YADDA AKE FARA SOYAYYA

0

 YADDA ZAKA FARA SOYAYYA DA WACCE KAKE SO

Shin kana da wata wacce kake so a zuciyar ka ko wata wacce take sonka amma abun na baka wahala wajen nuna kaima kana so. To ka daure ka karanta wannan gajeren Bayanin da zamuyi domin ka san yadda zaka fara Soyayya. 


YADDA AKE FARA SOYAYYA

Da farko yana da kyau kayi tinani mai zurfi akan shin ma wacece wacce kake son nan, ta dace dakai? sannan zaka iya Soyayya da ita ko A'a.

Bayan kayi wannan tinani ka yanke shawari kuma ka ajiye cewa zakayi Soyayya da ita. Abu na gaba shine kayi duba zuwa gareta akan menene yake baka sha'awa da ita ko yake burge ka. Daga nan sai ka jin cewa wannan abun kawai shine kake kallo a zuciyar ka kuma yasa kake son ta.

Sannan sai ka bata Hankalin ka dakuma kulawa, Idan ka bata waɗannan zaka fahimce ta itama zata fahimce ka sosai, kuma zai iya jawo wani ƙarin abunda zaka so agame da ita wanda ma yafi na baya da ka gani.




You may like: YADDA-AKE-SOYAYYA-DA-QARAMAR-YARINYA


Ka faɗa mata Abubuwan da kake so da wanda baka so, Saboda tasa me kake so da kuma me ka tsana. Hakan zai bata damar Fahimtar ka itama sosai idan har tana sonka. Duk abunda za tayi to zai zama wanda kake so ne kaima zaka ƙara sonta sosai.

Ka ƙara yawan Lokacin da kake bata, Kana Buƙatar abu biyu Sune Kiran Waya da Kuma Tura Saƙon Text Messages. Sannan ya kasance idan ka kirata itama zata kiraka. Idan ka tura mata Text Itama zata dawo maka dashi. Yawan kira da tura Messages yana saurin saka Shauƙi a zuciyar masoya. Yana sa a tina dakai idan baka kusa.

Ka ƙara da wasanni da tsokana acikin hiran ku, Mata suna son Mutum mai bandariya sosai.

Daga Ƙarshe, Fara Soyayya Yana da Sauƙi Amma yana ɗaukar lokaci da hana aiki kafun ka faɗa duka. Amma ka sani kana Buƙatar shawari mai zurfi kafun ka fara Soyayya da wata mace.


HANYOYI GOMA DA ZAKA MAMAYE ZUCIYAR MACE


Farawa (Preface)

Kamar Yadda kowa ya sani Mata Suna Son Wanda Yake Kyauta ta musu ne, Duk irin yadda kake son mace Matuƙar baka kyautata mata to wataran zaka Haɗu da Fishin Late Comer.

Kamar Yadda Muke so Mata suna nuna mana Soyayyar su A Fili To Suma Mata Suna Son Ana Nuna Musu Soyayya a Fili kuma a Idon Kowa.

Wannan dalili yasa Zamu Kawo muku wasu daga cikin Hanyoyin da zaku bi domin zama daram dam a zuciyar mace batare da wani ya shigo tsakani ba.

1. Kana Yawa  Kiran Ta Da Safiya Kafun ta Karya Koma Ka zamo kaine kake tada ita da Safe, Kana Yawan tambayar ta Yaya Take, Ya Lafiyar jikin ta dana Ƴan Uwanta.

Sannan Sai Ka Baje Kolin Soyayyar ka Da Kalamai masu DaÉ—i masu ratsa Zuciya Kuna Wanda hankali zai É—auka.

Bayan Nan Sai Kayi Mata Addu'a Kuma Kace Mata itama tana Muku Addu'a.

Karanta: ABUBUWA GOMA 10 DA MAZA KE SO A JIKIN MATA

2. Kada Ka Yiwa Mace Ƙarya Domin ita ƙarya Ko Ba'a Soyayya ba Tana Lalata komai ta samu.

Idan Kana Son Mace Da Gaske Kuma Soyayyar Gaskiya Ce Ma'ana Soyayyar Aure To Duk Yadda Ranta Zai Baci Ka FaÉ—a Mata Gaskiya.

Idan Ka Yiwa Mace Ƙarya Daga Baya Ta Gano Abokina RIP Za'a saka akan Hoton ka. Dan Duk yadda kake son Ta Sai Ka Fita A Ranta Musamman idan Ƙaryar Ka Jima Kana Yi Mata.

Mata basa Son Namiji Maƙaryaci. Amma Hakan Fa Ba shine zai Hana Ka Sanin Hanun ka Ba. Ina Ƙara faɗa Kasan Hanun Ka Kawai.



