WASIƘUN SOYAYYA MASU TSAWO (LONG LOVE TEXT MESSAGE)

0
ZABABBUN WASIƘUN SOYAYYA
Domin Inganta Jin Dadin Ku Da Farin Cikin Mu Daku Baki Daya, Ga Wasu wasiƙu Nan Domin Ku.


BUGUN ZUCIYAR MASOYA

Amincin Allah Ya Tabbata A Gareki Jinin Jikina. Da soyayyarki Dukkan jiki na ya ke motsi, sanyi ko zafi hakan baya sanya ni kasalar kallon hotonki, tsanani ko azaba basa sanyawa na rufe bakina da ambaton kyakkyawan sunanki. 

Tabbatuwa mafi bayyanuwa a raina shine soyayyarki. Kakkarfar iskar sonki ta lula da ni cikin sararin samaniya ta yanda bana hangen duk wata 'ya mace fa ce ke, babu wani juriya ko karfi da ke wanzuwa gare ni face da karfin ambaton harafofin sunayenki.

Zuciyata takan saurari bugun zuciyarki, yayin da kike furta mata kalmomin qauna daga baki mafi tsafta da dadin zance.

Idanuwana sukan makance na rasa ji da gani a duk sanda kyakkyawar surar jikin ki ta sauka a idanuwana, sautin muryarki ya kan narkarmin da zuciya har naji kunnuwana sun gaza tantance zakin muryarki illa iyaka tafi duk wani sauti zaki.

Bakina yakan zama tamkar idanuwana a bude a duk sa'inda yalwataccen murmushin ki ya bayyanu a gareni. Kafafuwa da hannayena basa iya daukar jikina a duk sanda kika furtamin lafiyayyun kalamanki.

Ke ce hasken raina, ke ce jina, gani na da duk wani abu nawa, sonki daga Allah ne, a lokaci daya da ganin tsararren hotonki na ji kibiyar son ki ta nutsu ga ruhina. Ke kadai ce a gareni da zuciyata, sonki azimun ne. Ina sonki da gaske.
Wasikun Soyayya
TSAGIN ZUCIYATA CE KE

Ina Sonki Har Cikin Zuciyata Ina Kaunarki Har Cikin Raina, Son ki Tamkar nunfashi ne a gareni, rashin ki a cikin rayuwata babbar musifa ce da bansan karshenta ba.

soyayyarki a daskare take cikin jinin jikina, akoda yaushe bugun zuciyata tana tafiyane da mizanin adadin son danake maki.

Adadin fitar numfashina yana fitowane da furucin kalmar ina sonki, Daga zuciyata nake miki wannan furcin.

Kisani cewa ni masoyinki ne ina kaunarki sosai bazan iya misaltamaki daukakar matsayinki arainaba, inason kiyarda da cewa arayuwata bazan taba mantawa dakeba koda munrabu Allah Ya Tsare.

Gangar jikina zata tafi da kwayar sonki da kaunarki. Tuna ninki nake akodayaushe begenkine yacikamin zuciyata ko cikin barcina hoton fuskarki nake gani ina kaunarki bazanso naga bacin rankiba arayuwata ke kadai naji inaso akoda yaushe da shaukin sonki da kaunarki nake kwana ina tashi.


SARAUNIYAR MATA

Amincin Allah ya tabbata a gareki motsin zuciyata. Raunanniyar zuciyata ba za ta iya juriyar rashin ki a gare ni ba, babu wani dadi da zai kai matsayin dadin da zanji idan kika kasance tare da ni ma'ana ki aminta da ni ki ce kina sona. 

Kunci ko damuwa baya hanani ambaton harafofin sunayenki domin sune mafi dadi gareni a jerin sunayen 'yan mata. Kyawunki ya kai matuka ta yadda bazan iya jeranta shi da dukkan wani kyau ba.

Rurutacciyar kaunarki ta cinye dukkan wani Soyayya ta wata 'ya mace da bake ba, da sonki zuciyata ke rayuwa. Zarah kike cikin taurari, Sarauniya cikin Sarakuna haka Gimbiya ki ke cikin kuyangi. Ke daban ce ga komai, kaunarki ita ce jarina, na kan manta da komai na tuna ki.

