YADDA AKE MALLAKE YAR MASU KUDI

0

 YADDA AKE MALLAKE ZUCIYAR ƳAR MASU KUƊI

Samun yaddar mace ƴar me kuɗi ba abu ne mai wahala ba, amma yana Buƙatar himma da Fahimta. Yardar mace ba abune da Za'a sameshi da sauri ba, amma Za'a iya Samun shi ta hanyar bin wasu matakai ma banbanta. Acikin wannan page zamu tattauna akan wasu hanyoyi da zaka bi dan ka samun yarda da Amincewar ƴar me kuɗi.

Ku Sani.

Ƴar Mai Kuɗi fa Kuɗi basa burgeta!!!1. KA ZAMA AMINTACCE ME GASKIYA

Ɗaya daga cikin Abubuwa masu mahimmanci da za kayi ka samu yaddar mace dakuma girmamawar ta shine ka zama Wanda Za'a Amincewa Kuma Mutum Me Gaskiya. Mata Suna son mutum me gaskiya da Amana a Soyayya, So Idan Har ka kasance cikin mutanen da suke da wannan Halin zaka Samu Yardar Mace. Ma'ana Zama mai gaskiya akan dukkan lamuran ka da abunda kake Aikatawa, sannan kar kayi ƙarya ko Yaudara tako ta wani Hali ko Hanya.

Karanta: ABUBUWAN-DAKE-LALATA-SOYAYYA

2. KA ZAMA MAI ƘARFIN GUIWA DA DAURIYA.

Hanya ta Biyu da Zaka Samu Yardar Mace shine Ka Zama Mai Azama da Ƙarfin Guiwa akan Ayyukan yau da Kullum. Sannan ka zama bamai nuna gajiya wa ba. Mata suna son Mutum Mai Tabbas, Sannan Mai Nitsuwa a Cikin  Rayuwar shi. Ka zama wanda kake dogara da Kanka.....Continue reading

3. KA KASANCE MAI FAHIMTAR MACE

Mata Suna Girmama Mutum mai Saurin Fahimtar Yanayin da Suke Ciki. Wannan yana nufin ka zama mai Gane Farin Cikin Su da Bacin Ran Su, ka zama mai Taimaka musu da tallafa musi yayin da suke buƙata. Kada ka guje musu Yayin da suke Ƙunci.
Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA

4. KA ZAMA MAI DOGARA DA ALJIHUN KA DA MUTUNCI

Mata Suna son namijin da Zai iya Riƙe kanshi kuma cikin mutunci. Ma'ana ka zama mai ɗaukar nauyi kanka Financially batare da ka dogara da Wani ya baka ba. Sannan yana nufin Ka zama mai Yin Abu da kanka ba tare da tsoron Yin abunda ranka keso ba.

Karanta: ABUBUWA GOMA 10 DA MAZA KE SO A JIKIN MATA

5. KA NUNA GIRMAMAWA DA CONSIDERATION

Mata Suna Yarda da Duk wani Mutum wanda yake Girmama wasu koda ba nashi ba. Ma'ana Ka Zama Mutum Na Kowa Kuma wanda ya Iya Kalami mai kyau, Ka Treating Mutane da Tausayawa da Girmamawa. Karka zama mai Son Kai Ko Tsauri.

You may like: YADDA-AKE-CHATTING-DA-BUDURWA A ONLINE

6. KA ZAMA MAI IYA HIRA

Duk namijin da ya iya hira da mace zaiyi saurin sace mata tinani. Wato ka zama wanda kake bayyana damuwarka ba tare da ka boye ba, ka zama mai sauraron dakuma fahimtar abunda akeson ka Fahimta. Ka zama ka ƙware wajen Iya Magana Da Sarrafa Harshe. Idan zaka Iya Ma Kana Ƙireta Idan Kuna Hira.

You may like: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA 

7. KA ZAMA SHUGABA NA GARI.

Mata Suna girmama mutumin da ya iya Shugabanci wajen Murɗa su yadda suke so. Ma'ana Ka Juya Mace ta Hanya mai kyau kuma kana ɗaukar Shawari, kuma ka zama wanda kake iya burge wasu kuma ka sasu su bika cikin Soyayya.

Karanta: SIRRINKA 21 DAKE SAKA SOYAYYA KARFI DA JIMAWA

8. KA ZAMA KA IYA KYAUTATAWA

Mata nason mutane masu kyautata musu. Wannan yana nufin ka zama mai kula dasu dakuma buƙatun su Financially. Wannan bawai yana nufin sai ka zama me kuɗi ba ko ka zama mai riƙe da wani babban muƙami ba A'a, Kayi Musu abunda shi ya cancanta dasu ta Wajen Kuɗi, Shawari da Kuma Rarrashi.

Karanta: ALAMOMIN KAMUWA DA SOYAYYAR GASKIYA

9. KA ZAMA MAI BIYAYYA WA ALƘAWARI

Na Ƙarshe, Mata Suna Yarda Da Namijin dake Biyayya wa Amana Da Alkawari dake tsakanin su. Wannan yana Nufin Ka Zama Yardajje akan Mace, Ka zama a shirye wajen Nuna Musu Goyon Baya A Yanayin Wuya Ko Daɗi.

Conclusion

Samun Yardar Mace Ba Abune Mai Tsauƙi Ba, Amma yana yiyuwa. Ta Hanyar Nuna Gaskiya, Rashin Gajiyawa, Fahimta, Dogaro Da Kanka, Mutunci, da Iya Magana, Ka Iya Shugabanci, Ka Zama Mai Basu, Biyayya Ga Alkawari. Idan Kayi Waɗannan Mata Zasu Girmama Ka Kuma Zasu Nuna Maka Yarda.

  • Newer

    YADDA AKE MALLAKE YAR MASU KUDI

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)