AMFANIN AUREN MACE A NESA

0

AMFANIN AUREN NESA DAKUMA RASHIN AMFANIN SHI

Auren nesa a kasar hausa na nufin mutumin daya auro wata mace daga gari me nisa musali kamar É—an kano ya auri Æ´ar meduguri ko dan meduguri ya auro Æ´ar lagos kodai wani gari me nisa,

AMFANIN AUREN NESA

Yana daga cikin amfanin auren nesa gasu kamar haka

1. Ƙarancin kananan maganganu da gulmace gulmace saka makon ba danginta a kusa basu san meke faruwa ba agidan mijinta, taci me kyau bata ci ba, ba wanda yasani bare ya damu. Sannan duk iya gulmar mutum ba zai tashi yatafi meduguri ba daga kano dan hada gulma.

Karanta: AMFANIN AUREN BAZAWARA KO WACCE TA GIRMEKA

2. Ƙarancin Yawace Yawace.

Matar da ka auro daga nesa bata fiye yawace yawace ba sa kamakon batada dangi agari. amma kaga yargari kuwa kullun itace akan hanya zuwa yawo yau tatafi gidan biki gobe dubiya jibi wane ya karye tatafi jaje gobe auren wance kullum dai tana yawace yawace amma kuwa in yar nesa ce baka da wannan matsalar da sauki, domin ba kowanne abune yake faruwa a danginta taje ba sai wanda yazama dole. wata hatta ganin gidama ma sai bayan shekara shekara koma shekara biyu take zuwa ziyara sabanin yargari,





Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE

3. Rashin É—ora ma nauyin Æ´an uwanta wanda ya dace da wanda ma bai dace ba

4. Mace Tafi Sallamawa Miji Da Jin Shine Uwarta Shine Ubanta

Matar da bata da kowa agari sai mijinta tafi É—aukar mijinta amatsayin shine ubanta shine uwarta dan haka sautari ma ko bacin rai kukayi sai dai tashiga daki tai kukanta ta shafe kafin gari yawaye kowa ya huce idan abun yai tsamari karkari ta tafi gidan ubanta na aure shikuma dasafe zai nemeku yai sulhu sabanin in matar yar garice yar karamar magana zata yafa hijabinta tatafi gidan su sai kaje biko washe gari kowa sai yaji me ke faruwa.


Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA ME KWAÆŠAYI


4. RASHIN KATSALANDAN ƊIN IYAYEN MATARKA WAJEN TARBIYAR MATARKA DA NA ƳAƳANKA

Idan matarka Æ´ar garice zakaga tarbiyyar gidan matarka sai yashafi Æ´aÆ´anka wasu ma surukanka har katsalandan sukeyi acikin tsarin tarbiyyar Æ´aÆ´anka.

5. SAUƘIN HIDIMDIMU YAYIN WASU ABUBUWAN AL'ADA

Yayin bukukuwan al'adu irin su kai tuwon sallah, da wasu Al'adun da miji ke kaiwa gidan iyayen amarya.

idan matarka yargari ce to komai sai kayi kuma yadda akeyi in bakayiba kuwa kasha surutu da mita da gori daga danginta na uwa dana uba.

Amma in kuwa matar ƴar nesace zaka sami sauƙin yin abubuwan ko yaya kayimata shikenan tabawa wanda taga dama ta hana wanda bai mataba.

Karanta: YADDA-AKE-GANE-SIFFOFIN-SAMARI-MAYAUDARA


ILLOLIN AUREN NESA

1. ÆŠAWAINIYA RANAR AURE

Zakasha wahalar jigilar kaya da Æ´an biki da É—auko amarya daga guri me nisa

kusan dukkan yan uwan amarya zasu ce sai sunzo kuma kaine zaka ɗauki nauyinsu wasu ma har bayan biki basu da kuɗin mota dole ango sai yasamo kuɗi yasa wasu amota zuwa gida sa6anin auren kusa inda kowacce tatafi a ƙafarta kokuma tafiyar bata da yawa.


Karanta: YADDA AKE KULAWA DA SOYAYYA


2. ÆŠAUKAR NAUYIN TA YAYIN ZIYARAR MAHAIFANTA

Idan zata gaida iyayenta garin su watakila takai shekara 1 ko 2 ma rabonta da iyayenta kaga kenan in zata je gida sai kayimata hidima kun mota zuwa da dawowa da dan guziri watakila ma sai ka haɗamata da tsarabar da zata bawa iyayenta, sa6anin auren kusa inda da ƙafarta ma zata tafi.

3. ÆŠAUKAR NAUYIN YAN UWANTA YAYIN DA SUKA ZOMATA ZIYARA.

Wataƙila takan kai shekara bata ga kowa daga danginta ba kaga kenan duk sadda wani ko wata yar uwarta tayi doguwar tafiya ziyara kaga dole aimasa hidima sosai wataƙila ma sai kaimasa kuɗin mota bayan ya kwashi kwanaki agidanka, sabanin ace matarka yar garice.


Karanta: YADDA AKE RARRASHIN BUDURWA


4. Idan kuka sami sabani babba har yakai ga matar tatafi gaban iyayenta to takan iya zuwa ta shiryama karya da gaskiya bakada wanda zai shedeka kuma su iyayen suna iya yadda tunda ba agaban su kuke ba.

Yana daga illar auren nesa ga Ƴa mace yawan kewar gida da rashin ganin danginta a kusa da ita wata matar koda taji labarin wani abu yafaru a danginta sai dai tashiga daka dai kuka ba yadda zatai.

Sannan Mace Ta Kan Rasa Abokanin Shawara Na Jini WaÉ—anda Zasu Na Zuwa Gidanta Ko Ita Taje Suyi Zumunci Ido Da Ido.


Karanta: HANYOYI-GOMA-10-DA-AKE-SACE-ZUCIYAR-MACE


5. Idan akasami akasi tsakanin miji da mata har aka rabu to matar na shan wahalar É—iban kaya watama sai dai ta tsaya agidan makota har sai ta sai da kayan dakinta araha ta kyautar da wasu sannan tai kuÉ—in mota ta koma ga iyayenta. Inko bata da komai haka zai koreta sai dai yan yuniyal ko mutanan unguwa suyi mata kuÉ—in mota.

6. Ƴaƴan ku sukan rasa zumunci ingantacce da danginsu na uwa.

karanta: YADDA ZA KAYI IDAN MACE TAQI KARBAN SOYAYYAR KA

7. Yana daga illarsa shine idan namiji matarsa É—ayace to duk sadda taje ganin gida sai anga dawowarta wata takanyi wata guda ko sati 2 kafin ta dawo megida ya takura yakuma kosa idan ita kaÉ—ai ce.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)