Tsiron sonki ya yalwatu a ruhina a lokaci daya dana kalli kyakkyawar surar jikin ki, kina da kyau kyawun da duk wani da namiji sai ya jinjina miki, ko cikin kyawawa ke ce Sarauniyar su. 

❤❤❤❤
Na kamu da son ki a sa'inda ban yi aune ba, ina son ki, zan ci gaba da son ki har abada. Ke ce kawai a zuciyata, ke ce alfaharina, da ke nake a koda yaushe.
Kece na bawa zuciyata.

❤❤❤❤

Soyayya Sa'a ce, Wani lokaci dace ce, Ana Samun riba ana samun faduwa, damar dana samu ta zuwa gareki Sa'a ce, Kyautar da kika damkawa zuciyata kuma riba ce, Yau naci kasuwa kuma wannan kasuwar zuciyarki ce, tunda kika amince mini zan sakaki cikin jerin yammatan da ko zan rasa nunfashi na bazan yada su ba, zan saka ki cikin farin ciki tsundum kamar an jefaki rafi, girman kine yar babban gida Sarauniyar mata, Kyakkyawa mai kyawu, Shugaba kuma Queen of my heart.

❤❤❤
.
Na saka ki a zuciya tace badan kikai ba, sai dan kin Chanchanta, na shigo dake rayuwata ne badan Inaso ba, sai dan zuciyata tana ƙaunarki, Na Bari Ƙaunarki Ta Kewaye Ruhin jikina ne saboda Ina Miki So na Gaskiya So irin wanda yafi na Uwa, so irin wanda bana Yaudara Ba, so irin wanda baki baya iya furtawa, Zan Iya Bada Duk abinda Na Mallaka Domin Na Mallakeki Jarumar mata. 


03
Zanso mu Rayu Dake cikin Aminci, Zanso Na Kasance dake Cikin ko wani minti dake shudewa na rayuwata, zan So ki So ni fiye da yadda ni nake son ki, Bazan Miki Alƙawarin Soyayya Har abada ba, amma na miki Alƙawarin Zan Rike Soyayyar ki har zuwa ƙarshen Nunfashi na, Da in rasa ki Shalelena Gwara Na Mutu banyi Aure ba, da Ace In ƙare Rayuwata Babu Ke, na gwammaci Shan Guba Domin Rayuwata Babu Ke Tamkar Rayuwar Shukar Fure ne da Ba'ai mata Ban Ruwa.


04
Kullum ina Jaddada miki Kalmar INA SONKI Domin Wannan Kalmar itace Iyakar ƙurewar Abunda Bakina Zai Iya Fada Akan Soyayyar ki, Duk Yawan Kalamai Duk Girman Bayanai, Duk Saukin Magana, Soyayya Ta agareki Bazata Iya Fassaruwa ba, da zaki Tsaga zuciyata Babu Abunda Zaki Gani Sai Gonar Danai Shukar Ƙaunarki , Cikin Jinina Kuwa Ba Komai Sai Ruhin Ki Da Yake Gudana Aciki. Ina ƙaunar Ki Ne Da Raina Bada Bakina Ba, Ina ƙaunarki Ne Da Zuciyata Bada Gangar Jikina Ba. Komai Naki Yayi Min.


05
Lokaci Mai tsawo na bata domin na fahimtar da zuciyarki soyayyata, kuma da duk kan alama hasashen zuciyata bai sabawa zahirinki Gimbiyata, Zuciyata da soyayyar ki na rene ta badan komai bah domin ki zame mata abokiyar rayuwa ta har abada, Koda jin sautin ki bazan iya yin nisa ba balle daga kallonki, Kamar Hasken farin wata haka nake hangen kyawun murmushin ki daga nesa domin ya kasance mai ɗaukar hankalin mai kallo, Tabbas a zahirinki bazan iya misalta matsayin ki da komai bah saboda kamar furen fulawa haka kike da ɗaukar hankali, Kowacce zuciya tana da nata burin ni tawa zuciyar kece muradinta


