ALAMOMIN SOYAYYAR GASKIYA GUDA 14

0
ALAMOMI 14 DAKE NUNA KUN DACE A SOYAYYA


Soyayya Wani abu ne DA bashida tabbas a rayuwa, Amma wata Soyayyar tana ginuwa har abada, akwai wasu da tasu Soyayyar idan ta jima shine takai wasu watanni ko Shekaru sai ta wargaje, daga Nan sai batun rabuwa.

Kamar yadda muka sani, Rabuwa da masoyi akwai zafi, Haka kuma gina rayuwa da wani shima wani abune mai wuya. Domin kasancewa cikin rashin kokwanto a Soyayya, Anan Wasu alamomi ne Ƴan Kaɗan guda 14 da Zasu tabbatar maka cewa kai da Masoyiyar ka Kuna yin Soyayya Irin wacce ta dace sannan Kuma Kunyi Dacen Juna.

1. BAZA KAYI/KIYI RAYUWA BABU SHI KO ITA BA.

Daga Lokacin Daka Fara ko kika fara tinanin cewa baza ka/ki iya rayuwa babu shi ko ita ba, ko kuka fara jin rayuwar ku batada ɗanɗano idan babu ɗaya ba, wanna yana nuna cewa he/she is everything to you. Idan Kana Soyayya da mutum kuma ka fahimci cewa zaka iya yin rayuwa dashi cikin sauƙi, ku haifi ƴaƴa, ku tsufa tare, to lallai babu makawa cewa kun dace da juna.






Ba abu ne mai sauƙi ku samu irin haka ba, sai kunyi Bincike, Kuma kun saka nitsuwa acikin lamarin neman macen data dace, ko namijin daya dace.


2. SUNA GOYON BAYAN JUNA.

Duk Soyayya Mai DaÉ—i akwai yarda a cikin ta, Soyayya babu ruwanta da irin sana'ar ka ko kyawun jiki nasaba ko iko, babu talaka ko mai arziÆ™i, Soyayyar gaskiya itace Soyayyar dake haÉ—a masoya biyu su tafi akan hanya É—aya, duk irin Æ™unci, damuwa, daÉ—i ko farin ciki baza ta saka su rabu ba. Kuma zasu Goyi bayan juna akan ko wace irin buÆ™ata ce ta cigaban su. 



3. AKWAI FAÆŠIN GASKIYA, KODA ZA'A YI JAYAYYA.

Soyayyar da kake/kike wa masoyin ki/ka da tsoron kada ka rasata yakan iya jefa ka cikin danasani. Idan har da gaske kuna son juna, to zaku iya yin faÉ—a dan ku canza wani abu da ba dai dai ba. Koda Ran É—aya zai Baci ku faÉ—awa juna Gaskiya, Kuyi Gaskiya.

Saboda Shi Itace tun yana ÆŠanye ake Tankwara shi, Idan Ya Bushe saidai ya karye. Tun kuna Soyayya Zaku koyi yadda zaku Magance matsala tsakanin ku ba tare da kun cutar da juna ko Soyayyar ku ba.


That's
what it really means to compromise for the sake of your relationship. After all, your partner makes it all worthwhile and you see everything as a lovely journey.



4. YIN DARIYA TARE YAYIN HIRA.

Idan Kai da Masoyiyar ka kuna dariya tare yayin da ɗaya ya bada abun dariya, to Soyayyar ku tana da ƙarfi kuma alamu ne na Soyayya irin ta aure. Sakewa da juna wato sake jiki yana da matuƙar tasiri acikin Soyayya.

Shawari: koda Sau É—aya ne acikin Wuni kuna gwada irin Wannan Dariyar, Zaku na Tinawa da ita.


5. SANIN SIRRIN JUNA.
Kasan sirrin Ta, tasan sirrin ka wanda ba kowa ya sani ba. Wannan shi yake nuna cewa bakwa boyewa juna wani abu da yakamata ku sanarwa juna, kuma shi yake Æ™ara saka shauÆ™i na Soyayya domin kunsan sirrin junan ku. 

