LAIFIN MATA DA MAZA A ACIKIN SOYAYYA

0
LAIFIN MATA DA MAZA A ACIKIN SOYAYYA
DAKUMA DALILIN DAYASA AKE SAMUN BACIN RAI A SOYAYYA


1. Yawan Zurfafawa a soyayyar saurayi ko budurwa har SON yazama ƙauna. Wanda kuma hakan yakan jawo wa wasu illa

2. Boye soyayya a zuciya, wato zurfin ciki ƙin bayyana SO ga juna.

3. Ƙin nunawa masoyin gaskiya Soyayya mai kyau.


4. Ƙin ƙarfafawa masoyi guiwa akan son da kike ko kake mata na haƙiƙa. Ko wasa da hankalin juna.

5. Tara samari sama da ɗaya, kowanne kuma kice zaki aure shi ko kina sonsa, dole su gane ki wani a cikin su sai ya ankare, in wani ya haƙura, wani sai ya cutar dake kota yaya, ko tara ƴan mata sama da 1 danufin zaka aure su, sa'annin juna kuma.


6. Zabar saurayi ko budurwa da amunce masa ko mata kafin bawa Allah s.w.t zabi tahanyar addu'a, ko istikhara, domin koda bana gari bane ko, bata gari bace zuciya makancewa zatai akan so, sai kuma Allah yajarrabeku. Dan kun saba sunnar annabinsa s.a.w.


Karanta: ABUBUWAN-DAKE-SA-MATA-DA-MAZA-YAUDARA

7. Biyewa shashashun samari ko ƴan mata da nuna musu SO kuma kin san basuma tashi yin auren ba.

8. Rashin haƙuri akan laifi ɗan ƙarami.

9. Saurin fushi da rashin bincike a nitse, matsanancin kishi.

Dukkan su abubuwane da mata da maza suke yi a soyayya amma SO ne yake sa yin hakan, matsalar kawai in an samu kishi, ko sunyi zargi ko an bata musu rai, to baza su nutsu suyi bin cike a hankali ba, tahan yar azauna da masoyi a tattauna asami mafita, me laifi yaba da haƙuri me gaskiya ya dau gaskiyar.


Su mata sai dai su canjama ko sudena kula ka, ko su bata rai suƙi sakin fuska koma suƙifitowa inkaje hira ko suƙi daukar kiran ka ko suyi ta yima tsaki da sauran su, koda baka san me kayi ba, sukuma maza sutayi miki mita, faɗa ƙin kiranki da sauran su.

10. Matsanancin jan aji ga saurayin da a ka amunta dashi wato su mata, sukuma maza rashin bawa masoyiya kulawar da ta dace kamar kiranta saƙo, zuwa hira akai a kai.

11. Rashin nunawa juna soyayya bayan an aminta dajuna akan gaskiya.

12. kwadayi da tambaye tambaye, tambayan saurayi wasu abbuwan.


Karanta: ILLOLIN-CIN-NAMA-DA-YAWA-GUDA-BIYAR-5


13. Rashin boye sirrin ki ko bayyana kome game da soyayyarki ga maƙota ko ƙawaye.

14. Rashin tallafawa masoyiya da wasu abubuwa na buƙata

15. Boye wani abu ga masoyi ko yimasa Ƙarya, fitsara, rashin kunya.


16. Ɗaukar tsawon lokaci ana soyayya kamar shekaru da yawa.


17. Saba dokokin Allah da sunnar annabinsa s.a.w.

18. Rashin uziri ga juna da tausayi.

19. Ƙarya da yaudara, da girman kai.

20. Cin amana, jahilci, rashin cika alqawari mugun hali.

Allah yasa mu gyara ameen

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)