ALAMOMIN KAMUWA DA SOYAYYA
Soyayya Wata Ilhama ce da Allah yake wa bayin sa mace da namiji, Ba kowa ke gane cewa ya kamu da so ba, sai wanda ya taba yin Soyayya, Ga wasu alamu nan da ake gane Soyayya na shirin Shiga Tsakanin Mace da Namiji:
1. Yawan Ambaton Mutum
Idan Kaji kana yawan ambaton mutum, a baki ko a Zuciya, a fili ko a boye, ko yawan tunanin mutum Bayan baya nan, ko son jin muryar mutum, son zama kusa da mutum, son gani ko kalo. WaÉ—annan Wasu kenan Daga cikin alamun ka kamu da Soyayyar wanda hakan take faruwa dakai akan shi.
Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE
2. Bin Umarni
Idan kika ji kina yawan bin unarnin wanda kike jin kamar akwai Soyayya a tsakanin ku, Yana faÉ—a miki magana kin É—auka, yana ce miki Yi abu kaza kinyi, bari kin bari, ko kiji kinason Yace yanason abu kiyi mishi. Wannan Ma Alamu ne na Soyayya.
Karanta: ABUBUWA 10 DA MATA KE SO A SOYAYYA
3. Sadaukar Da Kai
Saudaukar Da Kai na Nufin: Kaji ko Kiji Mai Yace za kiyi ko Zakayi, Kaji Shauƙi Na Ɗiban ka, Marmarin Shi kake/kike. To akwai Soyayya Anan.
Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA
4.Yawaita kyautatawa
Kyautatawa a Soyayya babbar makami ne wanda ke saka Soyayya ta Ƙara Ƙarfi Sosai.
Daga Lokacin da ka fara jin kanason kana Kyautatawa Wata Ko Wani To Ka shiryawa shiga Soyayya domin nesa tazo kuSa.
5.Damuwa Da Wani ko Wata
Haka Kawai kaji ko kiji kin damu da wani, bakyason kiji ya shiga damuwa, kaji kanason yayi farin ciki, kaji kome zaka iya yi dan ganin rai nashi bai baci ba. Wannan Alama ce ta Soyayya.
Karanta: SHAWARI GOMA GA MASOYA
6. Farantawa wanda ake so
Daga zarar ka faÉ—a Soyayya zakaji fa duk abunda yake so zaka bashi, duk abun da yakeson ayi mashi zaka masa, ba ruwanka da kowa idan dai zai yabe ka. Kaidai damuwanka ka faranta mashi to Soyayya ce.
7. Kishi
Kishi Yana daya daga cikin abunda yake fara nuna alamun SO, Kaji Bakason Wani Yayi magana da wacce kake so ko wanda kike so.
DALILIN DAKE SANYA FARA SOYAYYA
1. Dace
Da zarar Kaga wani ko Wata, Da Irin Halayen Da Kake so, ko Dabi'u irin wa'yanda kake so, ko Kaga Yanayin Suffar Halitta, Yanayin Shiga, Sunyi Dai-Dai da irin wanda kake so ko kike so to daga Nan zakaji ka fara son mutum.
2. Ilimi
Da zarar kaga wata mai Ilimi da Nitsuwa Kuma tana aiki da wannan ilimi, sai abun ya burge ganin ka. Domin wasu sunfi son mace mai ilimin boko kona Addini.
Karanta: KALAN-MAZAN-DA-MATA-KE-SO
3. Alheri (kyauta)
Wasu kuma sunfi son mutum mai yawa kyauta, ko me son ayi Kyauta, ro zaka ji An Burge ka, kanason mai wannan Halin.
4.Gaskiya
Wasu kuma suna son mace ko namiji mai gaskiya ko mai kamanta gaskiya, wanda baya qarya Baya cin amana ko zamba cikin aminci, wanda Ba'a hada kai dashi ayi cuta Kamar dai Irin Na IZZAR SO.
5. Sakin Fuska
Wasu kuma suna son mutum mai Yawan sakin Fuska, wanda baya yawan bata rai ko saurin fushi.
Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA
ABUBUWAN DAKE KARA KARFIN SOYAYYA
1. Yawan Kyautatawa
Ka kasance kana Kyautatawa wanda kake so, kana yawan yi mashi kyauta.
2. Yawan Fadin Kalmar INA SON KA/KI (I Love You)
Kuna yawan fadin kalmar ina sonka daga zarar kun gama hira a zahiri kota waya,
3. Sabbin Salo
Soyayya na son koda yaushe kuna zuwa da sabbin salon Nuna Soyayya ga Juna. Kuna yawa bijiro da sabbin kalamai ba irin na yau da Kullum ba, kada kuna maimaita abu daya kullum.
4. Text Messages
Masoya suna son yawan tura message na kalaman Soyayya, amma basa iya turawa saboda wanda suke turawa baya dawo musu da amsa.
Abune mai kyau idan akai maka/miki text kayi reply Irin Wanda ake samu a www.Qauna.com.ng domin hakan yana qarawa Soyayya qarfi har ma da shauki cikin lokaci qalila.
5. Yawan gajeren Hira
Masoya yakamata suna hira amma kar tayi tsawo domin hira mai tsawo tana saka shauki ya ragu, Ku kasance duk bayan wasu mintuna ko Sa'an ni kuna hira Ta Soyayya mai saka Shauki Amma ba mai tsawo ba.
Akwai Wasu Amma Sai Nan Gama Ku Kasance Da Shafin www.Qauna.com.ng Muna Godiya da irin Gudummawan da kuke bamu.