Computer a Harshen Hausa 2

0
KOYON COMPUTER A HARSHEN HAUSA


BAYANIN BANGARORIN COMPUTER (PART OF COMPUTER)


 Computer nada bangare kashi daban daban, wadannan sune bangaren da zamu tattauna akai domin koya wa wa’yanda basu iya ba, ko suna neman qara sani game da computer.

Kada ku manta muna wannan rubutun ne a shafin mu na www.Qauna.com.ng muna godiya.


Part Of The ComputerBANGARORI A COMPUTER KASHI BIYU NE
 1. Na Cikin Computer (Software): Na Cikin Computer sune wanda idanu ke iya gani, ama ba’a taba su.
 2. Na Wajen Computer (Hardware): na wajen computer sune wanda ido ke gani kuma hannu ke iya tabawa.

AMFANIN BANGARORIN COMPUTER
 1. Akwai masu Shigar da Bayanai (Input Device), Misali: keyboard, Pointing Device, Joystick, Touch pad, Scanner, Light pen, etc.
 2. Akwai masu Fitar Da Bayanai (Output Device), Misali: Monitor, Printer, etc.
 3. Akwai wanda ke shigar da bayanai kuma yana fitar da bayanai (Input & Output Device), Misali: CPU (System Unit)
Part of the computer
 1. Monitor (Output Device)
 2. Keyboard (Input Device)
 3. Mouse (Input Device)
 4. CPU (System Unit) (Input/Output
Wa’yannan sune Bangarorin computer wanda suke da matukar muhimmanci ku sani, kuma computer zata iya aiki da iya sub atare da ta nemi wani abu ba, akwai wasu da dama kamar yadda muka fada mu computer nada iyakoki ma’ana aikin da kake da computer ba lallai haka kowa ke aiki da it aba, wani kallo yake da ita, wani jin Music, wani yana rubutu, da dai sauransu. 
Zamu dauke su daya bayan daya domin tattaunawa game da su.MONITOR 
Monitor shine ido na computer Screen: yana kama da TV da muka sani, kamar yadda muke kallon TV haka shima monitor yake nuna aikin da ake a cikin Computer. Amfanin shi a takaice kenan.

Computer MonitorKeyboard 
Keyboard: Yana da matukar amfani a game da computer, yana shigar da bayanai ne ta hanyar rubutu, da kuma wasu ayyuka wanda bata hanyar rubutu ba. Yana da part guda biyar sune kamar haka:
 1. Bangaren Alfabet (Alphabetic Keys): Sune Daga ‘A’ zuwa ‘Z’. 
 2. Bangaren Nambobi (Numeric Keys): sune 1,2,3,4,5,6,7,8,9,0.
 3. Bangaren Control (Control Keys): sune Ctrl, shift, Alt, Tab, Caps Lock, Windows Key, Enter, and Esc Etc. 
 4. Bangaren Navigating (Navigation Keys): sune Sama Up, Kasa Down, Gefen Dama Right, Gefen Hagu Left, Page Up, Page, Down, End, Home, Insert, Delete, Backspace etc.
 5. Bangaren function (Functions Keys): Sune F1, F2, F3, F4, F5, F6, F7, F8, F9, F10, F11, F12.


Keyboard
Mouse (Mice)
Mause ko Mice Shine ake kira da beran computer, yana amfani ne wajen shigar da bayanai, wato yana iko da pointer na cikin computer, wato Cursor. 

Yanada Bangare Guda Uku
 • Left Click: Aikin shi Shine Drag and Drop, Ma’an Dauka Da Ajiyewa, sannan ana iya selecting dashi, idan akayi double click ana bude abu dashi.
 • Right Click: Ana amfani dashi ne ta hanyoyi da dama, misali zaka bude abu idan ka taba right click zai bude maka Zabi wato options ko kace menu. 
 • Scroll: Aikin shi sama da kasa yayin rubutu ko duba document acikin masu yawa, zaka iya aiki dashi domin

  zuwa kasa ko sama, musamman wajen rubutu.


Computer MouseCPU
CPU (System Unit): Yana Nufin Central Processing Unit, Shine Kwakwalwan computer, shine yake duk wani aiki da computer take misalin aikin CPU shine Kwakwalwar dan adam ko Zuciyar dan adam aikin su daya.Computer CPU.
Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)