ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA

0
ZANTIKA, WASIKU TARE DA ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA DOMIN MASOYA NA HAKIKA BANA YAUDARA BA




17
Indan Da Rai To ina saka tsammani, tare da fatan cewa watarana zan kasance a fadar ki yayin da zan kiraki matata, bana cire rai da tsammani domin kullum ina addu'ar Allah ya bani ke, Nayi nisa a cikin Soyayyar ki irin nisan da bana tinanin idan an kirani zan juyo, sahibata Qaunar da nake miki a yanxu


Itace numfashi na, Wannan dalili yasa bana qaunar kiyi nesa dani, rayuwata sai dake, idan babu ke babu ni, da Za'a tsame ki daga cikin ruwan qaunar da nake miki, to wannan ruwan ko shayi bazai dafa ba, sai dai zubarwa. Kece jindadi na, kece farin cikina. Zuciyata mallakin ki ne. Ina Qaunarki Matata.


18
Lambar yabo a gareki mai sona.
Zinariya masoyiyar rai na.
Gimbiya alkhairin rayuwa na.
Saruniya cikon farin ciki na.
Tauraruwa hasken ruhi na.
Lokaci daya rurutaccen sonki ya ruru a zuciyata, sai dai sanin cewa ke wata da ban ce cikin *yan mata, ma'ana ke tamkar sarauniyar su ce, ya sanya na miko gaisuwar ban girma a gareki sahibata.

Bana tunanin samun kamarki domin raina gaba daya ya kamu da sonki.

 Na sani cewa zanyi alfahari da ke idan kika furta kalmar INA SONKA a matsayin amsar ki gareni.

Ina sonki da wani irin so mai dauke da sinadarin ratsa dukkan sassan jiki. Ke daya ce mafi haske da dauwama a zuciyata. Ina son ki.
Zafafan Kalaman Soyayya 2023




19
Rurutacciyar wutar kaunarki tana ci gaba ruruwa a zuciyata wanda hakan ya sanya sonki ya ke sake kwaranyuwa a zuciyata. 

Na ji son ki ne a take a yayinda idanuwana sukai arba da tsaleliyar kyakkyawar fuskarki. 

Sai naji bugun zuciyata yana fita da karfi, dukkan wani kuzari na rasa shi, kin dolantar da ni sosai hakan na zama mara wayau. 

Duk da cewa da akwai kyawawan *yan mata a duniya amma sai naga kinyi musu zarra, ma'ana kin kere su wajen kyau da haduwa.

Hakika kin boyeni a cikin hazo na so ta yanda bana kallon kowacce *ya mace sai ke.

Tauraruwarki ba zata taba disashewa a zuciyata ba, abadan da'iman son ki yana tare da ni.

Ke mai kyauce, dole a ce kina da kyau, haka surarki kyakkyawa ce wanda ko makiyinki yasan da hakan.
Ina sonki koda yaushe.





20
Kin shigo rayuwata kin koya mini yadda ake rayuwa da gaske, kawai ki kasance a doron duniya. Daga lokacin da kika shigo rayuwata, kowace rana rana ce mai kyau da ban mamaki wacce koyaushe nake jira. Ina mai farin cikin samun ki, kuma koyaushe zan kasance tare da ke kowane lokaci tare da ke. Ina matukar kaunarki, gimbiyata Ina son ki, kuma zan so ki har abada. Kece farin cikina na yau da kullun ba tare da ke ba, zuciyata na zama kamar fanko. Kin cika ni kuma naga alherin samun ki a rayuwata. Tare da ke, duniyata cikakkiya ce kuma kyakkyawa, kamar yadda kike.


21
Amincin Allah yatabbata agareki yake tauraruwa mai haske da walwali a idon abokan gaba Datan kina lafiya yake abar kaunata farin cikina, rayuwa, nunfashina, rabin jikina Kaunar dake miki bazai misaltu bah duk randa na rasaki to jijiyoyin jikina zai bar aiki kece ta farko kuma ta karshe,kin bude kuma kin rufemin zuciyata na baki makulin a hannuki. Take care of your self i love u more than my self 
Always be mine ,i will be your insha Allah bye.





