Computer a Harshen Hausa 1

0
COMPUTER A HARSHEN HAUSA


Sabon Tsari ne wanda zamu kawo muku yadda zaku koyi na'urar computer cikin harshen hausa, Kuma a Aikace Wato Practically, Dalla Dallah.

Sannan Wannan Shiri Zai dinga Karba Tare da Amsa tambaya akan wannan Topic.

Muna Karban shawari daga gareku Game da wani kuskure ko jan hankali, gyara ko wani abu me kama da haka.


GABATARWA (Introduction)

Computer na’ura ce mai aiki da kwakwalwa, wajen karba da sarrafawa da adanawa da kuma mika bayanai, a sigogi daban-daban. Wannan shine ta’arifin kwamfuta a takaice. Bayan haka, kwamfuta na tattare ne da manyan bangarori guda biyu; bangaren gangan jiki, wanda aka fi sani da Hardware, a turance. Sai kuma bangaren ruhi ko rai, wanda ake kira Software (manhaja), shima a turance. Kafin mu yi nisa, mai karatu zai ji ana fassara kalmomin turancin nan, sabanin yadda zai gansu ko yake ganinsu a cikin kamus (Dictionary). Hakan ya faru ne saboda a yanzu muna cikin wani zamani ne mai suna “turban masana”, ko Information Highway, kamar yadda bayani ya gabata a kasidar Matambayi ba ya bata. A wannan zamani, kalmomin harsunan duniya za su yi ta sauyawa ne iya gwargwadon fannin ilimi ko rayuwar da ake amfani da su. Don haka sai a kiyaye.



AMFANIN COMPUTER


Komfutoci ana amfani dasu wurin aiwatar da ayyuka a kamfani, masana'anta da kayayyakin da ake aiki a gidaje dasu. wadannan komfutoci sun hada da kananan kayayyaki har da manyansu, kamar abin dafa abinci na Microwave, Rimotin tsara TV, Robotics, na'urar komfuta' wayar hannu da sauransu. Komfutocin da aka kirkira da farko anyi sune dan taimaka wa mutane yin lissafi kawai, kamar 'abacus'. Sannan ansama cigaba a rayuwar Dan'adam ta yadda yafara kirkiran sabbin komfutoci dazasu taimakesa wurin yin ayyuka masu wahala da daukan lokaci.

Na'urar da aka fara kyerawa na komfuta dake amfani da wutan lantarki sune wadanda aka kyerasu a lokacin yakin duniya na II. Komfutoci na zamani da ake yinsu ayanzu suna dauke da []injina]]n dake aiwatarwa da gudanar da ayyuka acikinsu, kamar shashin gudanarwa da ake kira da turanci central processing unit (CPU), da kuma wani bangare na kwakwalwan komfutar dake kula da ajiye abubuwan da aka sanya aciki. Shi dai fannin gudanarwa ta komfuta itace ke aiwatar da ayyukan daya danganci lissafi da nazarce nazarce da sauransu.



Computer a Harshen Hausa





FANNONIN COMPUTER
Akwai Fannoni daban daban dasuka hada komfuta, akwai fannin kayayyakin dake waje wato output devices da na ciki wato input devices, da kuma

kayayyakin dake sanya aiki acikin komfutar da wadanda ake saukar da aiki dasu daga cikin komfuta. Wadannan sune; keyboards, mice, joystick, monitor screens, printers, touchscreen. komfuta nada matukar amfani a rayuwar dan-Adam.




Reference



ABUBUWAN DA ZAMU TATTAUNA AKAN SU.
1. Gabatarwa
2. Abubuwan Da Zamu Tattauna Akan Su
3. Bayanin Fannonin Computer da Aikin Su.
4. Yadda Ake Aiki Da Sassan jikin Computer na Waje (Hardware)
5. Yadda Ake aiki da Sassan Jikin Computer na Ciki (Software)
6. Microsoft Office Package
7. Shawari Ga Mai Aiki Da Computer
8. Rufewa



Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)