Karanta: YADDA-AKE-GANE-MATAN-AURE-MASU-BIN-MAZA


3. Ka Nunawa Ƴan Uwan ka da Abokan ka Irin Yadda Kake Sonta.

Ita mace Tana son Taga Kana Nuna Ta a Dangi domin Hakan Na Basu Ƙarfin guiwar kasancewa dakai. 

Musamman Kana Yaba Mata a Gaban Abokan Ka, Kana Wasa ta Kana Hura Mata Kai. Hakan Zai sakata farin ciki sannan Kaima zata saka ka cikin farin ciki.

Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA

4. Ka Tabbatar Kana Biya Mata Duk Wasu Buƙatun ta Wanda Zaka Iya.

Ita mace Idan Tana Sonka Da Gaske Bata tambayar ka kuÉ—i ko wani abu. Kaine zaka Karanceta sannan Ka Gano Matsalar ta.

Wasu Matan Ko Kayi Musu basa Karba koda da Gaske suna Cikin Matsalar.

Yadda ake musu Shine Zaka Kira Ƙanwarta ko Ƙanin ta Sai ka Bashi Wannan Abun Kace Yaje ya Ajiye mata a gida. 

Daga Baya zata ji daɗin Haka Kuna Zaka Ƙara Shiga Ranta.

Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-BI-KA-SACE-SOYAYYAR

5. Idan Mace Tayi Maka Kyauta To Ka Yaba Mata a lokacin Kada ka 6ata Lokaci.

Su Mata ƴan Son a Yaba musu ne. Da zarar mace ta maka kyauta to ka nuna mata kaji daɗin wannan Kyautar, Kyan samu ka Haɗa Mata da Ƴan Kalamai da Zasu nuna Kaji daɗin Kyautar ta.

Sannan Kaima ka Samu Lokaci Kayi Mata Kyautar Bazata.

Karanta: HANYOYIN DA AKE BI A DAINA ISTIMNA'I (Masturbation)

6. Mata Suna Son Abun dariya Musamman Ma Namiji mai Yawan Bada Dariya. 

Yanxu Yanxu zaka Sace Zuciyar Mace Idan ka iya bada dariya.

Dan Haka Karka Na Tsumewa mace kana Ɗan Tsokanar ta haka kana ɗan Bata dariya koda Tana cikin Baƙin Cikine to zaka rage mata Wannan Baƙin Cikin. Kuma duk lokacin data tina da wannan abun dariyar Zatana tinawa dakai.

Karanta: ABUBUWAN DA SUKE BATA SOYAYYA

7. Inda Hali Kuna Fita Yawon Shaƙatawa, Kuna Zuwa Wajen Cin Abinci Da Wurin Kallon Abubuwan Morewa Idanu domin Hakan Zai saka mace farin ciki Sosai.

Kyan Samu Kuma Kana Riƙe Hannun Ta Kuna Kewayawa Mata Suna Son Haka.

Karanta: YADDA SAMARIN DA SUKA FI SAMARIN YANXU IYA SOYAYYA

8. Idan Kana Son Mace Ka Fito Fili ka faÉ—a mata cewa kana Sonta Kuma Ka Yarda Da Ita Sosai, Kuma Ka Nuna Mata Girman Ta A zuciyar ka. 

Sannan Ka Nuna Mata Yadda Kake Girmama Alƙawarin dake tsakanin Ku. Musamman Alƙawarin Aure.

9. Akwai Kalan Wasan Da Mata Basa So. Wajen Hira Kana Fahimtar Yanayin da Mace take ciki dakuma irin wasan da Take so a lokacin dakuma wanda bata so.

Kada ka mata wasa alokacin da kuke magana mai Muhimmanci.

Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

10. Ka Nuna Mata Idan Tana Tare dakai To Batada Wani Matsala. 

Ka Nuna Mata tana cikin Tsaro da Kulawar ka. Ka Nuna Mata yadda kake ji da ita Zakayi Komai akanka.

Hakan Nasa Mace ta sakankance dakai sannan Ta Yarda Dakai kuma Shaƙuwar ku zata Ƙara ƙarfi sosai.

Karanta: KALAN MAZAN DAKE WAHALAR DA MATA

11. Karka Lalata Mata zuciya Domin Duk Lokacin Daka Karya zucomace sau É—aya, bazata sake yarda dakai ba. Mata suna da Tsork kuma ba ko wace mace bace ake cizon ta sau biyu.

Rifewa (Conclusion)

Domin Inganta Soyayyar dake tsakanin Ku Kuna Buƙatar Hanyoyi Sabbi Domin Soyayyar nason ana Bullo da Sabbin Abubuwa masu Ƙayatarwa. Kuma Mata Suna Son Ana Zuwa Musu da Abunda Basa zato ko tsammani.


Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)