KALAN MATAN DAKE JAN HANKALIN MAZA

0
DALILAN DAKE SA KA AURI MACE


AURE wani fanni ne mai muhimmanci. Babu abunda yakai samun abokiyar zama ta haƙiƙa wacce zaku yi tafiya mai tsawo tare. Dangane da haka, Maza sukan maida hankalin su kan wasu abubuwan da suke so a tattare da su matan na daga Kyawu, Iya Magana, Iya Soyayya da Sha'awa. 

Waɗannan nada Muhimmanci amma ba zasu zama sune a sama ba wato farko (Top Priorities) wajen neman ƙulla Soyayya mai tsawo har takai ga aire.

Zamu Zayyano muku wasu Abubuwa da zasu taimaka sosai wa namiji wajen neman matar da zai aure.
  

1. Auren Mace mai Mutunci: Duk macen da take da Value Itace mace mai mutunci Kuma ƴaƴan ka zasu taso cikin mutunci da mutuntawa. Ba wacce zata zamo mai son kanta ba. Mace mai mutunci Duniyace.
2. Mace Maras Kwaɗayi.

Duk macen da batada kwaɗayin kuɗi, ko mulki idan ka aure Ta zata mai dakai Sarki. Domin shi kwaɗayi wani aibu ne wanda ke shiga zuciyar mata, duk macen da wannan aibun ya shafe ta zaka ga tana rayuwa irin na ƙarya zata na ɗagawa ƙawayenta kai tana girman kai.
Karanta: ILLOLIN-CIN-NAMA-DA-YAWA-GUDA-BIYAR-5


3. Ka auri mace dan Dabi'arta

Macen da take ɗaukar komai bada wasa ba, wacce bata yawan dariya sai ɗan kaɗan, wacce bata yawan wasa saima yana gundurar ta. Gidan ka ana buƙatar shine ya zamo ba Cikin wasa kullum ba, ba cikin Shiru Shiru kullum ba. Ana son koda yaushe ya kasance A tsakiya.


4. Ka auri mace dan Tana da Tausayi.

Tausayi alamu ne na Imani daga zuciya. Tausayi yana ɗaya daga cikin dalilin ƙarko na aure ko jimawar shi. Idan macen da ka aura tana da tausayi, zaka ga duk halin daka shiga zata tsaya dakai duk wahala duk rintsi. Idan har kuna tausasa junan ku rayuwa zata zo muku da sauƙi.
5. Ka aureta dan Addinin ta:

Auren mace mai addini yana da fa'ida. Zakana Ƙaruwa da addinin ta wajen aikata abubuwa masu kyau. Sannan ƴaƴan ka zasu tashi suma da wannan addini domin sunga ana yi a gidan su kuma ana koya musu. Addini shine ginshiƙin rayuwa.


6. Macen data Kwanta maka

Duk wacce zaka aura ka tabbatar kana son ta kada ka auri mace amma ranka bai kwanta da ita ba. Zaman aure yana buƙatar kulawa da Soyayya tare da farin ciki, idan har babu waɗannan To wannan zaman zaina samun Wasu tangarɗa.

Karanta: AMFANIN-CIN-GAUTA-DA-YALO-GUDA-10

7. Kada ka auri mace da take yawan Tara samari.

Yawan Tara samari alamu ce na rashin kamun kai, duk macen da take da kamun kai bazata na biyewa ko wani saurayi ba sai wanda ya nemeta da gaskiya. Rashin kamun kai na iya jefa mace cikin hali irin na Besty.

8. Auri mace dan Kyakkawan Alaƙarta.

Duk macen da take kula da iyayenta da ƴan uwanta, danginta da yayunta ƙannenta manya da ƙanana to Itace Wife Material. Wannan itace irin macen da take renon Yara masu Hankali da Biyayya.


9. Ka Auri mace dan kyawun Ɗabi'unta.

Kyawawan ɗabi'u Ko Halaye kan iya zama na har abada bazasu janzu ba. Duk macen da take da ɗabi'u masu kyau to mijin ta zai caba.


10. Macen da Bata da Girman Kai.

Babu wani namijin da zaiso mace mai girman kai wacce take jin kanta. Duk macen da Za'a ƙirata Mata (Wife) dole ne ta zamo mai ƙanƙan da kai ga mijin ta. Ta zamo kamar zata bauta maka saboda Biyayya. Ta girmama ka amatsayin miji.

11. Ka auri mace saboda iya kula da Yara.

Duk irin Ingancin da Makarantu ke dashi wanda zaka saka ƴaƴan ka, Matar ka ta fisu ƙwarewa. Dan Haka kada ka auri macen da bata iya kulawa da yara da karutun su ba.


12. Mace Mai Basira. 

Auren mace mai basira Duniya ne Alaji. Yana da ban sha'awa kaga matar ka na control na wasu Al'amurorin ka Yadda kake so har ma ta fika ƙwarewa akai. Mace mai basira ta iya kula da miji.

Idan ka samu mace mai Waɗannan abubuwan ko wasu daga ciki, ka bata lokacin ka. Kada ka kasance cikin hanzari da rayuwa. Ka tabbatar ta yarda dakai. Ka yawanta Addu'a. 

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)