HALAYEN MATAN DA MAZA BASA SO

0

KALAN MATAN DA MAZA SUKE GUJEWA

Meyasa Ko wani Namiji Yake Gujewa mata masu Irin Wadannan Halaye Guda 7???


Matan hausawa da dama Musamman na wannan zamani kansu na kullewa, tinanin su na kafewa saboda maza na guje musu, amma sun kasa gane dalili. To ga dalilai gida 7 da suke sa namini Gujewa mace.


1. Macen Da Take Soyayya da namiji, amma kullum maganan Tsohon saurayinta ne a Bakin ta.


Duk macen da ta rabu da saurayinta na baya to bata mantawa dashi lokaci ɗaya, Wannan dalili yasa akwai matsala acikin zamansu da namijin da take tare dashi presently. 

Hatsari ne a Soyayya kina yiwa saurayin ki maganan tsohon saurayin ki, wato Ex Boyfriend. Zaki iya sake rasa wannan ma idan kika cigaba, maza suna da kishi fiye da mata.2. Macen da ta ɗauki soyayya abota kawai.

Kada ka batawa kanka lokaci idan ka nemi soyayyar mace amma tace maka sai dai kuyi abota. Akwai soyayyar wani a zuciyar ta, Rabuwa da ita shine mafi dacewa.

3. Macen Da take son Abun Hannun ka, Ba Kai Ba!
 
Yana da matuƙar muhimmanci namiji yayi amfani da duk wata hanya dan ya gane wani irin so mace take masa, wasu matan suna amsa cewa suna son ka ne saboda kana da ƙarafu a pocket. Kayi iya abunda zaka iya dan kada ka faɗa irin wannar soyayyar.


4. Macen da Bata da Lokacin Ka!

Duk macen da bata da lokaci naka, koda yaushe cikin busy, Alaji ka fece kawai, bata ɗau soyayyar ka da muhimmanci ba, bata da lokacin ka, bata baka muhimmanci, bata mutunta ka, ka nemi wata kaiwa.


5. Macen da Bata Kiran ka sai tana buƙatar wani abu!

Wasu matan basa taba kiran namiji a waya sai idan suna son wani abu daga gareshi, ko su  shiga cikin matsala, idan ka samu irin wannar macen kai Hoto ne kawai a wurin ka, Please avoid such types of women because they will only be wasting your time.
6. Macen da Bata da Yarda.

Macen da bata da yarda tana iya turo maka text sau 30 cikin hour 1, anjima kuma ta kira ka dan kawai ta ji   baka tare da wata ko baka jira da wata. Irin waɗannan matan sun yi soyayya a baya wanda basu share da kyau ba, tsoron da suke sai ya janyo musu matsala. Su hana ka sakat baka da katabus, Wannan sai yasa namiji ya guje ta.7. Macen da take son maƙalewa namiji (Overly Clingy)

Maza basu cika son mace mai yawa takura ba, irin macen da take son koda yaushe kana nuna mata soyayya kamar ƙaramar yarinya, kawai kanta ta sani, basa yiwa namiji uzurin shima zai buƙaci irin abunda yake mata. Wannan sai yasa namiji ya guje ta.


Overly clingy women tend to also have some sort of insecurities (Rashin Yadda) and need constant reassurance that you love them. An overly clingy person will never give you space and sooner or later you will begin hating the relationship and that is why you should avoid an overly clingy type of woman.


MATAN DA MAZA KE HAƘURA DA SOYAYYAR SU.


1. Mace Mai Yawan roko ba macen da zan baka shawari ka nema bace, irin waɗannan matan sukan saka Namiji kokwanto akan Shi suke so ko kuɗin shi.

Daga Ƙarshe namiji zaina jin kunyar haɗuwa dake, zaina jan baya har ki nemeshi ki rasa. Ya Fece!


2. Macen da bata Damuwa da Damuwan Saurayin ta, bata damu ba dan bashi da lafiya ko akan wani nashi bata damuwa, ko Yawan sakawa namiji ido da sunan kishi maza basa son irin waɗannan mata. 
3. Rashin Kulawa daga wurin Mace, Ba Namijin da zai kula da mace ya sata farin ciki, kuma bazai so shima ta mayar masa ba. Duk macen da bata bawa namiji kula, Bata bashi time. Shaukin soyayyar zai fita daga zuciyar shi. Zai ta danasanin abunda yayi miki. Daga ƙarshe wata tazo dare ɗaya kiji ana Next week ne bikin nasu!🤣


4. Idan Namiji Ya Fahimci bakya mashi Irin Ƙaunar daya ke miji, To zai sa namji yaji bakya son shi, yaji kamar baki cancance shi ba, Daga nan zai fara baya baya da lamarin ki. Watarana zaki tsinkayi Babu shi.5. Macen Da Take da Wuyar Sha'ani, Duk macen da take da yanga, yawan jan aji, nuna halin ko in kula ga saurayinta hakan yana wahalar da zuciyar Namiji, wanda kuma yakan kai ga rabuwar su. Saboda bata lokaci ne zama da irin waɗannan mata.


ALAMOMIN YANKEWAR SOYAYYA

1. Chanja Fuska.

Idan kuna soyayya ɗaya daga cikin ku ya fara chanjawa ɗaya fuska, zai fara ƙin duk abunda ɗaya yake so a sannu. Idan aka tambayi dalili sai dai ya faɗi ƙarya ko ai ta kauce kauxe.


2. Rashin Shauƙi (Lack of feelings) da Annashuwa

Rashin samun Shauƙi yana ɗaya daga cikin alamun ɗaukewar soyayya daga zuƙatan juna. Ko rashhin Annashiwa a fuska Ro Lallai ɗaya zai gudu yabar ɗaya.


3. Rashin Fara'a

Duk Abunda Kayi ko kikayi Zai saka fara'a a fuskar dayan ba indai yana son rabuwa da ke ko kai. Duk ƙarfin kalamai ko Murmushi or something else bazai nuna yayi mai daɗi ba.
4. Rage Yawan Magana

Idan Aka samu ƙarancin magana tsakanin ku, to ba La shakka An kusa rabuwa domin ɗayan ku ya gaji da ɗan uwan shi kenan.


5. Sabbin Halaye Marassa Kyau.

Idan masoyi zai rabu da masoyi sukan yi amfani da hanyar muzgunawa daya don kawai suna son rabuwa da juna, wannar ma wata hanya ce ta yankewa soyayya.


Ku cigaba Da Ziyartar Shafin mu domin Samun irin wadannan Dama Wasu Shawarin Ga Masoya. Muna Godiya


Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)