DABARUN YADDA AKE CHATTING DA BUDURWA
Gabatarwa (Introduction)
Yin chatting da budurwar da kake so wasu lokutan yana bada wahala idan kana jin kunya ko baka iya hira mai ɗaukar Hankali ba. Idan Baka san yadda zaka Ɗauke hankalin mace da chatting ba kuma kana son ka iya, Har ka gano wasu Sirrika, to ka Tsaya ka koya.
Farawa (Preface)
ABUBUWAN DA ZAKU TATTAUNA DA MACE
Idan Kana magana da mace ko zakayi magana da mace a farkon haɗuwa, ku tattauna akan abunda ya Shafi Kowa misali: zaku iya magana akan Siyasa, Wasanni, Celebrities, Waƙoƙi, Littatafai, Fina-Finai da Sauran Su.
Kar ka Tambayi Number wayar ta sai bayan ka ɗan Girgiza mata Zuciya da hira ko Kalamai masu taushi. Kayi ƙoƙarin karantar Ta domin sanin me ya dace ka tattauna a lokacin. Kamar yadda zamu zayyana anan ƙasa.
Karanta: ABUBUWAN DA AKE DUBAWA AJIKIN MACE KAFUN AURE
Ka zabi Topic da zaku tattauna ko ku ɗan Hiranta akai da ita amma a wayence. Manufar ka nada Amfani anan. Idan Kana son Kayi Soyayya da Ita mai tsawo to ka nemi sanin ta sosai a lokacin.
Ka Karanta Yadda za kayi magana da mace wato yadda za kayi chatting da budurwa a online, ko ido da ido.
Zaka iya tambayar ta akan abunda ya wuce ko yake faruwa yanxu kamar Abunda take na Sana'a ko Abunda Take So.
Kuyi Magana akan Abunda yake bata sha'awa ko ko take so tayi.
Ku tattauna akan Abubuwan da suka faru da ita a Baya ko suke faruwa yanxu.
Ka san wani irin Abinci take so ko take son ta iya girkawa.
Karanta:HALAYEN MATA WANDA MAZA BASA SO
Ka Tambaye ta Abunda take so wanda Kullum sai tayi su saboda kasan yadda take rayuwa.
Tambaye ta wani irin Fure (flowers) take so idan zaka saya mata.
Ku tattauna akan wani Littafin daya bata sha'awa kuma wanda ta karanta.
Ka Tambaye ta Abunda ake kwatancenta dashi. Zai iya zama Yawan Zuri'ar su, Ita Celebrity ce da Sauran su.
Idan Mai Sha'awar waƙe waƙe ce ka Tambaye ta irin waƙar da Tafi so saboda ka haɗa mata su don ya burgeta.
Ku tattauna yadda take son tayi Soyayya. Zai Taimaka maka wajen gane Abubuwan da take so a Soyayya da yadda take son su.
Ka Tambaye ta Wurin cin Abunci da tafi so wato Restaurants koda wataran zaka ɗauketa kuje cin Abinci.
Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE
Ka binciki mafarkinta, abunda take so wato Burikanta.
Kuyi Hira Akan Ƙasashen da take so. Ko take son zuwa.
Ka Tambaye ta abunda take jin Tsoro ko yake damunta saboda ka gane ko kasan yadda zakana kwantar mata da hankali idan tana Bacin rai ko Damuwa
Karanta: ABUBUWA 10 DA MATA KE SO A SOYAYYA
Ka Tambaye ta me yake sata nishaɗi idan ta gaji ko kanta ya ɗau zafi, zai Taimaka wajen ɗauke mata damuwa.
Ka Tambaye ta lafiyar jikinta, abunda tafi son ci, yadda take girki, da Aikin da Tafi so.
Ku tattauna akan yadda take magance Abubuwan da suka shiga mata duhu ko masu wahala. Musamman na Family ko na Abokai misali: Fishi ko faɗa da wasu.
Ka Tambaye ta su waye ƙawayenta dakuma wanda tafi son zama dasu acikin ƙawayen.
Karanta: YADDA ZAKA GANE DACEWAR KU A SOYAYYA
Idan Zaka Aureta ne, Ka Tambaye ta Yadda Dangin ta suke, Addinin suda Al'adun su na Yare, da Kuma Abubuwan da suke na Sana'a. Da Sauran su.
