GAJEREN LABARIN SOYAYYA

0
01. GAJEREN LABARIN SOYAYYA

Anyi wasu masoya guda biyu da sukai soyayya ta gaskiya kuma ta hakika, sunyi soyayya irin soyayyar da kowa ke son irin ta, shakuwar su abar sha’awa, kasancewar su talakawa ne basu damu da abun duniya ba musamman karya da kudi ko wani abu makamancin sa, wannan dalili yasa mutane da dama suke kawowa budurwar nan tayin soyayya saboda kyawu da Allay a hore mata, sannan kuma far ace tamakar daga turai, kuma yawancin masu zuwa mata da soyayya masu hanu da shuni ne, takan kori wasu, wasu kuma sukan kori kansu da kansu domin irin halin da take nuna musu (hausawa suka ce kora da hali) wasu da dama suna bata kudi amma taki karba, wasu idan taki karba su aika gidan su, amma ita soyayyar saurayinta ya dauke mata hankali domin ita tayi nisa da soyayyar shi kuma bata ga abunda zdivai sauko da it aba, bangaren iyayen

su kuwa basu samu wani tangarda ba, sai ma yabo da suke samu domin an samu hadin kai a tsakani kasancewar unguwar su daya kuma sun san juna sosai, kusan tare suka tashi ma’ana soyayyar bata yanzu bace.
Duk wayewar gari yakan kirata a waya tun bayan sallar asuba sukan jima suna hira ta soyayya har sai gari ya gama wayewa, haka zasu wuni suna kirani in kira ka, duk lokacin da zaizo gidan su hira kuwa yakan taho ne da littafi domin suyi karatu dan qarawa juna ilimi na addini sukan dau tsawon lokaci suna tare.

Labaran Soyayya
Watarana iyayen su suka nemi yi musu aure kasancewar ita budurwar batada wani manemi sai wannan saurayin, domin dashi ne ta fara soyayya kuma ta qudiri aniyar shi zata aura indai tana numfashi, bayan iyayen ta sun nemi da ta fada mashi ya turo iyayen shi domin ai maganar aure, budurwar nan tayi farin ciki sosai wanda takai da a wanar ranar kusan wuni tayi ba’a gane kanta saboda murna sannan da bakin ciki, tana murna ne domin maganar da iyayen ta suka fada mata na aure, tana bakin ciki ne domin a wannan ranar basuyi waya da saurayin ta ba, kuma tun safe kiran wayar shi take baya shiga, ta damu matika, domin tunda suke tare bata taba kiran wayar shi taji a kashe ko bai daga ba, tashiga damuwa sosai domin da farko ta dauka ko laifi tai masa kuma bata son bacin ranshi daidai da kwayar zarra, kiran wayar tashi na farko bai daga ba har sau uku daga baya kuma wayar a kashe.Damuwar data nuna a fuskarta ne yasa mahifiyarta zaunar da ita domin tasan meke damunta, saboda bata taba ganin ‘yarta acikin irin wannan yanayin ba, kuma abun ya bata mamaki matika, tayi tayi ta fada mata meke damunta amma bata fada mat aba saboda kunyar ganin ido, tayi mata tambayoyi daba daban amma ina, sai mahaifiyar ta danyi ajiyar zuciya tace ko matsalar soyayya ce? Nan kuwa budurwan nan ta kada kai da alamun eh. Mahaifiyar tayi mata wasu yan dabaru na Magana inda budurwar nan ta zayyana mata komai dake tafiya, Mahaifiyar tata bata ji dadin faruwar haka ba domin tasan zafin da ake ji, amma ta kwantar mata da hankali tare da yi mata nasiha da cewa ta kasance mai yiwa mutane uzuri a rayuwa kada ta yanke hukunci batare da tayi bincike ba, watakila wayar ce ba charge ko ya mantata a gida, duk wannan nasiha da ake mata kunnen ta bai dauka ba, domin hankalinta a tashe yake bata jin dadin duk wani zance dake shiga kunnen ta. 
Haka dai aka Qare wanan wunin kam babu dadi ko fara’a a fuskar budurwar nan, abun har yakai ga Mahaifiyar ta fadawa mahaifin yarinyar nan, shima abun bai mashi dadi ba, yace zai yi bincike ya gani amma abari sai zuwa gobe da safe idan bai kirata ko yazo ba sai ya samu iyayen yaron tunda sukan hadu a masallaci da asuba, haka dai aka qare wannan ranar kam, dare yayi shiru. bayan gari ya waye ne mahaifin wannan yarinya neman mahaifin wannan yaro bayan idar da sallah ta asuba, amma bai zo salla ba, yayi tambaya sai wani makocin shi yake fada masa cewa jiya ma basu ganshi ya fito sallar asuba ba, kuma wunin jiya ma ba’a ganshi acikin anguwar ba!


Gajeren Labari

Wannan Magana da yaji ta daga masa hankali domin tsoron shi ko wani abune ya faru, dattijan unguwar sukai gangami domin zuwa gidan mahaifin yaron nan, bayan sun isa zuwa gidan suka aika akan ya fito amma said an aikan yace ya shiga gidan babu kowa, wannan wannar maganan tafi ta baya ciwo a wurin su, domin anyi zaman mutunci, bai kamata ace mutumin nan zai tashi daga anguwa amma bai sanar dasu ba, dan aikar ya Qara da cewa dakunan a bude suke kuma kayan su yana cikin gidan kofofin dakunan duk a bude, babu wata alama tada nuna cewa sun tashi daga gidan wannan dalili yasa hankalin anguwa ya tashi gaba daya, aka shiga bincike. 

Zamu Cigaba...................

Domin cigaba da karatu ku ziyarci wannan shafin www.Qauna.com.ng

Domin samun wadannan Labarai dama wasu Irin Su Kuyi Subscribe domin samun su da Mun dora
Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)