06
Amincin allah ya tabbata agareki hubby na adukkan lokacin da zuciyata zata harba jini kinanan acikin ta yakan harbawa ne tare d begenki, bazan taba dena tarairayarki ba a cikin zcyta ina ƙaunarki fiye da yadda uwa takeson ɗanta , koda Yaushe ƙishirwan tunaninkice ta mamaye acikin zuciyata ke kaɗai kike da zumar da zata magance Ƙishirwar dake acikin ruhina, aduniya jin muryanki ki

shi me cireni a ƙunci kallon kyakkyawar fuskarki shine cikar burina, kinsace tunania kin kame dukkan wata kofar da take shiga da fice na bakin ciki dakeyin supply acikin rayuwata,wayyo ƙaunata nashiga tarkon soyayya nakamu da matsanancin begen yar fara, madaideciya ga farin idanu Allah yacika mun burina nakasancewa tare da me amatsayin miji da mata...
Zanyi kewarki ƙaunata. Naki Akoda yaushe 


07
Babu abin da zan iya boye miki tunda kin riga kin sani kuma kin fahimta da cewa zuciyana ta riga ta jefani cikin tarkon da bazan iya kubuta ba, Kamar yadda na jima ina sanar dake cewa sonki kullum yalwa yake a cikin zuciyata, yake kara karuwa tare da yaduwa babu ƙaƙƙautawa wanda a yanzu sun riga sunyi karfi da banida iko, ko kuma zabi wanda Ya wuce na bin umarnin zuciyata, wacce takasance tana mai yi min jagoranci zuwa ko ina a duniyar soyayyarki!


YADDA AKE SACE ZUCIYAR MACE

Wasiƙa ce Ɗaya Tilo Amma Daɗin ta ya zarce Misali, Ku karanta a Natse kada kuyi sauri.

Nasan Za kiyi Mamakin Yadda Akai na turo miki wannan sako, amma ba komai bane wannan idan Za'a kwatantashi da abunda zai biyo baya.

Nasan wasu daga cikin halayyar ki, daya daga cikin shine bakya Wulaqanta mutane, wannan dalili yasa nace nima bari na gwada Sa'a ta ko Allah zai sa nayi nasara, dan Abun Sa'a ne.

Ba sai munje da nisa ba, 
Abun dake zuciyata ne nakeson na fadawa zuciyar da  tasa zuciyar tawa zama kamar bakuwar zuciya. Kin San mun dau lokaci tare, duk tsawon wannan lokaci akwai abunda na kudurce a raina da zuciyata wanda ban samu damar fadin shi ba, yau ma qarfin hali nayi duk da nasan bazaki Watsa mini qasa a ido ba, domin Ba Halin Ki Bane, kuma ba Tarbiyar bane.

(Sunan Ta) Ina Qaunar ki, Amma bansan yadda zaki kalli Al'amarin ba, koma ta yaya kika dubi lamarin, nidai nasan ina son ki, kuma daga Zuciyata nake fadin wannan Zance, Tare da tabbacin Zaki Min Adalci.

Nayi duba ne da wasu halaye naki da suke burge ni, kuma sune sila ta zamowa kamar bawa ga zuciyar ki indai kin karbi Soyayya ta.

Nidai banzo gareki da wasa ko Soyayyar qarya ba, da gaske nake, sannan domin Tabbatar miki hakan zanso ki bani amsa, sannan ki bani dama nazo mu gana koda sau daya ne.

Nidai ina Sonki, Ina Qaunarki, Soyayyar ta jima a zuciyata, nayi zurfin ciki ne saboda kada na bata miki rai ko na sakaki cikin kogin tinani wanda bazai bulle ba. Kuma na zabi nai miki magana ne yanzu saboda ina da tabbacin shine lokacin daya dace. 

Ki sani: idan kika karbi Soyayya ta, zan kasance cikin farin ciki, zan saka ki farin ciki fiye da yadda kike a yanxu, zan gina miki fada ta qasaita a cikin Zuciyata wacce za kiyi Mulki Irin wanda kika so, zan shagwabaki, zan Baki Kula Dai dai Qarfina, zan baki komai na duniya indai inada damar mallakar shi, zan zamo miki Rumfa domin Kareki daga zafin rana, zan Zamo Lema agareki Domin Tare miki duk wata cutarwa, Bazan Sakaki Kuka ko Damuwa Ba, wannan Shine Alkawarina

Ina fata zaki fahimcen yadda ya kamata.

Daga ni naki har kullum Kuma Garkuwa agareki ta ko wani fuska. (Sunan Ka)


ku Kasance Da Shafin www.Qauna.com.ng

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)