KALAMAN SOYAYYA GUDA 18

0

ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA

Kalaman Soyayya suna da daɗi a cikin Soyayya, kuma suna gyara Soyayya suna ƙarawa soyayya shauƙi da farin ciki. Wannan dalili  yasa muka sake shirya muku wasu wasiƙu na musamman domin jin daɗin ku na soyayya.

01

Soyayya na iya chanja mutum, domin ita Soyayya ba'a ganin, balle a koreta ko a hana ta shiga zuciya. Ba'a Cewa Soyayya ga yadda ake so, sai-dai kayi yadda take so. Ba'a Shiri wa Soyayya, ko babu shiri Idan taxo kamar mutuwa haka zata shiga Zuciyar mutum. Duk wanda yayi so dan Allah to shine keda riba, cikin Soyayyar ki babu sirki, na gani kuma na gamsu kuma na Tabbatar da ke me ƙauna tace ta hakika, ki sani, ni bazan taba son wata ƴa mace wacce bake ba, domin zuciyata bazata taba jindadin zama da wata ƴa sama dake ba, duk wani jin daɗin duniya bai damen ba indai babu ke. 

02

Rayuwata Fansarki ce, Zuciyata Tini ta Rikirkice, Kunnuwana Sun ƙi Karban zance, idanuwa na sun so su makance, duk sanadin Soyayyar da kika amince mini, Mulkin zuciyar Shine aiki na, samun farin cikin ki jindaɗi nane, Murmushinki Annashuwa Ce ga zuciyata, Duk ranar da kikai fishi Dani banida kwanciyar hankali, Ni Bawa ne ga Zuciyar ki.



03

Na Baki Kyautar Zuciyata, daga yanxu har abada kece mai mulkin zuciyata, babu kowa acikin ta sai ke, ƙaunarki ta mamaye gabadaya birnin dana gida a cikin xuciyata. Natsuwa ya ƙauracewa zuciya kafun na kifiyar ƙaunarki ta Soke shaiɗanin gake cikinta, Farin ciki ya Ziyarci Zuciyata a daidai lokacin dana iske ƙaunarki acikin zuciya yaje min satar SO. Kece tawa ta har abada.

04

Kece burina a duniya, banida wani buri daya wuce auren ki, zanso a kirani da bawan ki indai zaki nuna mini ƙauna irin wacce bata chanjuwa, kiso ni irin Soyayyar da uwa kewa danta, niko zan nuna miki ƙaunar da baki taba gani ba, Zaki zamo amarya, niko zan zamo angonki, musha Soyayya mai daɗi. Sarauniyata

05

Duk Tsananin Duhun Dare bazai hana ni ganin ki ba, duk Tsananin Zafin Hasken Rana bazai saka na gujeki ba, furucin da nayi na ina tare dake duk wuya duk rintsi bazai chanja ba, Babu wacce nake so acikin duniyar nan a yanxu sai ke, dake na damu, kece farin cikina, kece hasken idanuna, ke nake gani naji dadi a raina, banida kamar ki. Kece keda mulkin zuciyata kece Sarauniyar Xuciya ta, ke kaɗai nake so, Soyayyar ki ta Rufemin idanu bana ganin kowa sai ke, ina jin dadin Kasancewa dake ako wani yanayi, Ina Qaunar ki ne dan Allah Dan haka babu wani abu dazai sa na gujeki.

06

Duk Tsananin takurawar Abokai, bazai saka zugar su tasa na yasar dake ba, domin Soyayya ta agareki ta gaskiya ce, hannun da ya rike Soyayyar ki har abada bazai yasar ba, zuciyar data Killace ƙaunarki bazata jefar ba, kina cikin ruhina banida wata mafita cikin rayuwata in ba ke ba, ni dake zamu Kasance a raye har zuwa lokacin da Allah ya Kebe mana. Soyayyar zata Kasance har bayan mutuwa, duk irin daɗin da na shiga a duniya bazai saka na manta dake ba, domin kin min duk wata gata, kin bani duk wani farin ciki da nake nema, menene ribata idan na gujeki, rayuwata ce zata susuce. Ina ƙaunar Ki.

