BANBANCIN SAMARIN DA' DAKUMA SAMARIN YANZU A FAGEN IYASOYAYYA

0
BAMBANCI TSAKANIN SAMARIN DA, DANA YANZU. AFAGEN SOYAYYA.

Akwai bambance bambance tsakanin samrin da dana yanzu a harkar aurataiya da soyayya dayawa zan kawo kadan daga cikinsu.


1. Samarin Da Mafiya Yawansu Sunayin Aurene Badan Sha'awa Ba Illa Dan Kawai Aure Ibadane Kuma Sun Kai Minzalin Yinsa, domin wani anayimasa auren ma ya kwashe wata guda bai shiga dakin amaryarba, sabanin matasan yau mafiya akasarin su sunayin aure dan sha'awa ne ko dan wani nishadin na duniya ba wai danshi ibada ba. Illa anan shine dazarar aure yazamana maqasudin yinsa shine dan sha'awa to gaskiya ba zaitaba qarkoba. Abun daidai anan shine ka ka ƙudurce a ranka aure ibadane kuma silace da Allah SWT yasanya tazama sanadiyar biyan buƙatar ku dan kashe sha'awar da Allah yasanya muku ta bambancin jinsi.







2. Samarin Da Nagarta Sukebi, Ba Kyauba, su samarin da koda kina da kyau amma kina da mugun hali to wlh ba mai auren ki sai dai kikoma wani Æ™auyen da ba'asankiba ko wani mutumin banza ya nemeki. 

Amma Dazarar Kina Da Kyan Hali To Samari Zasuyi Miki Ca Aka Kowa Na Sonki Da Aure. Sabanin samarin yanzu mafiya yawansu sudai kyan fuska suke bi da zarar sunga yar fara ko ja saikaji suna wannan kalace komai munin halinta shi burgeshi take harso yake taimasa magana saboda ita kyakkyawace.



3. Samarin Da, Mafiya Yawan Su Suna Amfani Da Shawarwarin Iyayen Su Wajen Fara Neman Budurwa. Hasalima Wasu Lokutan Iyayene Kecewa Kaje Kayi Zance Da Wance Yar Gidan Wane In Kundai Daita Sai A Gama Ku Ayi Aure. Sabanin ayau sai saurayi aƙalla yakai shekara ko wata 5 yana soyayya da budurwa amma agidan su ba asaniba. Harsai ance yaturo sannan zaifada musu.
Yana Da Kyau Kafadawa Manyanka Zaka fara Neman Aure Tunkafin Kafara Zance Da Budurwa Zasu baka Shawara, Zasu yima Addau'a Zasu kuma ÆŠau Abun Da Muhimmanci.


4. Samarin Da Suna Iya Haɗiye Buƙatar Su Ta Ɗa Namiji, har saurayi yagama soyayya dabudurwa bai taba taba jikintaba ballantana makamancin haka. Amma mafiya akasarin samarin yau zakaga tun daga yanayi na hira yadda ake zama kusa da kusa alamu ne na aikata alfasha, ko hira amota, ko a lunguna ko aɗaki, ko da daddare, ko a ajujuwa, ko a ɗau budurwa atafi fati da'ita da sauran su hakan tasa kadan ne daga cikin matasan yanzu suke iya haɗiye buƙatarsu ga masoyansu. kaɗanne waɗanda basa jidadin junansu tahanyar kusantar zina.

4. Samarin Yanzu Mafiya Yawansu, sunfi son mace me ra'ayin duniyanci, wayayyiya kamar yadda suke cewa, sabanin samarin da, su me kyan hali suke so.




5. Samarin Yanzu Buri Yayi Musu Yawa Basa Zabar Dai Dai Su, Sai Wacce Take Ba'ajinsu Bace Da ka ganta Kasan Ta Dabance, sukuwa samarin da suna zabar daidai su.
Wacce Sunsan Zata Iya Haƙura Da Dukkan Abuncin Da Sukabata.

6. Dayawa Samarin Yanzu Su ke Taimakawa Wajen Lalacewar Ƴan Matan Yanxu, ta hanyar nuna SO da ƙauna ko sha'awa ga ƴan mata masu shigar banza, da shafe shafe dan suyi kyau da masu nuna su wayayyu ne. Sai kaga Abun Haushi Samari Harwani Haɗiyar Yawu Suke In Sunga Irin Waɗannan Matan, su kuma zuga su da zuwa gunsu koda ba dagaske suke sonsuba, Har Su Matan Suka Dauka In Ba Anyi Irin Wannan Shigarba Ko Shafe Shafen ba Bazaki Sami Saurayi Me Dan Dama Ba, daganan sheɗan ya hallakar da mafiya yawan mata su kama shiga ta banza, shafe shafe da yawace yawace na iska agari dan nunawa samari kwalliya da tsaraicincu, Sukuma Samari Su Ta Zugasu Tahanyar Zuwa Gunsu hira Dakuma Janyewa Daga Gun Yan Mata Na Kirki. Sabanin Samarin Da In Bakya Sa Kayan Kirki kinshiga uku wallahi ko yar limance ke kallon karuwa za anayi miki. kuma samari bazasu zo gunkiba dan za a zarge su ace lalata sukeyi tare

7. SAMARIN DA BASA NUNAWA ƳANMATA SU MASU KUƊINE KO ABUN DUNIYA, ILLA SUNANUNA SU JARUMAI NE SUNA DA ZUCIYAR NEMAN NAKANSU.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)