matsaloli nan da can kuma sai kaga duk an fara gunduran juna, Sai dangantaka tayi tsami. Sai rashin kyautatawa ya biyo baya, daga nan kuma sai ka ji ko dai mijin ya furta saki, ko kuma matar ta nemi a saketa saboda zaman yaki daÉ—i.

Wadannan hanyoyi guda 38 in aka bisu sau da kafa zasu dauwamar da soyayyar mata a zuciyar mijinta.
1. Ka zamo mai tausasa zance a gareta, kar ka zamo mai yawan faÉ—a.

2. Idan ka shiga gida kace ‘Assalamu Alaikum’, sallam tana korar SheÉ—an daga gida.


3. Annabi SAW yace mata kamar kayan karau ne saboda haka a kula dasu sosai, ka tuna akwai alkhairi a cikinsu saboda haka sai a tarairaye su.

4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata faÉ—a ya zamo a cikin sirri, wato alokacin da kuke ku kaÉ—ai, kada ya zamo a cikin mutane dan yin hakan muzantawa ne gareta.







5. Ka zama mai kyautatawa matarka, hakan yana ƙara soyayya.

6. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata wurin zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.

7. Ka guji yin fushi ta hanyar riÆ™e al’wala a koda yaushe. Annabin Rahma SAW yace idan kayi fushi to idan a tsaye kake sai ka zauna, idan a zaune kake sai ka kwanta.

8. Ka rinka yin ado kana sa turare saboda matar ka.

Zafafan kalaman Soyayya



9. Karka zamo mai tauri (MaÆ™o), Annabi SAW yace : ‘Nine mafi kyautatawa zuwa ga iyalina’, idan kayi tauri da yawa baza ka samu kusanci zuwa ga Allah ba, haka kuma baza ka zamo namiji jarumi ba.

10. Ka dinƙa sauraron duk abinda matarka zata gaya maka koda kana ganin abin bashi da muhimmanci, hakan zai sa ta san ka damu da ita.

11. Ka kaucewa yin musu da matarka, yana kawo rabuwar kai.

12. Annabi SAW yace ku kira matayenku da sunaye masu daÉ—i, sunan da suke so suji ka kira su dashi.


13. Ka riÆ™a yiwa matarka tsarabar bazata, idan tana sha’awar wani abin marmari sai ka siyo mata ba tare da ta sani ba.

14. Ka kula da harshenka zuwa gareta, wato ka guji abubuwan da zasu sa tayi fushi.

15. Mutum tara yake bai cika goma ba, kayi haƙuri da duk wani aibun da take dashi sai Allah (S.W.T) yasa albarka a cikin auren naku.

16. Ka dinƙa nuna mata yabo da godiya idan tayi maka abu mai kyau.

17. Ka dinÆ™a taimaka mata wajen ganin ta kula da dangantakar Æ´an’uwanta da iyayenta.





18. Ka yawaita janta da fira akan abinda take so.

19. Idan kaga Æ´an’uwanta suna kusa, ka dinga yabonta, kana kambamata, kana tabbatar musu da kirkinta da kyautatawar da take maka.

20. Ku dinƙa yiwa junanku kyaututtuka. Manzon Allah (S.A.W) yace kyauta tana kara soyayya.

21. Idan kayi mata laifi sai ka samu wani abu ka kyautata mata dashi dan ya goge laifin naka.


22. Ka rinka kyautata zato a gareta, banda zargi!

23. Karka dinga kulawa da kananan laifukanta, kayi kamar baka gani ko ji ba. Yana daga cikin É—abi’un Sayyidina Aliyyu (RA).

24. Ka nin-ninka haÆ™urinka da ita musamman a lokacin da take jinin al’ada.




25. Ka rinƙa sauraron zuwan kishin ta, kuma ka ringa yabon kishin nata, ko matan Manzon Allah (S.A.W) suna kishi!

26. Ka zamo mai ƙasƙantar da kai, idan ka zamo mai tunani to ka tuna cewa tana kula da ƴaƴanka, itace mai kula da gida!

27. Karka É—auki abokanka sama da matarka!

28. Ka ringa taimaka mata da ayyukan gida. Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana taimakon matansa.

29. Ka taimaka mata wajen girmama iyayenka, baza ka iya takura mata dan taso su ba amma zaka iya taimaka mata dan ta cimma hakan.


Karanta: ABUBUWAN-DAKE-SA-MATA-DA-MAZA-YAUDARA

30. Ka dinÆ™a nuna mata cewa itace irin matar da kake ta addu’ar ka samu.

31. KarinÆ™a tunawa da matarka a cikin addu’o’in ka, hakan zai kara Æ™arfin soyayyar ku.

32. Kada ka dinƙa tunawa da baya, babu abinda hakan zai jawo sai damuwa, abinda ya riga ya wuce a barwa Allah.

33. Karka taba nuna mata cewa taimaka mata kake yi idan kana mata wani abin kamar sayan abincin gida, saboda a zahirin gaskiya mu ƴan aikatarwa ne kawai, Allah shine yake azurtawa da ciyarwa. Wannan kuma wata hanya ce ta ƙasƙantar da kai ga Allah (S.W.T) da kuma gode masa.


34. Ka gane cewa Shaiɗan maƙiyinka ne amma ba matarka ba, wani lokaci idan mata da miji suna magana idan suka samu sa6ani sai Shaiɗan ya shiga tsakani. Kayi iya ƙoƙarinka wajen ganin Shaiɗan bai shiga tsakaninka da matarka ba.

35. Ka rinƙa bata abinci a baki, Annabin tsira (S.A.W) ya koya mana hakan, abincin ba wai iya cikinta zai tafi ba kawai idan ka bata a baki, har zuwa cikin zuciyarta.

36. Ka kare matarka diga duk wani sharri ta hanyar yi mata addu’o’in neman tsari.

37. Ka zamo me yawan yi mata murmushi Sosai.

38. Ka guji duk abinda bataso komai ƙanƙantarsa, idan baka kula ba ta haka ne zai girma har ya zama babba.

Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)