YADDA AKE GANE BUDURWA NA SON AURE

0

ALAMOMIN DA BUDURWA TAKE NUNAWA IDAN TANA SON AURE.

Idan mace takai minzalin balaga bayan ta daɗe da fara al'adarta alokacin dukkan wasu sassan jikinta sun gama bayyana takan sami kanta cikin damuwa da son kusantar namiji musamman ma in ba wani abu dake shagaltar da ita daga irin wannan tunanin, takan kasance cikin tunani da yawan damuwa akan hakan har akan gane wadannan alamomin agareta.

1. SON GIRMA

Takan yawaita ambatar Sa'anninta amatsayin kannenta ko ta girmesu, musamman maza Sa'anninta wadanda suka taso tare har zakaji tana tsokanar saurayi tace masa yaro.



Karanta: ABUBUWA-GOMA-10-DA-MAZA-KE-SO

2. SAN TABA JIKIN QAWA Ko Hannu Ko Yawan Ɗaukar ƙananan Yara Waɗanda Suka Fara Tasawa Ajikin Ta, Tana Wasa Da Su. Dakuma Yawaita Son Yara Nagoye.

3.YAWAITA NUNA DAMUWA A FUSKARTA

Awasu lokutan zakuga kamar an 6ata mata rai ko kamar tana jin haushin wani hakan tana nuna alamar aure take so.

Dalili kuwa su sanadaran balaga dake jiki suna da alaka da sakasu jin damuwa.

Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA

4. Son Zama A Ɗaki tsawon wasu lokuta ita kadai alhalin kalau take ba wata cuta ke damunta ba.

Idan budurwa na Buƙatar Aure takan yawaita zama a daka ita kadai kawai tana ta Saƙe Saƙe a zuciyarta kamar gashi suna soyayya da wani har sunyi aure da tunaninnika kala kala me alaka da aure.

5. BATA JIN TSORO KO KUNYAR TSAYAWA DA SAURAYI KO A GABAN WAYE

7. YAWAITAR HIRAR SAURAYI GA ƳAN GIDAN Su Da Rashin Boye Soyayyar Ta Ga Iyayenta Musali Takan Rubuta Wasika Ana Kallonta Ko Amsa Wayar Saurayi Acikin Gidan Su.

Karanta: YADDA ZAKA SAKA BUDURWA TA KWARE MAKA

8. SON ZUWA GIDAN KAWAYENTA MASU AURE DA MARASA AURE Suna Yawaita Hirar Samarin Su Ko Yanayin Zamantakewar Aure.

9. Yawaita kwalliya da sa diresin irin na mace me aure ko irin na amare musamman mace ustaziya tafi nuna wannan alamar.

10. Son magana da namiji kusa da kusa da son kura masa ido.

11. Yawaita hira akan kayan daki kamar fadar kalarsa ko kudin abu kaza da kaza idan yan matan qauyene ma sukan yawaita siyan kayayyakin bukatun su nagida tayi ta tarawa a maƙotan su fiye da lokutan baya.

.............. Continue reading

12. Yawaita tunani in tana hira a cikin yan uwanta sai a ga tayi shuru alhalin ba abun dake damunta. DA SAURAN SU.

Yana dakyau iyaye suna la'akari da irin wannan alamomin dan zai taimaka musu wajen gano halin da yarsu take ciki

Budurwa Inta So Aure Kawai Aimata Aure Shine Mafita Kawai Amma Sabanin Haka An zalunceta Kuma Hakan Kan Iya Sata Sa6on Allah Ita Kanta Batare Da Ta Ankara Ba Kusan Duk Yan Matan Da Samari Ke Batawa A Yayin Da Ake Kiran Ƴanmatan Hira, Su A Ransu Ƴan matan Basa Fitowa Da Nufin Ai Lalata Dasu Amma Ƙarfi Na Sha'awa Da Salon Yaudara Na Samari Yan Iska Sai kaga Sun Kai Budurwa Sun Barota,



YADDA ZAKA ZABI MATAR AURE

Akwai hanyoyi da dama da ake zabin matar aure domin yin rayuwa, ga kadan daga cikin su kamar haka:

Yin dacen samun abokiyar rayuwa me nagarta babbar nasarace a Wannan zamanin da muke ciki.

Idan ka samu kuwa matukar zata soka irin sonda kake mata ko fiyeda haka tabbas abokiyar zama ce, abunda ya rage shine ka rike ta da kyau.

Karanta: YADDA AKE HANA MATA YAUDARA A SOYAYYA

Matukar zata faranta maka rai toka riketa hannu bibbiyu 

Duk Budurwar dazaka furta mata kalmar so, kaima ta maidama da furucin kauna Abokina ka riketa da muhimmanci, Zamanin mu ya canja samun kamar su wuya gareshi. 


Karanta: YADDA AKE MALLAKE USTAZIYA 


Abokina idan Allah ya baka mace mai tsoron Allah wacce zata kusanto ka da alkairi sannan ta nisanta ka da sharri tabbas wannan itace matar aure.

Duk budurwar dazata baka kulawa ta musamman sannan tayi abunda kakeso, tabar abunda bakaso to wlh irinsu sunada wuyar samu ka Rike abarka da kyau. 

Mace Abokiyar rayuwa ce ni'imace kuma haske ce dake haska rayuwar duk namiji.

Dacewa a soyayya shine kasami mace tagari, wacce tasan mutumcin ka tasan nata mutumcin wacce zata karema mutumcin ta da naka ako yaushe. 

Sannan kasani mace yar'adam ce kuma tana kuskure duk lokacin da tayi ba daidaiba kayi mata uzuri ka fahimtar da ita ta hanyar dazata fahimceka.

Muna baka shawari idan zaka zabi mata, to ka zabi mai addini yafi domin haka addinin mu yayi mana umarni.

Wannan nasiha ce akan Soyayya, duk mai ƙarin bayani mu hadu a comment, muna Godiya Agareku masoyan wannan shafi www.Qauna.com.ng Muna Alfahari daku.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)