Idan Kun taba yin Abokantaka A baya, ku tattauna akan Yadda kuke a baya dakuma gane ko kun shirya cigaba da wancan Alaƙar sannan ku gina sabuwar Soyayya.
Idan Kun Jima Dama Abokai ne, ka Tattauna da ita akan Sanin da ta yiwa Addini da Al'adun ta, yadda take samun kuɗi. Yadda take son tayi rayuwar Aure da Sauran su. Ka Kwatantasu da Naka sai ka tantance zaka zauna da ita ko A'a.
Karanta: YADDA AKE MAGANIN MATA
YADDA ZAKA FARA MAGANA DA MACE
Ka Nuna Confidence wajen yin shiga mai Kyau da tsari saboda haɗuwar farko yana da Amfani sosai.
Bayan ka zabi abunda zaku tattauna akai kuma take so ko yake burge ta Ga wasu Daga Cikin Dabarun Hira:
Ka Tsara Zancen ka ya zamo Positive Affirmations. Irin Da murna haka. Idan ka ganta kaje kai tsaye wurin ta.
Ka Fara da Gaisuwa mai Kyau da Tsari.
Karanta: HALAYEN MATA WANDA MAZA BASA SO
Kayi magana a Hankali kuma cikin nitsuwa
Ka Daidaita Sautin Muryarka bayan Ta Amsa maka gaisuwa.
Karka mata Ko wace irin tambaya.
Maimakon haka, Ka Gabatar da Kanka.
Ka karanci Yaren jikin ta Dan ka gano tana son magana dakai ko A'a.
Ka Duba waɗan Nan Alamomin Kafun Ka Cigaba da Magana:
Karanta: YADDA ZAKI RUBUTAWA SAURAYIN KALAMAN SOYAYYA
ALAMOMIN DA ZATA NUNA IDAN TANA SON MAGANA DAKAI.
Zata Na Kallon idanun kamar na sakanni, da kyasta ido ko tana satan kallon ka.
Zata na yi maka Murmushi, ko tana Cizon Leben Bakin ta.
Za tayi Ƙoƙarin Gyara jikin ta dan ta burge ka, Misali: Wasa da Kunnen ta, zata Na ɗan nuna jin kunya.
Zata nuna sakewa yayin da kake mata magana. Kuma zata baka fuska.
Zata Fuskance ka, Idan Gefe take kallo zata juyo zuwa kallon ka.
Zata na juya jikin ta dan Ka gani ko Fuskar ta.
Karanta: ABUBUWAN DA SUKE BATA SOYAYYA
ALAMOMIN DA ZATA NUNA IDAN BATA SON MAGANA DAKAI
Baza tana kallon ka ba ko Haɗa ido dakai.
Zata Bata fuska ko ta tsume
Baza tayi komai dan ta burgeka ba ko nuba alama.
Zata Naɗe Hannun ta kuma ta boye Fuskarta, kuna bazata sake jiki tayi magana ba.
Zata Juya maka baya. Ko ta fara magana da wani.
Zata shareka tayi tafiyar ta da Gatsali.
Karanta: AMFANIN-SANIN-ABOKIN-SAURAYI
Idan Har ka Gane tana son magana dakai, Sai ka Tambayi Sunan Ta, Sai ka sake Tambayar sunan.
Kace mata tama Spelling idan kana son bata dariya ko Sunan nada wahalar faɗa.
Ka Yabi sunan sosai. Misali: Wannan Suna Yayi
Ka yabi wani abu a jikin ta daya banbantata da Sauran mata. Misali: Naji Daɗin Yadda kikai min magana, Kuma Kin Iya Magana mai tsari. Idanuwan kinnan Suna Ɗaukar Hankalina.
Tambaye ta Yakike, Ya Yau da Sauran su.
Ka fara Hiran Abu mai Ɗan Ɗaukar Hankali, Misali: Kamar ana Zafi Sosai ko? Nai miki rakiya ne ko kin iso? Da Sauran su.
Karanta: YADDA-AKE-SOYAYYA-DA-QARAMAR-YARINYA
Ka cigaba da Jawo Magana da Hira akan Abubuwan da kai da ita kuka haɗu akai. Misali: Littatafai, Kasuwanci ko Technology.
Karka mata maganan Siyasa, kona iyayen ta a Haɗuwar farko.
