LABARIN SOYAYYA (RIBAR SO) ❤

0
RIBAR SO
Wannan labari da zaku karanta Gajere ne, sannan Muna Neman afuwar ku akan kuskure ko Tuntuben Harshe.

👉🏼Labarin wasu masoya ne su uku, saurayi Saleem da Aisha Da Kuma Fatima, saleem da Aisha Masoya ne na hakika wanda sukai shakuwa mai karfi, a iya tunanin mai hange dole ya hango cewa wadannan masoya sun wuce wani ya shiga tsakanin su, sun fara soyayya ne tun suna secondary school wanda sukai tsawon shekara hudu suna soyayya, bayan sun gama secondary sukai shawarin cigaba da karatu ko Aure amma saidai yin Aure bazai yiwu ba dalili kuwa shine lokacin da suka dauko maganar zuwa ga iyayen su, iyayen nasu suka ce musu su kara hakuri sai nan gama sakamakon rashin dacewar yin auren su a ‘yan qananan shekarun su, amma iyayen sunyi musu alkawarin da zarar sun kamala jami’a ko sun kusa kamala jami’a za ai musu aure.
Bayan Sun shiga jami’a sun fara karatu, amma ya kasance department nasu ya banbanta. Amma duk lokacin da basu da lecture zaka gansu tare cikin farin ciki da soyayya.

Gajerun Labarai


Watarana saleem yana zaune a wurin hutawar dalibai yana jiran Aisha kamar yadda ya saba a kullum, waya ce a hannun shi yana duba news, kawai ji yayi ta bayan shi a sa hannu an kwaci wayar dake hannun shi, kun san sabo saleem yayi tunanin Aisha ce waigawar da zai yi cikin murmushi sai yayi arba da wata daban wacce ba Aisha ba, Bai damu ba ganin cewa shi ba mutum bane mai fada, mutum ne mai sakin fuska ga kowa, ya danyi ajiyar zuciya yace: Baiwar Allah kiyi hakuri amma bansan an saka dokar hana rike waya a cikin school dinann ba.
Ta dubeshi cikin murmushi tace: to ko an hana rike waya a cikin makarantar nan dokar baza tayi aiki a kanka ba, na dauke maka ita.

Mamaki yayi dajin wannan amsar sannan ya danyi Murmushi yace to waye ni da doka baza tayi aiki akaina ba? Ya tambayeta.
Saboda kai babban mutum ne mai mutunci da kima, daraja da kuma muhimmanci a wuri na, indai kana tare dani bazaka bi duk wata doka a school dinnan ba na dauke maka ita, ta bashi amsa tare da cewa zaka bani wurin zama ne ko na cigaba da tsayiwa?

Zaki iya Zama amma sai kin fada mini dalilin daya sa nakai wannan matakin ba tare da masaniyata ba. Ta kada kai tace zaman dai yana da muhimmanci da dai an barni na zauna din abun zaifi dadin fada ko?
Saleem yace babu damuwa mu ai bama rowar wurin zama musamman ga wa’yanda suke kwace mana waya ba tare da mun yi musu izini ba.

Idan hakan ya bata maka rai kayi hakuri ta bashi amsa sannan ta zauna.
Ya matsa ta zauna kusa dashi, sannan ta kara da ce masa: Sunana Fatima kuma ina karatune a wannan makarantar department namu daya amma baka wayen ba, ko zan iya sanin sunan ka?

Saleem ya bata amsa da sunana saleem amma nayi mamaki muna deparment daya ban waye ki, koda shike ban cika shiga hurumin kowa ba sai wanda ya shi nawa hurumin, meke tafe dake? Kuma ya akai nakai wani matsayi a wurin ki har kika bani wannan girman?



