YADDA ZAKI ZABI MIJIN AURE
WAYE NE MIJIN DAYA DACE?
Kowace mace tana son ta samu mijin daya dace. Babu wacce take son tayi kuskure ko rashin dacen mijin aure wajen zabin abokin rayuwa. Sai ma kaga mutane da yawa suna tsoron yin aure saboda gudun yin Kuskure a zabin miji, basa son suyi zaben tumun dare. Tsoron su gaskiya ne saboda wanda zaki aura zai rayuwa dake ne tsawon rayuwa either positively or negatively.
Idan Ka Tambayi Yawancin akan wani irin Miji suke son su aura, sai kaji abu ɗaya suke faɗa, za kaji abubuwa da dama misali, Namiji Mai Tsoron Allah, wanda zai baki kulawa da sauran su. Idan ka tambayi mazan irin Wannan amsar suma zasu bayar.
Koma wace irin ansa suke bayarwa, akwai abu ɗaya da yazo iri ɗaya. Shine suna son su samu abokin rayuwa mai nagarta ko na ƙwarai. Ra'ayin su ne yazo iri ɗaya duka. Ni da nake wannan Rubutun bazan so nayi Mistake wajen zabin aboki ko abokiyar rayuwa ba.
Amfani da muhimmancin auren Mijin daya dace baya taba zayyanuwa saboda shine farkon abunda ake dubawa wajen neman Mijin aure. Idan kika auri mijin daya dace, Matsalolin ki na aure ya ƙare. Domin zai magance miji su.
WAYE NE MIJI DAYA DACE KI AURA?
1. Wanda Ya Dace Dake.
Idan Aka ce abu ya dace, ana Nufin wannan abun yana da wasu abubuwan da ake buƙata gareshi kuma ya cika ko yana da waɗannan abubuwan, it also means that something is capable, qualified, fit, proper, appropriate for something.
So, the right person is someone who is suitable for you, someone that fits you, your personality, vision, aspirations, value system, belief system etc.
Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA
2. Wanda Zaki Jitu Dashi (Compatible)
Ga Mutane Biyu Da suke so suyi rayuwa ta aminci da juna, dole ne su zama masu jituwa, idan ka sayi sabon kaya to ka sayawa matar ka, idan kika yi abu mai daɗi ki bawa mijin ki. Idan kuna sowa juna abunda kuke sowa kanku wannan zama zai daɗi. Sannan akwai jituwa na Amintuwa, Darajtawa, Mutuntawa, Girmama Dalili, Sanin Darajar Lafiyar juna, Burika Iri ɗaya, Buƙatuwa Iri ɗaya.
Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE
3. Mutum wanda Ya Yadda dake.
Yadda Yana Nufin, Yadda da Ra'ayoyin ki, Ɗabi'un ki, Halayen ki. Mijin da ya dace ki aura shine wanda zai zauna dake da irin halin ki. Misali, kin auri Namiji Mai Son hira da yawa a waje, kekuma kinfi son da yayi sallar isha ya shigo gida, duk haƙurin ki watarana sai kinyi magana. To ku zama masu Ra'ayi iri ɗaya abune mai muhimmanci acikin aure. Duk da yana wahala amma a ƙoƙarta.
4. Wanda Zaina Wasa Dake.
Idan Kika san cewa bayan kin aureshi bazaina wasa dake kamar ƙaramar yarinya ba, bazai na miki wasu abubuwan da zasu baki farin ciki ta fuskar nishaɗi ba, Hajiya Aure fa ba kurkuku bane.
Wasanni acikin aure suna da amfani wajen ƙara danƙon soyayya da shi kanshi auren.
Karanta: YADDA AKE RAGE SHA'AWA
5. Mai Kyakkyawan Hali
Mutum mai Kykkawa Hali ɗaya ne daga cikin mazajen da yakamace ki. Halaye masu kyau, Nagarta, Ilimi sanin yakamata, waɗannan sune ƙashin bayan Aure, Yaudara, cin Mutunci, zagi, kallon banza da sauran su, sune Manyan Maƙiyan Aure.
6. Wanda Zai Tayaki Neman Aljanna.
Na Ƙarahe Kuma Mafi Muhimmanci shine Wanda Zai kaiki zuwa ga aljannar ki.
Abunda ake nufi shine: mutum mai Ilimi na Addini, Mai Ibada, Sanin Yakamat, iya zama da mutane, iya Magana mai kyau. Da sauran su.
Karanta: ABUBUWAN-DA-MAZA-KE-SO-JIKIN-MATA
TAYA ZAKI GANE HALIN NAMIJIN DAKE ƘAUNAR KI???
Hanya ta farko da ake gane halayen namji akwai Sanya Lura da Hankali Yayin da kike mu'amala dashi ta zamantakewar rayuwa. Yau da gobe tana sa a gane halin mutum, mai kyau ko mummuna.
Hanya ta biyu shine Kallon Abokan shi da yake abokantaka dasu. Hausawa sun ce: Zama Da Maɗaukin Kanwa shike kawo farin kai.
Abokan shi idan na kirki ne to lallai zai iya zama na kirki, haka idan na banza ne shi.
Sai mu kula mu saka lura da idon basira tare da neman shawari daga Mutanen da suka girme mu a shekaru ko sanin Rayuwa.
Ina Muku Fatan Alkhairi.🙏🏻