FARILLAN SOYAYYA GUDA 7

0

FARILLAN SOYAYYA GUDA 7 DA ZAKA BI KAYI SOYAYYA MAI DAƊI

Soyayya babu wahala, amma mutane da dama sukan sha wahala akan Soyayya, wasu na kiranta da suna zuma, wasu na ce mata maɗaci. Gaskiyar maganar itace Soyayya takan iya zama a ko wani suffa, Zamowarta Alheri shine yafi yawa 75%. 

Ko da jimawar Soyayyar ku ta kai kwana 50 ko Shekara 50, Zaku iya bin waɗannan hanyoyi domin sake dawo da ita Kamar sabuwa.


 1. KA SA A RANKA CEWA YIN FAƊA A SOYAYYA, KAMAR WANI BANGARE NE NA RAYUWA.

Kada ka gujewa Soyayya kawai dan kun samu sa6ani, rashin fahimta ko rashin Dacewa har sai idan Raini, zagi, Yawan Buri ko Tsangwama ya shiga Cikin lamarin. Duk irin yadda zaku bata rai ko kuyi fishi da juna to ku tsaya da ƙafafun ku akan Soyayyar ku shine zai ƙara mata Ƙarfi da Shauƙi.


2. KAYI SOYAYYA ABISA SHAUƘI

Wasu mutane, suna da halaye marassa kyau wanda su kansu suna cutuwa sanadin halin, kuma su cutar da wani. Kamar saurin yanke hora, rashin iya magana, rashin iya sarrafa Shauki wasu abubuwa ne da basu dace ba acikin Soyayya. Iya sarrafa shauki yadda ya kamata yakan saka Soyayya daɗi fiye da farkon haɗuwa, yakan saka Soyayya jimawa acikin shauƙi ba tare da kun nuna ƙosawa da juna ba. Hakan zai faru idan har kuna tattauna matsalolin ku ba tare da jin kunya ko tsoro ba.3. KUNA BAIWA JUNA LOKACI NA HUTAWA

Koda Baku da wata matsala, Soyayya tana buƙatar hutu. Zama wuri ɗaya kai kaɗai, cimma wasu buƙatu naka, kashe lokaci kai da ƴan uwa da abokai, Yin wasu harkoki naka na daban. Kada ka damu idan Budurwar ka tace tana son ka bata lokaci Kaɗan domin ta huta. Yakan taimakawa Soyayya.

4. KA ZAMA MAI DARAJA DA ƘIMA

Macewa da wata damuwa data shuɗe a baya Yana saka muku daraja da ƙima tare da ganin girman juna saboda yafiya. Kawar da kai akan wasu ƙananan laifuka kan saka jin tsoro a zuƙatan masoya wajen daina yawan laifi. Yawan yiwa kai faɗa alamu ne na nasara a Soyayya domin masoya sukan samu ƙarin Fahimtar juna yayin da sukewa juna nasiha.

5. KU KULA DA ABUBUWAN DA KUKE SO NA MUSAMMAN

Ku ba yara bane, kun girma. Kune kuke gudanar da rayuwarku. Kuyi abunda kuke so mai kyau. Kuyi wasanni na tsokana amma mai ban Dariya, Soyayya kuke ba gaba ba, kada ku zauna ku kullum daga kalaman Soyayya sai shauki, wasa acikin Soyayya abu ne mai kyau ka tsokabe ta, itama ta tsokane ka. Musamman idan ɗaya na baƙin ciki zaku iya saka juna farin ciki ta wannan hanyar.


Karanta: 40-ROMANTIC-LOVE-TEXT-MESSAGES


6. KAUCEWA MUNANAN HALAYE.

Kada kana kawo ko bijiro da wasu abubuwa wanda basu dace da Soyayya ba, Kada ka tilasta acikin Soyayya, ita Soyayya ba aure bace balle ka bada umarni. Acikin Soyayya shawari kawai ake bayarwa, tare da dagewa akai. Kada ka zamo mai tsawwalawa. Ka zamo mai sauƙin hali, sauƙin kai sauƙin juyawa. 


7. KU KASANCE CIKIN SOYAYYA

Soyayya dole ce ta zamo abar morewa! Kuji daɗi, A ɗanyi Faɗa, kuma da yawan dariya da Soyayya. Wasu masu Soyayya suna mantawa da waɗannan abubuwan, haka yake janyo ɗaukewar shauƙi ko Soyayyar. A wurin ma'aurata takan iya sanya rabuwar aure. Kuna samun Lokaci Na musamman Dan wasan Guje guje, ko motsa jiki, ko wani wasa mai daɗi. Kuna magana da juna mai daɗi. Yawan yin waɗannan ƙananan abubuwan suna taimakawa Soyayya matuƙa.


Muna Godiya Abisa Gudummawar ku. Kada Ku Manta kuyi Mana SHARE.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)