Idan zuciya na son abunda take so idanu basa iya hanata ganin shi, kada kayi mamakin duk wadannan abubuwan da kaji na fada akan ka, na kasa rike zuciyata ce yasa shiyasa bakina ya furtasu gareka duk da banso hakan yanxu ba, amma kada kamin mummunan fahimta fa, kawai inason ka zama abokina ne a cikin makarantar nan kasancewar banida wasu abokai ko Qawaye, ina fatan bazaka kore Tayin danai maka ba?

Nan fa saleem ya shiga kogin tinani domin yasan irin wadannan kalaman da ta furto baya fita sai da soyayya a bakin duk wata macen data furta su. Gashi kuma bai shiryawa yin soyayya biyu ba, amma tunda tace abota maybe yasan hanyar da zai bullo mata, kodan Irin kishin da Aisha take dashi yakamata yasan dabarun da zaiyi mata.
Bayan ya dawo daga kogin tunanin daya shiga ne ya dubeta sannan yace bazan ki barbarki a matsayin Abokiya ba, amma ki sani Nan makarantar Ce, karatu muka zo yi ba wasa ko abota ba, amma tunda department namu daya ne babu damuwa na karbeki, amma dai bani wayata ina duba wani assignment ne.

Fatima ta mika mashi wayar tare da cewa naji dadin amsar data fito daga bakin ka, nagode dama gida na nufa yanxu zan wuce na hango ka idan bazaka damu ba na rage maka hanya mana tunda ina tare da mota. Saleem yace a’a nagode sosai banda yau wataran zaki ragamin, akwai abunda ban kamala ba tukunna, kuma naso saina gama zan tafi. Tace to dan Allah ka kula sosai domin nan jami’a ce, kar a sacemin kai banason rasa abokina. Karki damu tunda inada abokiya ai ko an sacen zata nemoni. Ta juya ta nufi inda motar ta take ajiye, shiko ya cigaba da jiran Aisha.


Haka rayuwar su a makarantar taci gaba yana soyayyar shi a gefe daya, kuma yana abotarsa a gefe daya, batare da ko wacce ta sani ba. Sun dauki tsawon lokaci a haka, Watarana suna ajin qarshe na gama jami’a Fatima ta bijiro mishi da batun soyayyar ta a dai dai lokacin da bazai iya cewa a’a ba, domin a tsawon wannan lokacin da suke tare sun shaku sosai wanda hatta iyayen Fatima sun sanshi sani na gaske, abokanshi na wannar makarantar sun san shakuwarsu.

A wannan lokacin ne saleem yake fada mata cewa: Banki soyayyarki ba, kuma bazanki ba, amma kiyi hakuri da abunda zai fito daga bakina, tun ranar da kika fara min magana a wurin zaman dalibai nasan wannar ranar zata zo, kuma na shirya mata, ina soyayya da wata kuma tana cikin makarantar nan, amma ba’a nan muka fara soyayya da ita ba, tun muna secondary school muke tare da ita, kasancewar ba department namu daya da ita ba shiyasa baki santa ba, amma lokaci yayi daya kamata ki santa, nidai namiji ne kuma addini na ya amince na auri mata hudu, dan haka ganin cewa ni dake akwai fahimtar juna zaki bani lokaci domin nayi tinani akan lamarin.

Fatima tace yanxu duk tsawon wannan lokacin ashe kana soyayya da wata amma ban sani ba, kuma baka taba fadamin ba? Saleem yace mata eh inayi amma kasancewar ni dake abotarmu tafi qarfi wajen karatu shiya baki santa ba. Yanxu dai zan shiga masallaci lokaci salla yayi za muyi waya idan kin koma, ki mikamin sakon gaisuwa wurin hajiya. Tace bazan fada ba tunda ka Qi zuwa ka gaisheta, saleem yace ba damuwa zanzo amma sai wataran............. To be continue
 
Zaku iya zuwa shafin mu na Facebook domin Samun sabbin labarai Wasikun Kalaman Soyayya



✍🏼✍🏼Habidam✍🏼✍🏼
Ku kasance Da Shafin www.Qauna.com.ng Domin Samun Labarai Masu Inganci.
Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)