Akwai Matuƙar Shauƙi mak daɗi idan kuka san cewa kun karbi junan ku yadda kuke.



6. TURA SAƘON WAYA KAÆŠAN 
Wasu Mutanen, Sai kayi ta tura musu Message ta waya da yawa kafun su fahimci SaÆ™on da kake son isar musu. Amma akwai waÉ—anda basa buÆ™atar dogon zance suke ganewa. 

Yawancin maza suna tinanin yin amfani da Message idan basa son suyi wa mace magana ido da ido, Mata kuma Sukan turawa mutum Message ne idan Ran su na bace Yawanci.

Soyayyar Da ake da gaske Kuma ta gaskiya Yin Zance Ido-da-ido Yafi saka shauƙi a wurin masu yinta. Kuma yafi tura Message daɗi da saurin fahimta.

Kumq Ba'a yawan Tura Saƙonnin Soyayya Wanda Basu da amfani.





8. SUNA FAÆŠA A WASU LOKUTAN.

Yin Faɗa Da Abokin Soyayyar ka ba abun ƙi bane, kai, Duk Masoyan Da Basa Yin Faɗa Basu Cika Masoya Ba, Domin Soyayya ce kaɗai take saka ayi faɗa da safe zuwa hantsi An shirya kamar basu ba.

Faɗa a Soyayya yana nufin bakwa boye damuwar ku a zuciya, idan ɗaya yayi ba dai dai ba ɗayan zai faɗa mishi koda za suyi faɗa ne, bawai muna nufin faɗa da hannu ba, A'a, Faɗa Me shauƙi wato Jayayya ko Fishi.


8. KUNA HAÆŠUWA AKAN RA'AYI

HaÉ—uwa Akan Ƙuduri ko Ra'ayi Guda ÆŠaya abune mai kyau wa masoya, domin yakan basu karfin guiwar tunkarar duk wata matsala tasu. 

Yadda kuka HaÉ—u akan Ra'ayi É—aya Haka Rayuwar ku ta Future zata ÆŠaukaka.




9. NUNA SOYAYYAR KU GA JAMA'A.

 Ilimi Ya Nuna cewa Masoyan da suke nuna Soyayyar su ba tare da sun boyewa Jama'a ba, ta hanyar Nuna Hotuna a Social media, ku rashin tsoron nunawa kowa cewa suna Soyayya, To Sune masoyan Gaskiya Kuma na HaÆ™iÆ™a, kuma Sun Shiryawa Yin Rayuwa Tare.

Ka Nuna Mata Yadda Kake Alfahari idan Kana Tare da Ita wa Jama'a.


10. KU KASANCE NUTSUWA IDAN KUNA TARE.
Ba'a Buƙatar Bayyana wani Launi na shauƙi idan kuna tare da masoyan ku. Koda kana farin ciki, Bacin rai, Baƙin ciki ko Nuna Wani Takaici, Baka buƙatar nuna Shi Kusa da wanda kake so. Idan Kana iya boye Damuwar ka dan Abokin Soyayyar ka kada shima ya shiga damuwar to Soyayya ce me Tsafta kuke Tare Da Nitsuwa.


11. KUNA SON BAYYANA WA JUNA DAMUWAR KU, KO FARIN CIKIN KU

Masoyiyar kace ta farkon zuwa maka a rai idan ka samu abun Farin ciki kona Baƙin ciki? Idan Haka ne to Kana da Tabbacin ka samu Abokiyar rayuwa. Kuma itace wacce zata taya ka murna, ko ta rarrashe ka idan kana kuka.




12. KUNA KALLON CIKIN IDANUNA JUNAN KU.
Kamar yadda na faɗa, kallon idanun junan ku a tare yana da matuƙar amfani wajen nuna shauƙi. Ko da kuwa zaku iya kaiwa awa guda to kuyi Alamu ne dake nuna irin zurfin Soyayyar da kukewa juna.

Idan Kasan Wani Wanda Yake Soyayya, Ko Zai Fara Soyayya, Kayi Masa SHARE domin Shima ya samu abun da zai kama a Soyayya.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)