YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HADUWA

0
YADDA AKE HIRAR SOYAYYA
❤❤❤❤❤

Samun Soyayya a yanxu yana yiwa Samari dama ƴan mata wuya. Musamman idan zasu tare budurwa domin su yi mata magana da zummar bayyana abu dake ransu, abun yana basu wahala Sosai, mun kawo muku wata hanya mai sauƙi domin zata taimaka.

Da Farko Yakamata Kayi Wasu dabaru domin ka Samu damar yin magana da ita. Idan ka sami damar magana da ita to ka samu kaso mai yawa na damar da kake da ita da zaka tofa abunda ke Cikin Zuciyar ka.

Bayan Gaisuwa

Akwai Abun da nake buƙata a gareki, abun yana da Muhimmanci agareni, domin shine ya kawo ni gareki, kuma ina fata zaki kalli Ƙuduri na da Kyakkyawan fahimta. Inason na samu fahimta tsakanina dake sosai domin inason na ƙulla zumunci tsakanina dake kuma inason zumuncin ya rayu tsakani na har abada.

Inaso kimin wani taimako, kuma kece a yanxu zaki iya min wannan taimakon, Zuciyata ta kamu da Soyayyar ki, lokaci É—aya ba tare da na ankara ba❤ .
Inason ki Sama min Gurbi a zuciyarki koda ba yawa, kisani a Cikin zuciyarki koda sau É—aya ne a rana, idan kika min wannnan taimakon to kin kamo hanya mai kyau kuma mai tsarki wacce zatai maganin ciwon dake zuciyata.

Farkon fara saka kwallin idanuwa na akanki naji zuciyata tayi bugu irin bugun da bomb yakewa dutse, haka SOYAYYAR ki ta Shigen nayi farin ciki sosai da ganin ki. Gurbin da nake nema ina son nayi amfani dashi wajen shuka furanni masu kyau a kallo, zan samar da ƙoramai Masu Daɗin zama, zan shuka bishiya irin wacce Ba'a tugewa, zan toni rami me girman eka Dubu, nai ajiya a ciki na Soyayyar ki nai mashi fandisho wanda babu wani mahaluƙin da zai iya tono shi.


Idan kin bani dama zan saki farin ciki daga Xuciyar ki zuwa fuskarki na har abada. Xan tabbatar Bakiyi Hawaye na bakin ciki ba, zan Tabbatar miki da yanci wacce duk wata diya mace take nema wurin d'a namiji. Zan doraki akan kujeral mulki wacce babu adawa balle yan siyasa. Zan shayar dake zumar Soyayya wacce zata saka ki manta duk wani bakin ciki da kika shiga a baya. 


Idan kika amince min zan kai dogon ginin da yafi ko wanne gini tsawo a duniya, na baki sandar girma ki mulki dukkanin ilahirin Birnin dake Fadin Duniyar Zuciyata.

Zan tanada miki kuyangu masu miki hidima ta kota wani fanni, zan gina miki gida irin gidan da babu irin shi a duk fadin tinanin ki. Zan Shagwaba ki kamar yadda uwa ke Shagwaba diyar ta. 

Ina Fatan Zuciyar ki zatai shawari mai inganci irin wanda ta saba akaina, domin inason kasancewa dake Badon komai ba sai dan Allah.


Ki sani Soyayya ta agareki ta gaskiya ce, babu sirki, Xuciyata kuma mallakin ki ce duk. 

Ina sauraron Ki Sarauniyar Zuciyata, Ki daire kiyi adalci kamar yadda kika saba ga wannan dan saurayi wanda keson saka ki farin ciki na har abada.............

Kada ku Shagala Kuna Tare ne Da Shafin QAUNA

Ku watso mana naku Mu gwada, Tare da Ziyartar Shafin www.Qauna.com.ng Domin Cigaba da Zanbado muku KALAMAN SOYAYYA

Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)