Duk wasu Abubuwan da kasan yin maganan su ga mace zai iya bata haushi to karka mata su. Kawai ka faɗa mata abunda take son ji. Idan har ka samu hirar ta saitu to ka ta nemo maganan da zaisa ku jima kuna hirar.
Karanta: YADDA-AKE-YIWA-MAZA-SHAGWABA
Waƴannan zasu Taimaka wajen janyo hankali da jawo hira mai tsawo.::
Kana Ɗan Satar Kallon Idon ta.
Ka dinga kallon ta sama da ƙasa.
Karka na Kallon Gefe ko kana Kallon wasu idan kuna tare.
Karka Kalleta Sama da Seconds 5.
Duk Kallon ka Ya Ƙare akan idanun ta ba wai Ƙirjin ta ko Bayanta ba.
Idan Kuka haɗa ido karka ɗauke har sai kun kai seconds 3-5 a Hankali sai ka kauce.
Kana yawan haɗa idanun Kamar 50% wato Ka yawaita kallonta musamman eye contact, Musamman idan Tana Magana.
Ka dinga Blink Kaɗan.
Karka faɗi maganar da zai bata mata rai Misali: Tabon fatar jikin ta yayi baƙi ko Fari.
Kaɗan Bata dariya Domin mata suna son Namiji mai Bada Dariya.
Karanta: HANYOYI-GOMA-10-DA-AKE-SACE-ZUCIYAR-MACE
Yadda Ake chatting Da Budurwa
Kar kaji wani ɗar wajen yiwa mace magana a online. Bayan ka duba posting da Tags ɗinta, anan zaka gane irin abunda tafi so. Ka faɗa mata komai da Cikakken bayani.
Ga Wasu Dabarun Yadda Ake Chatting da Budurwa a Online:
Ka maida hankali sosai wajen abunda take yawan posting akai a Online. Mata suna duba posting ɗin namiji anan suke fara karantar rayuwar Namiji kafun suma Magana. Dan haka kana yin posting masu kyau masu jan hankali. Sannan ka kiyaye Yin Posting maras Tsafta.
Kayi Mata Like da Comment a hotunan data poster amma ba duka ba kamar kashi 3 cikin 5 haka Kafun ka mata Magana.
Ka fara mata da Magana wasa kamar tsokana haka ko wani abun ban dariya, sannan ka Tambaye ta Zaku iya chatting yanxu ko sai anjima, sai ka Gabatar da Kanka.
Karanta: YADDA-AKE-GANE-BUDURWA-ME-KWAƊAYI
Ka Yabi wani hoto data saka ko Posting. Zaka iya tura mata wasu hoton ko post ɗin ka yabe su amma kayi amfani da Kalmar Girma.
Ka Tambayi sunan ta kuma ka yabi sunan.
Zaka iya amfani Da Posting da take yi na Rubutu kona Hoto Ka Jawo hira dasu.
Ka faɗi komai mai kyau. Kar kayi Ƙorafi akan Abunda ya faru dakai, na Aiki, Dangi da Sauran su. Musamman Finacial Issues.
Kar kace ta tura maka hoton ta.
Kayi Saurin Gane abunda take so kamar Burinta da Basirar ta, ko abunda take son ci koda wataran zaka gayyace ta Fita Date.
Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-NUNAWA-MACE-SOYAYYA
Kana tura mata Saƙo amma na abokantaka da safe dakuma da Dare. Karka sake mata sosai har sai kun haɗu Face to Face. Zata iya tinanin ko ka damu da ita ne.
Karka tura mata Messages akai akai ako wani lokaci, musamman idan bata reply akan lokaci, saboda za tayi tinanin ka Maƙale mata.
Ka Kula da jimawar hiran ku. Idan hirar tana jimawa to zata so ku haɗu.
Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA
Rufewa (Conclusion)
Muna Fata Ka koyi wani abu daga cikin abunda muka faɗa. Ka jarraba waɗannan fabarun wajen Burge Macen da Kuke chatting. Dakuma idan kuna magana Ido da Ido.
Kana Qauna.com.ngZama Da Mata Kamar Ƙanne Ƴan Uwa anokai, Abokan karatu. Zama dasu zai sa ka saba da mata kuma bazaka ji tsoron Tinkarar mace ba.
Muna Kawo muku Kalaman Soyayya na Mata da Maza, da Sabbin Dabarun Iya Soyayya.