KALAN MAZAN DAKE BAIWA MATA WAHALA

0

NAU'IN MAZAJEN DA IN KIN AURA ZASU BAKI WAHALA

Su Waɗannan Samarin In Kin Auresu Zaki Fuskanci Matsala Sosai Keda Ƴaƴan Ki Domin Zaki Iya Fuskantar Matsin Rayuwa Cikin Wahala Da Kunci Ko Rashin Walwala A Sakamakon Halin Su. Harma Da Duka Tsangwama Da Cin Mutunci.


1. NAMIJI MALALACI

Tabbas akwai matsala sosai idan kika auri namiji malalaci, domin dukkan haƙƙoƙin ki na dole zai kasa biya miki su haka zaki rayu cikin rashin abubuwan more rayuwa ƴaƴayen ki ma haka zasu zauna cikin wahala da rayuwar kaskanci.

Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAƊUWA

Namiji Malalaci Shine Me Yawan Son Jiki Bashi Da Juriya Wajen Neman Halal Hakan Tasa Baya Iya Wadata Iyalan Sa Da Abunci Ko Sutura Da Sauran Su.

Irin waɗannan mazajen matan su a ƙarshe sune ke rike musu gidan, suke kula da yaran su, kusan har megidan ma su ke ciyar dashi rabi da rabi ana masa gori kusan kullum matansu na cikin damuwa da nadamar auren su.


Karanta: AMFANIN-SANIN-ABOKIN-SAURAYI


2. NAMIJIN MATSOLO (maƙo)

Shi wannan yana da abun duniya sosai kokuma daidai gwargwado amma tsanani yasa baya iya magance matsalolin sa na rayuwa da suka zama dole.

Shi matsolo yana da dubu goma a ajiye amma sai yakasa biyawa iyalan sa bukatar dubu uku har sai ankai ruwa rana.

Shi namiji matsolo tun yana saurayi ake gane shi domin samun sa na kirkine amma baya iya yiwa kansa sutura ta kirki ballantana wani nasa, kuma ba wani planin yake tsarawa kansa ba na rayuwa.

sauran matasa sa'anninsa da basukaishi samu ba kuma sukafishi nauyi na ƴan uwa sun fishi sa kaya da shiga tsaf tsaf.

Baya Basu Abinci Da Sutura Yadda Yakamata Irin Wadannan Mazan Sai Sun Mutu Iyalan Su Suke Cin Dukiyar Su.


Karanta: ALAMOMIN SOYAYYAR GASKIYA


3. NAMIJI ME YAWAN KULA MATA

Zai yi wuya namiji me yawan kula mata ka rasashi da waɗannan ɗabi'un.

A. Almubazzaranci.

B. Zina.

C. Yawaita aure aure, ko auri saki.

D. Matsananciyar jaraba da naci wajen jima'i

E. Yawaita Mu'amala da mata barkatai.

Koda bashi da ɗaya daga waɗannan ɗabi'un to in kin aureshi kusan kullum kina cikin damuwa, domin kullum kina cikin zargi da fargaba da damuwa yau kin ganshi da wacce gobe da wacce ance miki saurayin wance ne, ko an ganshi da wacce kuma mutuniyar banzace. Hakadai kuma har tsufan su basa denawa.


Karanta: YADDA AKE RARRASHIN BUDURWA


4. NAMIJIN DA BAYA KULA DA IYAYEN SA ALHALIN YANA DASHI.

Irin wannan mazajen in kin auresu awasu lokutan zakisha wuya jama'ar gari na zaginki iyayen mijinki na zaginki suna ganin kece kike kwace masa abun hanu koda kuma kema baya kula dake yadda yakamata.

Sannan dukkan saurayin da baya kula da iyayen sa to kema wallahi ba zai kula dake ba musamman ma in kin fara manyanta ko kin tara yaya tofa dole kiyi zaman kaddara.

Su irin waɗannan mazajen ana auren sune kawai idan kin tabbata soyayyar da yake miki tafi wacce ke kike masa to anan za'a sau miki bakin aljihun sa.

Ɗiba yadda kike so in kina da imani da tsoran Allah zaki iya canjashi ya kyautatawa iyayensa da ƴan uwansa kuma yan uwansa zasu soki sosai amma idan kika ci ke kaɗai to zasuyi ta la antarki.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)