YADDA AKE KULAWA DA SOYAYYA

0

  YADDA AKE KULAWA DA SOYAYYA

Kafun ka san yadda ake kulawa da Soyayya, kana Buƙatar sanin menene ita Soyayya.

What is Love?
Menene Soyayya
?
Soyayya Wani Matsanancin haɗin kai ne, da buƙata irin na yau da kullum. Na daga Abin ban mamaki, ji na sha'awa da girmama Juna. Soyayya Wani motsin rai ne Na kulawa da juna, ƙauna, da kama. Soyayya Sadaukarwa ce don taimakon juna, Da girmamawa, da kuma kula da juna, kamar a cikin aure.


Karanta:YADDA-AKE-DAINA-ISTIMNAI


Yaya Ake Kulawa Da Soyayya?
Yadda Ake Kulawa da Soyayya.
Idan a kace kulawa yana nufin Abubuwa da yawa dake ƙunshe a cikin kalmar Kulawa. Haɗuwar waɗannan Abubuwa na sanya Soyayya kasancewa mai cike da Shauƙi da Soyayya mai ƙarfi.

Daga Cikin Waɗannan Abubuwa Mun kawo kaɗan wanda za muyi bayani dan a fahimce su:


Abubuwa da Soyayya ke buƙata:

Lokaci: Lokaci Abune mai Muhimmanci idan ana maganr Soyayya, kamar yadda lokaci keda
Muhimmanci a rayuwar mu ta yau da Kullum haka yake Acikin Soyayya.
Duk yadda kake da mace Komin ƙarfin Soyayyar ku idan har ka gaza bata lokaci wadatacce, to sai Soyayyar ku tayi rawa.
Mace lokaci take so a wurin namiji, domin da lokacin da ka bata zaka iya Fahimtar ta, kasan damuwar ta, ka abunda take so, kasan abunda Bata so. Wannan dalilin yasa lokaci nada Muhimmanci a Cikin Soyayya.


Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-NUNAWA-MACE-SOYAYYA


Kulawa: Kamar yadda Masoya suka sani Soyayya kamar shuka take tana Buƙatar bayi so that it ca grow kuma tayi ƙarfi.
Kulawa na daga cikin Farillan Soyayya, Yadda Ake Kulawa da Soyayya Shine: ka zama available at any moment budurwar ka ta nemeka da wata buƙata wannan Buƙatar tana iya zama Financially ko shawari taimako daya shafi sanya jiki wato ƙarfi.
Duk lokacin da mace ta gamsu cewa kana tsaya mata acikin al'amurorin ta na yau da kullum to ta samu kulawar da take buƙata.

Tura Mata Saƙonnin Love Text Messages, Good Morning love text Messages, Evening text Messages, afternoon love text Messages and good night love text.
Indai Kana Ƙoƙarin tura mata waɗannan wasiƙu akai akai tare da Yawaita Kiran wayar ta, to zaka Samu zuciyar taYou may like: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

Yarda da Aminci: Idan Kana ƙaunar Mace Wajibine ka Nuna ka yarda da ita kuma ka bata Amincewa domin hakan zai bata damar sakankancewa dakai sannan zata samu Saukin Damuwa a ranta na cewa anya ka yarda da ita kuwa? Daga lokacin da mace ta fahimci ka Bata Aminci, Daga Lokacin Zata mai dakai ɗan lelen ta. Ko shawari aka bata saita tuntube ka kafun tayi amfani da wannan shawarin.


Karanta: YADDA-AKE-GANE-MATAN-AURE-MASU-BIN-MAZA


Kalamai: Kana Tsaftace Kalaman Ka Idan Kana Tare da budurwar ka. Kasan irin hanyar da zaka na magana domin gujewa yin Maganar da zata dameka wataran. Karka yawan Ɗaukan Alkawari indai kasa baka da halin cikawa yanxu ko anan gaba. Kada kana sakewa ƙawayenta suna saka ta tana faɗa maka abunda suke so kai mata. Duk maganar da zaka faɗa ta kasance gaskiya ne don gudun bacin rana.
Sannan Ku kasance cikin faɗawa juna kalaman Soyayya a fili na yabawa, koɗawa, wasawa, da hura kai Masoya nason haka.

Sannan A Duba Kalaman Soyayya masu dadi sosai.

You may like: YADDA AKE YIN SHAGWABA

Tsafta: Kana Tare da mace budurwar akoda yaushe kana Buƙatar ka zamo mai tsafta, Jikin ka na ƙamshi.
Su mata ƴan Tsafta ne akoda yaushe, kuma suna son mutum mai tsafta wannan yasa mata suke yawan sanyawa ƙafafun maza idanu domin ance tsaftar namiji Ƙafarshi.
Karka sanya a ranka cewa sai zaka je wurin ta zaka na tsafta A'a, Koda yaushe domin ko ba ita ba zaka iya haɗuwa da ƙawayenta a hanya ko a unguwa. Ƙawaye kuma ƴan fasa taya ne idan ba ai Sa'a ba.


Karanta: ABUBUWAN-DA-MAZA-KE-SO-JIKIN-MATAN-DA


Kyauta: Kyauta shine ka samu wani abunda budurwar ka take so na kayan tsaƙi, Abinci, ko tufafi etc kana Bata su. Given her a gift can make your Relationships more stronger than ever.
Sannan Kyautar kada ya tsaya akan ta kawai, Ƙannen ta Suna ciki, Ƙawaye na ciki da Sauran Ƴan Uwanta saboda tsaro.

Masoya A Kula Da Soyayya Domin Watarana Soyayyar Zata Kula Dakai. Ayi Soyayya Dan Allah Domin Soyayya Rayuwar Wasu ce.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)