KALAMAN SOYAYYA GUDA 30 MASU DAƊI

0

KALAMAN SOYAYYA GUDA 30 MASU DAƊI


Yin soyayya da mace wani abu ne na musamman, ba'a wasa da soyayya, idan kayi wasa da soyayya, za tayi wasa da zuciyar ka, so idan kana son Budurwar ka, to anan wasu Wasiƙun soyayya ne na musamman guda 30 da zaka iya aika mata domin wanzuwar farin cikin ta.


 • Tun Ranar dana hadu dake, na yanke shawarin baki komai dana mallaka, sannan na mai dake macen da tafi kowace mace farin ciki a doron ƙasa.
 • Zuciyata ko da yaushe ta jiyo ƙanshin ki saboda kina cikin ta har abada, ina son ki Sosai.
 • Ki yarda dani ban taba son wata sosai kamar yadda nake son ki ba, Domin kin canjamin rayuwa.
 • Gaskiya, Bazan iya baiyana abunda nake ji tattare dake ba, amma in kina cikin zuciyata zaki gane.
 • Ban son wata ƴan mace sama da irin son da nake miki ba, kina sa naji cewa nima ina da muhimmanci a wurin ki a ko wani lokaci. • Ke ta musamman ce acikin rayuwata. Ina jin shauki idan ina magana dake ko ina tare dake.
 • Ya ɗaukeni lokuta da dama amma ban taba jin irin abunda nake ji tare dake ba. Ina son ki fiye da yadda bazaki iya fara tinani ba.
 • Kyawunki na gaskiya ne, kuma ke kyakkyawa ce, saboda lokaci na farko dana daidaita idanu na akan ki, na gane cewa na samu abokiyar rayuwa.


 • Soyayyar ki shine abu mai amfani da nake tsawon lokaci kuma nayi alƙawarin zan cigaba da sonki.
 • Soyayya dake wata ni'ima ce daga Allah, wacce bazan son na wayi gari na rasata ba, ina sonki.
 • Duk yawan dandazon taron jama'ar duniya, ina farin ciki da murna da na zama mutumin da zai yi rayuwa dake.
 • Duk ranar da bata tafi mini dai dai ba, tinanin ki ne yake dai daita min ita. Ina ƙaunarki.
 • Nasan zan iya zama mutum mai rikon amana, ina godiya da nuna tausayin ki yayin da na shiga lokacin damuwa.
 • Kinsa zuciya ta farin ciki.
 • Nayi farin ciki da samun kamarki abokiyar rayuwata.
 • Ina sonki ko me zai faru!
 • Duk irin yanayin da kike ciki yau, ki tina: akwai wani mutum a cikin wannar duniyar wanda yasan girman ki. Ina Son ki!
 • Me zan iya yi domin ganin kinyi Murmushi yau? Ki sanar dani ko menene zan yi miki.
 • Nagode da nuna hakurin da kike dani!
 • Ina son yadda kike saurin fahimta cikin sauƙi, Wannan kuma abune mai matuƙar muhimmanci a rayuwar mu ni dake.
 • Ina so ki sani, kin taimaka mini wajen zama wani mutum mai girma da ɗaukaka acikin wannar duniyar, I am ever thankful.
 • Cikin shauki nake murna saboda kece wani bangare na jikina wanda bazan iya baiwa kowa ba sai ke!

 • Zaki iya tuna lokacin da muka fara rayuwa tare? Farin cikin da nayi wannan ranar bana iya mantawa!
 • Ina matuƙar godiya da kika saurare ni, ina son yadda kike kulawa dani tare da mayar da hankalin ki kaina.
 • Soyayya me riba itace soyayya irin wacce muke dake, bazan manta kike kulawa dani ba, ni naki ne.
 • Ina son nayi rayuwa dake, yaushe ne zan kasance tare dake, na daukeki mu zagaya duniya.
 • Ki sani, yau kece farkon tinani na, kuma kece ƙarshen ganin, kece ƙarshen jinina.
 • Zan kasance a zuciyar ki tamkar mugun jini, na zauna a rayuwar ki tamkar jinin jiki, zanyi rayuwa dake kamar numfashi.
 • Sarautar Zuciya sai ƴar halak, wacce tasan mutunci kamar dai ke ɗinan. Ina son ki!
 • Sabuwar duniyar dana fada a soyayyar ki, shine abunda nafi jin daɗin shi a yanxu duk duniya. 


Idan kun ji daɗin wanɗannan kalaman, kuyi mana subscribe, ku sambaɗa mana comment, sannan kuyi following ɗin page namu. Muna Godiya.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)