ILOLIN AUREN WACCE BATA SONKA

0

 KADA KA AURI WACCE BATA SONKA

Kasani ɗan uwa aure ibadane duk da kasancewarsa ibadane ba haka karazube Allah (S.W.T) ya umarta ayishi ba sai da yasa masa wasu shariɗai da Ƙa'idoji kafin ayishi yana daga cikin ka'idojin aure shine asami soyayya tsakanin saurayi da budurwa wata macen tana so shima namijin yana so.

Tabbas É—an uwa yana daga kuskure mafi girma a al'amarin aure shine namiji yakafe akan sai ya auri wacce bata sonsa, tabbas hakan kuskurene ku ma tamkar sayen kasadane. Ita mace wacce take sonka ma yaya ballantana wacce bata sonka.

Karanta: ABUBUWAN-DA-MAZA-KE-SO-JIKIN-MATA

Babu wani gata da iyaye zasuyima ko y'an uwa zasuyima a cikin tilastaka ka auri wacce bata son ka domin su Waɗanda zasu tilastata ta aureka koda sun tilastata ta aureka tofa gangan jiki kawai ka aura amma a zahirin gaskiya zuciyarta tana ga waninka ba kai ba dan haka koda tanaima biyayya dan iyayenta tofa ka rasa wani kaso me girma na aure wato soyayyar gaskiya da gaskiya wacce shauƙin ta da daɗin ta da muhimmancinta ba a iya siffantashi sai su masoyan ne kawai suke jinta. Tabbas ka auri matar da bata sonka tofa ka auri buhu bakin ciki.




Karanta:YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAÆŠUWA 

Idan akai rashin Sa'a kiyayyar takai kiyayya ko batada tarbiyya sosai ko shauƙin son waninka ya rufe mata ido wallahi shi yafi komai sauki ta kashe ka murus har lahira ta hanyoyi dayawa.

70% na matan da suke kashe mazajen su suna kashe sune akan basa son su, wasu tun a daren farko suke kashe angon wasu sai bayan shekaru.

Karanta: YADDA ZAKA GANE DACEWAR KU A SOYAYYA


MUHIMMANCIN AUREN MACEN DAKE SONKA

+ Wasu kan shiryawa miji makirce makirce kala kala.

+ Miji kan rasa farin ciki É—ari bisa É—ari irin na ma aurata kodama ta zauna.

+ Mace na zama cikin ƙunci koda akwai wadata.

Karanta: KALAN MAZAN DA MATA SUKA FI SO

+ Takan ga mijin kusan abanza komai zaimata koda ta haƙura.

+ Yawan gorace gorace ga miji a yayin da kuka sami sa6ani.

+ Wata kan gaiyato tsohon saurayinta har É—akinka kuma suyi lalata bakasani ba.

+ takan ci mutincin kowa a danginka dan ba tsoron saki take yi ba.

+ Kai kanka bazaka sake acikin sa'anninka ba domin sunsan ba auren soyayya kayi ba.

+ Hatta yayanka na iya fuskantar tsangwama da gori akan laifinka. da sauran matsaloli da dama.

Karanta: YADDA ZAKA SAKA BUDURWA TA KWARE MAKA

Awasu Lokutan Akan ɗanyi Sa'a Kaɗan Mace Ta Zauna Da Wanda Ba Ta So Tsawon Shekaru Har Suyi Ƴaƴaye.

Shima da irin wannan auren baikai auren soyayya ba daÉ—i, sannan shima cike yake da matsaloli koda bai kai ga kisan kaiba.

Dan haka É—an uwa mafi alkairi gareka ka auri wacce kake so, ta yadda tana sonka kamar yadda addini ya umarta.

Dan Uwa Babu Wani Addini Ko Doka Da Ta Yadda Da Auren Dole.

Karanta: ABUBUWAN DA AKE DUBAWA AJIKIN MACE KAFUN AURE


ME YASA AKEYIWA MATA AUREN DOLE

+ Kwadayi Da Son Abun Duniya Na Iyaye

+ Zaton Alkhairi na iyaye

Wasu iyayen yarinya a zuciyar su akwai zato na Alkhairi ga wani mutum kodan ilminsa ko basira ko wata baiwa ta daban hakan kawai yasa suke son haÉ—a zuriya dashi, to wannan zaton sai yasa su tilastawa yarinya auren wanda bata so.

Karanta: LAIFIN MAZA DA MATA ACIKIN SOYAYYA

+ Fitinar Budurwa

Wata budurwar bata da kamun kai iyayen ta sunyi sunyi taƙi nutsuwa tana daf da ɗauko musu abun kunya kuma taƙi futo da saurayi a irin wannan yanayin iyaye sukan iya aurawa mace kowaye koda bataso.

+ Kafiya da Aqidar Gargajiya ga iyaye musamman ma kakanni.

+ KwaÉ—ayin budurwa 

Mace Na Iya Aurar Wanda Bataso Dan Kwadayin Abun Hanunsa, inta sami abin da take so takan iya zama in bata samu ba takan kashe mijin ko tanemi ya sake ta.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)