AMFANIN AUREN BAZAWARA

AMFANIN AUREN BAZAWARA KO MACEN DA TA GIRMEKA 

Kafin mu shiga cikin bayani yakamata mu san shin wacece bazawara, budurwa da kuma wacce ta girmi mijinta.

Bazawara dai ita ce matar auren da suka rabu da mijinta sanadiyyar mutuwa ko kuma rabuwa. Da ƴaƴa ko Babu.

Budurwa kuma ita ce wacce ba ta taba yin aure ba.

Sannan ita kuma matar da ta girmi mijinta ita ce, wacce ta fi mijinta shekaru, wato ta riga shi zuwa duniya.

Mafiya yawan samari ba sa son auren bazawara, amma masana sun yi nuni da cewa, akwai fa’idodi mai yawa game da auren bazawara ko kuma wacce ta girmeka. Ga kadan daga cikin fa’idojin.


Yana daga wasu fa’idodi da namiji zai samu in ya auri matar da ta girme shi ko bazawara kamar haka.

-Na farko zai samu ladan sunna, idan ka yi domin yin koyi da fiyayyen halitta.

– Auren mace wacce ta fi ka shekaru akwai yuyuwar samun ingantacciyar rayuwar aure matuƙar akwai soyayya sakamakon cewa, ita ta zauna da wasu mazan ta san rayuwar aure, ta san mai namiji yake so ta san abin da baya so, ta sami ƙwarewar iya kwanciya da miji, sabo da haka da zarar ka auri irin wannan kuma akwai SO da ƙauna da tarbiyya, to ba ma auren da ya fi shi dadi, sakamakon ta sami Ƙwarewa koda ba ta taba aure ba a bayan shekarun da ta yi a rayuwarta, zai sa ta ga abubuwa kalakala a rayuwarta wadanda za su zama mata darasi a zamantakewar aure nan gaba.

-Haƙiƙa bazawara ta fi budurwa sanin makamar aiki a zamantakewar aure musamman ma in ta sami saurayi wato wanda ta girma, musamman ma a ce akwai soyayya.


Amfanin Auren Bazawara





-Bazawara tana da hakurin zamantakewa fiye da budurwa, domin ita budurwa ta ƙware wajen yaudara.

Bazawara ko wacce ta fi ka shekaru ta san halayen iyayen miji da yadda ake zama da su sabanin budurwa.

-Ayyukan gida, kula da gida, gyaran ɗaki, iya girki da tsaftace shi, kula da yara da sauran su dukkan su bazawara ta fi budurwa ƙwarewa a kai. 



-Daɗin kalamai, kisisina, iya rarrashin miji, rashin katobara yayin zance, daɗin hira duk bazawara ta fi ƙwarewa fiye da budurwa.

-Rashin almubazzaranci da dukiyar Miji ko Barnatar da Dukiyar Miji. Wataƙila ta zauna a inda bekai naka wadata ba, zaka ga tattali.

- Iya Kula da Uwar Miji, Iya Zama da Ƴan uwan miji ko dangin miji. 

Waɗannan kaɗan kenan daga Cikin Abubuwan da Bazawara Tafi Budurwa dasu.
Previous Post Next Post