YADDA AKE SA BUDURWA TA KWARE A SOYAYYAR KA

0

  YADDA ZAKA SA BUDURWA TA KWARE MA


Shin kasan hanyoyin da ake bi wajen saka mace tace tana sonka? Kana son kasan Hanyar da zaka sa mace taji tana Sonka? Kana damuwa saboda bakasan yadda zaka narka ta cikin begen ka ba? Kason sanin abunda za kayi ka janyo hankalin ta? To ka biyomu sannu a hankali acikin wannan rubutun zamu Sanar dakai Abubuwan da za kayi ka sanya mace jin Soyayyar ka cikin zuciyar ta cikin Sauƙi.

Yadda Zaka Sa Mace Ta So Ka!

DAGA SHIGAR KA

Ana Magana ne akan yadda zaka janyo hankalin ta sannan kasa ta faɗa Soyayya dakai. Ina baka shawari da ka fara chanja yanayin Shigar ka da kayan da kake sakawa. Domin mata suna son namiji mai tsafta da Ado me kyau. 

Karanta: YADDA AKE SACE ZUCIYAR MACE

Sannan ka nemo irin shigar da take so kuma yafi burgeta. Zaka san haka ne ta hanyar ganin irin tata shigar, Shin macece mai son Ɗaukar wanka, kayan Atampa take sakawa ko na bature ko na Al'adarsu. 

Bayan ka samo wannan sai ka haɗa da naka da nata kana sakawa don ka burgeta.

Karanta: YADDA-AKE-GANE-MATAN-AURE-MASU-BIN-MAZA

KANA YI MATA KYAUTA

Sayawa Budurwa Kyauta yana daga cikin Abubuwan da suke saye hankalin ta. Harma Wasu na Ganin cewa idan kana son mace tayi saurin cewa tana sonka, to ka Ka yawanta bata kyaututtuka. Domin mata suna son Kyauta sosai kuma basu Kyauta zai sa mace ta kasa mantawa dakai domin zata na tinawa da Kyautar da kayi mata da kuma kai kanka duk bayan wasu ƙananan lokuta.



You may like: YADDA-AKE-MALLAKE-YAR-MASU-KUDI

KANA YAWAN YI MATA MAGANA KO HIRA

Kayi Iya Ƙoƙarin wajen samun hankalinta kuna hira koda ba yawa a hankali kana mata kalamai masu daɗi hakan zai gina Soyayya mai ƙarfi a zuciyar ta. Kuma magana da ita zai Taimaka wajen sanin shin ta kirki ce ko ta banza. Sannan zata fahimce ka kaima ka fahimce ta. 

Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-NUNAWA-MACE-SOYAYYA

Idan haka na faruwa da kanta zata fara tinanin Soyayya a dakai daga nan ka cinye zuciyar ta tare da Rubuta Littafin "How to make a girl fall for you" a Cikin Ruhin ta.

KANA MATA RAKIYA

Idan akwai Dama Kana samun lokacin da zata anguwa ko aika ko wani wurin kana raka ta, idan tace A'a kace kana son ka tabbatar mata da tsaro ne. Daga lokacin zata fara gane manufar ka na Soyayya. Kuma haka zai ƙara mata shauki na jin cewa lallai ta samu mafaka a Soyayya. Kuma zata saki jikinta dakai domin kana damuwa da ita.

Karanta: SHAWARI GOMA GA MASOYA

Ka Sani Ba kana so ta faɗawa Soyayyar ka bane saboda kuɗi don haka kada kace zaka kashe mata kuɗi sosai ba dai dai bane, kaidai kasanya Murmushi da dariya yayin rakiyar taka.

KA TAIMAKA MATA YAYIN BUƘATA

Ka zamo na Farkon Bata Agaji da Taimako yayin da take cikin damuwa ko Rashin Lafiya, domin yin haka zai Taimaka Wajen tattalo gaba ɗaya zuciyar ta zuwa gareka. Kuma duk lokacin da take cikin damuwa zata so ace kana kusa da ita domin ka shiga zuciyar ta. Saidai ka Kiyaye kuma ka tabbatar Soyayyar gaskiya take maka.

Karanta: YADDA-AKE-ZAMA-DA-MIJI-ME-SAURIN-FUSHI

SAKIN FUSKA

Ba sabon abu bane domin mata suna son maza masu sakin fuska da Ban dariya a kusa dasu. Namiji mai Ban Dariya yana saurin sace zuciyar mace cikin sauƙi. So kayi ƙoƙarin Sata Dariya domin Kawo Murmushi a fuskar ta. Ka tina fa ba sai ka zamo ɗan Comedy ba, amma ka fitar da ita daga ɗaure fuska Zuwa sakin fuska ta hanyar data dace kamar nuna mata rashin bacin ranka, yawan Murmushin ka, da nuna alamun ka farin ciki idan kuna tare. Shima akwai shi acikin "How to make a girl love you"

Karanta: YADDA-AKE-GANE-SIFFOFIN-SAMARI-MAYAUDARA

KANA MATA GODIYA

Mata suna son Ana Nuna Musu An Ji daɗin Abunda Suka maka. Musamman idan suna sonka To kana Yawan yi mata godiya da zarar ta yi maka wani abunda kaji daɗin shi. Yawan godiya mata suke so domin yana jan hankalin su zuwa ga namiji.

Karanta: HANYOYIN-MALLAKE-USTAZAI-MAZA-DA-MATA

KA YABA MATA

A dai dai lokacin da Kake nuna mata godiya idan tai maka abun da kaji daɗi, haka yakamata kana yabon ta sosai fiye da yi mata godiya ma. Domin su mata Suna son yabo dan Sunfi Sarakuna Son a Yaba Musu. Ko Bata mata rai kayi Yabon Surar ta ko Kwalliyar ko shigar ta zaisa ta sauƙo cikin sauƙi. Kuma har Alfahari wasu matan suke idan suka samu Namiji mai yabon su.

Sannan Kuma Mata Ku Sani, Duk Waɗannan Abubuwan ku ake yiwa amma suma mazan Suna Son Ayi Musu. So Idan Kinga Namiji kuma kinji Kina Sonshi Zaki Iya Amfani Da Waɗannan domin janyo hankalin shi.


Duk mai Wata Tambaya ko Ƙarin Bayani ya Ajiye mana Comment.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)