ABUBUWAN DAKE SA BUDURWA IYA RANGWADA

0
ABUBUWAN DAKE SA BUDURWA IYA RANGWAƊA

1. YANGA DAI-DAI MiSALI 
Yanga tana matuƙar yiwa mace kyau ba namiji ba musamman ma budurwa kuma tana daga cikin abunda yake ɗaukar hankalin namiji zuwa gamace shine mace a wasulokutan kamar bata son yin wani abu, samari suna so suga suna soyayya da mace me yanga domin hakan na nuna musu sunkai ne. Amma kada tayi yawa sannan kuma karkiyiwa yan uwanki mata hakan zaisa su wareki.


2. IYA YI. 
Itama sifface datafi kyau ga yan mata musamman ma atsakanin su. idan mace tana da iyayi zakuga takasance itace shugaba a ƙawayenta kuma akan saurareta komai tafara ko tafaɗi ra ayinta hakan na matuƙar burge samari suga budurwa me iyayi.


3. ƊAUKAR KAI KO SHAN ƘAMSHI 
Ɗaukar kai gabudurwa yana matuƙar kara mata kwarjini agun samari domin ba kowanne saurayine ya isa ya kulata ba sai me aji kamarta, koma wanda ya fita in nace ɗaukar kai bawai girman kai ba. kada kizama common ta kowa. Ɗaukar kai da iyayi da yanga zakiyi su ne baya baya domin in sunyi yawa sun zama girman kai da raini.
4. KAMUN KAI 
Shine budurwa tabar shirmen nan na ƴan mata tazama ita ta dabance acikin ƙawaye ba kula samari kowani iri, ba shirme da shashanci. Kamunkai na matuƙar kai mace babban matsayi kuma harmanyan mutane na yabon budurwa me kamun kai.


5. Iya kwalliya da Dressing: Suna daga sahun gaba wajen maida mace ƙasaitacciya, bakuma lallai wai sai kina da tarin kaya ba ko masu tsada ba, a'a komai talaucin ki yazamana kayanki ko kala 4 ne ace koda yaushe a wanke a goge bakya futa sai kinyi kwalliya yazamana ako wani lokaci aka ganki to cikin tsaftar jiki da ta tufa Komin Talaucin ki. Sannan kwalliyarki tazama ta iyawa ba irin make up ɗinnan ba dazakibi duk kifante jikinki ki dogara da siffarki ta asali kawai hakan nasa kizama babbar mace abar yabo.
6. Kada abun hanunki yarufe miki ido atsakanin ƙawayenki ko waɗanda kuke mu'amala Dasu. Zasu gujeki.


7. Kada kizama me roƙon samari abun Hannun su, ko ƙawayenki hakan na rage kimarki hakan bai hanaki neman taimakon wanda kikasan zai tai makeki.


8. Kwatanta Aiki Da Ilminki Daidai Iyawarki.

9. TSARI NA RAYUWA kizama kina tsara komai naki daki-daki komai zakiyi.

10. Kula da lafiyarki mutunta kanki.
Idan Kina Bin Waɗannan Dabarun Tabbas Zaki Zama Mace Ƙasaitacciya Wacce Samari Masu Ji Dakansu Zasuyi Rububinki Domin Samari Suna Matuƙar Jindaɗi Da Wani Jin Isa Idan Sukaga Suna Soyayya Da Mace Ta Daban Ko ƙasaitacciya Wacce Ba Kowani Saurayine Zai Iya Tunkarartaba.

Wasu zasuyi tunanin sai dai inke kyakkyawace ne kawai zaki iya hakan sam ba hakabane shi so ba ruwansa da wani kyau sila kawai yake so, kowani ɗaya daga cikin halayen dana zayyana na iya sawa aso mace sosai Koda Bata Da Kyau To Ballantana Kuma Ace Kin Hada Halayen Duka. Akwai mutanen da burgesu kawai zakiyi suji sun antaya cikin sonki bawai kyanki ba.
Sannan kuma Waɗannan halayen kan boye muninki susa kizama ta daban.

Yan mata agwada agani.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)