07

Sahibata, na miki tanadin wani farin ciki wanda ni kaina ban taba ganin irin shi ba, na miki tanadin wata Soyayya irin wacce baki taba gani ba, na ajiye miki wani gurbi a zuciyata wanda shine kyautar da zan miki mai girma a duniya, nayi miki wani gini na gida a cikin birnin dake zuciyata mai girman da yafi ko wani gini tsawo, acan zamu tare ni dake musa Soyayya, duk wani tattalin da zanyi yanxu saboda ke nake yin shi, kece asusu na, kece banki na, banida wani sirri wanda ban ajiye shi wurin ki ba. Bazan taba miki Ƙarya ba domin kin fahimce ni, bazan taba cutar dake ba, domin ina ƙaunarki.

08

Inason ganin fuskar ki ta cika da farin Ciki, inason naga annashuwa a tare dake, inason naga kina walwala na jin daɗi, banason naga bacin rai naki, bana son kiyi kuka, kukan ki tayar min da hankali yake, hawayen ki zazzabi suke sakani, nakan dimauce idan bakya farin ciki. Burina ni dake mu Kasance abokai na har abada, mu Kasance Aminai, mu Kasance ma'aurata, ni dake mu Kasance hanta da jini. Mu Kasance kamar ƙarfen jirgi dan ƙarfi, mu zamo kamar zinare ko ina aka kalle mu an ga mata da miji cikin Soyayya. Mu kasance masoyan juna na haƙiƙa.

 09

Zanzo gareki domin warkar da raɗaɗi da xogin da zuciyata keyi akan kaunarki, ciwon ƙaunarki ne abinda ke fisgar xuciyata ta jefani cikin duniyar tunaninki, Shalele ƴar lele sarakiya mamallakiyar xuciyana mai sarautar zuciyata sakon ƙauna mai ɗauke da tambarin zuciyata zuwaga Queen👑 ɗina kina Zuciyata my heart

 10

Banyi ba kuma bazanyi da nasanin kasanchewa tare dake ba, na yarda na aminche da soyayyarki agareni kuma ina matukar godiya abisa kulawar da nake samu daga gareki. Dalilin hakan ne yasa akullum nike rokon ALLAH Yachika mini burin kasanchewa ango agareki, inada yakinin chewa zan samu chikakken ladabi da biyayya agareki domin ke mace ce tagari wacce tafito daga gidan mutunchi kuma tasamu chikakken tarbiyya.

My besty ina fatan kema burinki kenan a kaina, Abar ƙaunata Zan iya manta komai amma ki sani ba zan iya mantaki ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinki ba, haƙiƙa daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki ya ziyarci zuciyata, wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wata Ƴa cikin walwala ina Ƙaunar ki masoyiya🙍🙍.

11

Bansan ya akayiba bansan wani lokaci ba dakuma yanayin da sonki ya dabaibayi zuciyata ❤ ba. A lokaci daya sonki ya shammace ni ya tumbatsa a zuciyata 💖. Bansan ya zanyi ba kuma bansan mafita ba domin dani 🙋🏻‍♂ da zuciyata❤ duka muna hannunki, idanuna👀 ke suke nunawa, bakina ke yake furtawa, nitsuwata shine kunnuwa suji sautin fitar zazzaƙar tattausar muryarki

12.

Amincin Allah ya tabbata ga amintacciya, Wacce zuciyata ta aminta da amincinta, Wacce nakeyiwa SON da bana yiwa kaina, wacce tazamto sarauniya me isashshen iko datake tafiyar da mulkinta a yalwatacciyar fadar zuciyata, Ina Tabbatar miki bawata bayanki, Ke kaɗai ce tawa.

13.

Ƴar uwata Masoyiya me ciren damuwa, Kece farincikin zuciyata💙 me bani kulawa, Kece burina, mafarkina, muradina, indake babu damuwa, Na amsa kira labbaiki habibiyata kiban kammalalliyar soyayyarki, Zan baki kulawa ta musamman irinta masoya na hakika. Bazan gujekiba dan banida tamkarki ako ina, kisani ni nakine ako ina ina matukar sonki!

14

Ina neman wata kalma wacce babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciyata da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Wannan alƙawarine da na yiwa zuciyarki. Ina son ki.

15

SO shi ne abun da ya dunƙule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya Bamu ankare ba, ina fatan ba za ki bari wani dan ƙaramin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Sahibata.

16

Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin sonda nake yi miki. Ina Son Ki.

17

Kece Murmushi Na Yanxu. Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniyar da muke ciki. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Samuwarki ne jin dadina Ina Son Ki.

18

Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me? Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fukafukai na tashi sama, Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shauƙi a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke, Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!


Ku kasance da shafin www.qauna.com.ng


Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)