22
Zuciyata cike take da tunani a yayin da idanuwa sukayi jawur tamkar jini babu komai dake yin dadi zafi da radadi sai ziyartar xuciya suke. kewa hadi da sanya rai mara tabbas. ashe idan babu ita a duniya ni ba kowa bane. Numfashi sama sama ke tasowa. bugun zuciya na qaruwa yayin da harbawar jini ke raguwa, hanta kadawa take yayin da ruhi ya cika da tsoro, matsalar ba na rashi bane na maye gurbi ne. abinda matukar ciwo a lokaci da muka bayyana zuciyar mu aka kasa fahimta, zuciya kasa jurewa take. mu kan iya jure bakinciki, damuwa duk muyi hakuri sannan muna iya jure rashi da zafin ciwo duk wandannan abinda na lissafa zuciya tana iya jure su Amma kuma bata


da juriya akan danne soyayya. inji hausawa suka ce labarin zuciya a tambayi fuska, Amma masu iya magana sukace zuciya tana iya boye damuwa ba tare da fuska ta bayyana sakon zuciya ba duk da kasancewar daya baya iya boyewa daya sirri a cikinsu. Amma zuciya ta kan iya jure bakinciki tare da radadi ta yadda fuska zata saki yalwataccen murmushi mai haske ba tare da ta nuna alamun zuciya na cikin kunci ba. Amma kuma idan abinda ya shafi soyayya ce zuciya bata iya jurewa. Tabbas masoyi kan iya jure bakinciki dake damun sa Amma kuma baya iya jure bakincikin masoyin sa. wasu lokutandamuwar mu muke dannewa mu bayyana muku murmushin mu, shin wannan ba sadaukarwa bace?.


Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-BI-KA-SACE-SOYAYYAR MACE



Har abada xuciya baxa ta taba manta wa dake ba domin kece silar farin ciki na muradin xuciya ta na miki kyakkyawan shimfidaddan masauki mai dauke da kyawawan furan launin koraye Wanda xasu kayatar sannan su nisha dantar da xuciyar ki taka sanu a hankali gimbiya sarauniyar yan mata masoyiya ta abar kauna ta ya tsa gwaron xallar tsabar kwayar tsokar xuciya ta na yaba hasken kyawun ki tamkar yana Xinariya yay davan dana sauran mata


Masoyiyata, ina son ki fiye da yadda kike so na. Ina son kasancewa tare da ke domin kina farantawa zuciyata. Kallon ki kadai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Ke ce farin cikina. Ina nan rike da amanar soyayyarki har Qarshen rayuwata. Na saka a raina ba zan taba
mantawa da ke ba.


Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke Qawatuwa da kallonsa, hanci ya ji daddadan Qamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Jin dadi da walwala ba za su taba samuwa a tattare da ni ba matukar babu soyayyarki a cikin zuciyata. Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke lambun zuciyata.


So tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take dauke a jikin gangar jiki ma’abociyar zuciyar da take Qunshe da So. Kasantuwar so a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin zuciya bayan bayyanar sa, wato bakin-ciki da kuma farin-ciki. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi. Ina Son Ki.


MU KASANCE TARE HAR ABADA.

Masoyiyata ina neman alfarmar da ki mallaka min zuciyar ki, na dad’e da mallaka miki tawa lokuta masu yawa da suka shud’e abokai ma shaida ne, bayan ya kasance kin


mallaka min ita ni kuma zan had’a su na d’aure su waje guda da sarkar soyayya mai ‘karfi na jefa makullin a cikin tekun maliya. Ki amince ina son ki wannan shi ne burina. Ki huta lafiya.


SAMUN KI A RAYUWATA BABBAR NASARA CE.

Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d’aya, ina cike da zumud’in son dawowa domin cin girkin ki mai dad’i. ki kula min da kan ki, sai na dawo. Ina son ki matata.



KO KIN SAN YAYA NAKE JI IDAN BANA TARE DA KE MATATA?

Nesantar ki babban aiki ne da yake jigata zuciyata, dama ace zaki iya fuskantar halin matsi da takura da nake shiga da kuma shaukin son kasancewa a tare da ke da nake ji cikin zuciyata a dukkan lokacin da na nesanta da gida. Ina fatan zaki ci gaba da kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan dawo gida. Allah ya tsare min ke matata, ina son ki


Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)