GASAR KALAMAN SOYAYYA KASHI NA FARKO

0
GASAR KALAMAN SOYAYYA

Gasa ne Zamu Fara Ta SO Wato Gasar Soyayya.

Gasar Zamu Shiryata Ne Akan maza uku, Wanda Ya Iya Soyayya shine zai cinye gasar tare da Santaleliyar Budurwar da akai Gasar Akanta.


Misali:

Maza ne su uku, Abokai ne Matsayin shakuwar tasu takai Ace musu Aminai. Kawunan su a hade yake Musamman idan zasu aikata wani abu, ko ina ka gansu zaka kallesu cikin farin ciki, a gida, makaranta, aiki, kallon wasa, ko wani abu mai kama da haka.

A irin wannan Shakuwar tasu ne Watarana Sukai arba da wasu 'yan mata, wa'yannan 'yan mata su biyar ne, ko wanne taci kwalliya irin na kece raini, kana ganin matan nan kasan akwai inda suka nufa, Wa'yannan mata fa sun dauke hankalin mazajen nan uku, kuma gashi ba damar yi musu magana domin 'yan matan nan a bakin hanya suke, suko mazan sun fito ne daga gida cikin mota zasuje Daurin aure. 

Nan fa Suka sakawa 'yan matan nan idanu, kamar basu taba ganin mata kyawawa kamarsu ba, abakin hanya suke zasu hau hanya amma sun manta da hakan, saura qiris matukin motar ya kuskuri yan matan nan.

Daya daga cikin samarin nan yace kaga wasu mata masu zubin Hurul'ini, yana Bude baki yana Murmushi, abokin sa yace abun dake raina Ka rigani fada, Amma dai kunsan bazamu biye musu ba ana jiran mune ko? Direban motar ne ya fadi haka yana mai taka motar ta fara tafiya. Tafiya suke a hanya sai Abdallah yace Naga daya fa tamin, Abdul Yace Allah Abokina Nima fa na hango ko zamu juya ne kam?, Salim Yace badan Inda zamu nada Muhimmanci ba da yau saina gwada sa'ata akan su.

Suka cigaba da hirar wa'yannan mata har suka iso inda zasu, auren wani abokin su Za'a daura, sun iso amma Ba'a fara daurin auren ba sakamakon Lokaci kuma akwai mutanen da ake jira. Bayan isowar su kamar da minti 20, kawai sai ga Wadannan mata suma sun iso wannan wuri.

Abun ya basu mamaki ganin yadda suka sake ganin Wadannan mata kuma a inda suke, matan nan suka shige wannan gida da ake bikin.

Nan fa Kowa yayi hamdala domin a cewarsu, nesa ce ta matso kusa.

Salim Yace kowa ya zabi tashi suna fitowa mu janyesu gefe mu wanke allon mu. Abdullah yace kaima kayi magana, amma ni me farin hijabin ne tamin fa, Abdul Ya Wangame baki yace Kai alaji nima fa ita na hango. Salim yace akwai error kenan dan nima na ga fa kamar zata fisu a wurina. 

Ra'ayin su yazo daya anan (Masu karatu Karfa ku manta cewa Dama abokai ne) 


Kalaman soyayya

Bayan Daurin aure ya watse taron jama'a ya lafa, sai ga wadan nan mata sun fito daga wannan gida, wannan karon su Shida ne, ai kuwa mazan nan suna kallon su sukai yunkuri tinkaran inda suke, Amma Abdul Yace ku dakata wannar ta shidan da suka samo cikin gidan nan na wayeta sosai, inda nayi IT itama tayi IT a wurin kuma mun dan saba Sunan ta Naja. Abdullah yace to ai tazo gidan sauki, yanxu me abun yi kenan? Salim yace Abdul ne zai je ya Samo mana bayanai kawai, sukai shawarin haka tsakanin su. Abdul Ya sauka yaje ya taresu, kuma yayi Sa'a basui nisa ba.

 Abdul yaja Naja gefe suka gaisa yace kar na jaki da zance na bata muku time Wannan Me farin lufayan nakeson lambarta dakuma bayanai akan ta ya Za'a yi? Naja tace karka damu qawata ce sosai sunan Ta HANAN ka kirani da yamma muyi magana. Abdul yace Kaga yar gari ba damuwa Allah ya Kaimu Yammacin, sai kin jini. Ya juya Itama ta juya suka cigaba da Tafiya. 

Ya iske abokan shi a cikin mota na diri shi kawai ake jira su tafi. Bayan sun isa gida suna zaune bisa kujeru suna tattaunawa akan yarinyar nan da suka Gani, anan ne suka yanke shawrin Irin Dabarun da Zasu Yi wajen ganin dayan su ya mallake ta.


Ku cigaba da ziyartar shafin www.Qauna.com.ng domin Samun Wadannan dama wasu kalaman SO kona Soyayya.

Tags
  • Older

    GASAR KALAMAN SOYAYYA KASHI NA FARKO

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)