GASAR KALAMAN SOYAYYA KASHI NA KARSHE

0
GASAR KALAMAN SOYAYYA

Wannan Shine Kashi na Qarshe Cikin Gasar, Ku ajiye mana comment da Amasar Zabin Wanda yaci Gasa.

Sannan kada ku manta ku sambada mana subscribe domin samun sabbin posting da zarar mun dora.


Gasa ce Suka Shiya Shirya Amma Mai Tsafta, kuma wannan gasa sun amince duk wanda Hanan Ta Zaba to zasu mara masa baya. 


Gasar dai itace: Kowa zaije gareta, ya nemi Soyayyar ta, Duk wanda ta Amincewa kuma har aka kaiga maganar aure, to sauran zasu goya mashi baya, ba tare da Wani rigima ba.

Kunsan idan Za'a gasa dole ko wanne zai nemi yazo na daya ne.

Gasar ta fara tafiya yadda suka tsara saidai kuma kash, Hanan fa Taki Bada fuska domin duk qoqarin su abun na neman yaci tura. 


KALAMAN SOYAYYA


GA YADDA GASAR TA KASANCE:

Abdul: Bugun Zuciyata Ya Canja, Murmushi na Ya Sauya, farin ciki ya Qauracewa ruhina, Damuwa ta mamaye zuciya da gangar jikina, idanuna na rintsewa, nunfashi na yana neman Sarqewa, Saboda Qaunarki ta harbo min wata bomb din nuclear ta wargazamin komai, Soyayyar ki ce zata maidani dai dai, domin Irin suffar kyawun da Allah yai miki, son ki ya chanja min rayuwa, har wasu na ganin zan zauce.

Zuciyata Ta amince dake zatayi rayuwa, domin a yanxu babu wani ruwa mai sanyin da zai kashe wutar gobarar dajin data ruru a cikin duniyar zuciyata a can dai dai layin da na gina miki GRA sai ruwan Soyayyar ki, hadi da sassaken qaunarki, Burina Ki amshi Soyayya ta Sarauniyata.





Abdallah: Amincin Allah ya kara tabbata agareki yake cikamakin kololuwar kyan dake kure dukkanin tunanin zuciyata, Me yasa zuciyata take sonki fiye da rayuwata, me yasa take yawan bugawa da sautin ambaton sunanki, me yasa bana iya zama batareda nayi tunaninki ba? Kinsa so ya zamo abu mai matukar sauki agareni, Kasancewarki atare dani shine garkuwar dake yaye duhu wanda ya kafa sansani a cikin birnin idaniyata wadda take son yin tozali dake akowanne lokaci, Nazo gareki yake yar babban gida domin na gabatar da sallmar girma wadda da fito daga cikin kasan zuciyar da ta girma a cikin duniyar sonki. Sallama agareki yake ta farkon ambaton bakina da sonki na saba hakan yasa nake da tabbacin cewa zan samu Soyayyar ki, na miko qoqon barata ina jiran samun ruwan sanyin da zai kashe wutar sonki a Zuciyata. 





Saleem: Ranar dana fara ganinki zuciyata ta fada a cikin duniyar sonki, Ina matukar jindadi dana fada a cikin tekun kaunarki yake mai kyau, Akoda yaushe kina a cikin tsakiyar ruhina kin kawo haske wanda yake haskaka zuciyata ina sonki ne daga can tsakiyar tekun zuciyata, zan so ki bani kyautar Shugaban qasar zuciyarki. A shirye nake na sadaukar da dukkan motsin kabobin jikina tare da fitar numfashi na agareki, Soyayyarki agareni batada karshe ko kuma tsufa domin ako da yaushe ina miki kallan sarauniya, Zani iya aikata komai akan sonki kawai saboda na sakaki farinciki amatsayin ki na sarauniyar zuciyata na baki duk wata yarda ta: saina dameki zan gama cika namiji ina fatan kina da tausayin da zaki kalli buqata ta.


To masu karatu, kunde ji irin yadda Mazaje Uku suka Zazzago Kalamai masu Ratsa Zuciya. 


Sai kuyi musu Alkalanci.


Wanene Zata Bawa Zuciyar💙 Ta?????




Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)