GAJEREN LABARI KASHI NA KARSHE

0
GAJEREN LABARI KASHA NA BIYU

Bayan dogon bincike da aka gudanar a gane da batan da iyayen saurayinnan dashi aka gano cewa lallai ba tafiya sukayi da kansu ba, tafiya dasu akayi ma’ana sacesu akayi, makotanshi da yan uwanshi sun shiga rudani sosai musamman bayan daukan dogon lokaci da yakai har tsawon kwanaki uku babu labarin su.
Acikin kwana na uku tsakiyar dare da misalign kamar karfe 2 na dare aka jiyo dirin mota ta shigo layin, tana shigowa kuma ta fita, lamarin da ba’a saba ji ba cikin anguwar, nan kuwa mutane suka fito domin su san meke tafiya, kowa ya yafito yayin da sukai arba da wasu mutane kwance cikin jinni basa ko motsawa, da zuwar mutanen nan dai dai inda aka kwantar dasu, sai kuwa akai arba da iyayen yaron nan kwance tare dashi yaron, nan kuwa aka nemo mota aka dauke su sai Asibiti, hankalin anguwa dai ya fara kwanciya ganin sun dawo amma kuma an shiga rudani saboda halin da aka gansu aciki, kuma ba’a san suwa sukai musu wannan aika aikan ba. 

Acan gidan su yarinyar nan kuwa hankalinta ne ya qara tashi bayan ta samu labarin abunda ya samu yan uwan saurayinta, tayi tayi abarta taje amma iyayen ta sun hanata zuwa saboda suna tsoron kada wani

abu ya sake faruwa. Amma suna iya kokarin su wajen kwantar mata da hankali amma ita ba wannan ne agabanta ba, damuwa ta lullube ta, koda yaushe tana cikin kuka cikin ‘yan kwanaki kadan duk ta chanja, ta rame, abinci ma bata ci yadda ya kamata. 

Bayan kwana biyu da kaisu asibiti basu farfado ba acikin kwana na uku iyayen yaron suka farfado amma basa gane wadanda ke tsaye akan su, shikuwa wannan saurayin abun nashi yafi tsamari domin Adaren ranar da aka kawo su asibitin nan yace ga garin su, amma an rufe maganar ba’a fadawa iyayen ba, balle Budurwar shi. 
Ana cikin wannan hali yarinyar nan ta sati hanya ta fito daga gida iyayen basu sani ba, babu inda ta tsaya sai asibitin da aka kaishi, ai kuwa abunda ta tarar bai mata dadi ba domin domin yadda taga halin da iyayen yaron nan suke ciki, kuma ta nemi a hadata da yaron nan amma likitocin sun hana domin tsoron su kada ta fadawa iyayen yaron nan domin an boye musu, yan unguwar ne wato makwabtan su ne suka hana su fadawa kowa.

Gajeren Labarin SoyayyaZaune take kusa da Mahaifiyar yaron nan inda han haifiyar take mata tambaya inda yarona, tace mata nima ban sameshi amma likita ya tabbatar mini yana cikin qoshin ranka, sai Mahaifiyar nan tai mata wata tambaya wanda ya sakata cikin tinani, tambayar data mata kuwa cewa tayi: Dama Kinada wani manemi ba dana ba? Tayi shiru na tsawon lokaci sannan tace mata A’a. ta sake tambayarta ko a baya baki taba soyayya da wani ba? Dan jin wadannan tambayoyi fa hankalin ta ya tashi fiye da da, ta bata amsa tace mama nifa bansan kowa ba! tace karya kike, kinada saurayi kuma sunan shi umar, kuma shine dalilin shigar mu wannan halin daga mu har dan mu, dan haka ki tashi ki bamu wuri shigowarki rayuwar dana ba alkhairi bane kuma idan wani abu ya samu dana sai nayi shari’a da iyayen ki.Tana kuka ta fito daga dakin ma jinyatan ta nufi hanyar fita hankalinta a tashe, kafun ta Qarisa kofar fita taga an dauko wata gawa za’a fita da ita lamarin day tsaidata kenan domin ta basu hanya su wuce, yayin da aka dago gawar nan za’a shiga da ita mota, sai iska ya janye mayafin da aka lullube gawar nan ta dai dai fuskar gawar, nan kuwa tayi arba da saurayinta kwance acikin motar gawa, take ta yanki jiki ta fadi a wurin.
Iyayen ta kuma suna gida suna neman ta an rasa ina tayi, domin an duba duk inda yakamata ace tana nan amma ba’a sameta ba, sai Mahaifiyar ta tace wa baban nata yaje asibitin nan ko can tayi domin duba jikin yaron nan, mahaifin yace tabbas zata iya zuwa wannan wurin kuma, ya nufi asibitin cikin hanzari, yana isa asibitin nan kuwa yayi arba an fito da gawar yaron nan an nufi inda za’a mai sutura domin kaishi makwancin sa, beyi wata wata ba ya sa kai cikin asibitin nan domin duba halinda diyar sa take.

Bayan faduwar wannar yarinya jami’an asibitinnan suka dauke ta domin bata taimakon gaggawa, shigar su keda wuya aka kwantar da ita bias gado a sume, a dai dai wannan lokacin kuwa mahaifinta ya shigo wurin yana dubawa, yayin daya zo kan yar tashi hankalin shi ya tashi sosai domin halin daya sameta aciki, kafun likita yazo kanta Zuciyarta ya buga Allah ya dauki rayuwar ta. Qarshen wannan labara kenan

SHARHI: Wannan Yarinya Dai da kuka karanta labarinta yanxu, sunan ta Saleema, akwai saurayin daya taba mata tayin soyayya amma yarinta ya dibeta tayi masa babu dadi ta koreshi, inda shikuma yayi alkawarin cewa sai ya rama, bayan ta fara soyayya da wannan saurayin nata mai suna Ahmad, umar yaji labara inda yayi amfani da kundin sa yayi hayar ‘yan daba suka tafi da Ahmad da iyayen shi sukai musu dan banzan duka sanna shikuma suka harbe shi.
Sako: Wannan Labarin yana nuni ne da irin alhaki da wannan yarinyar ta dauka na iyayen wannan yaro Ahmad bayan WalaQanta Wani saurayi da tayi.
Wa’azi: Ku Daina walaQanta mutane dan kawai bakwa qaunar su, mai makon haka ku karramasu tare da fada musu bakwa son su cikin kalma mai dadi.

Ku kasance da wannan wannan shafin www.Qauna.com.ng domin samun irin wadannan dama wasu labaran.

Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)