KALAMAN SOYAYYA 2022

0
KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYAR MASOYA YAU MUKA KAWO MUKU, KUMA MASU TSAWO DOMIN SANYAYA ZUCIYAR MASOYAN KU.

💙ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA💙
Domin  bayyana yadda kake ji akan Abunda kake So Da Qauna. 

Kun san ita Soyayya Kullum ƙara sabuntata ake akai akai, dan haka ku sabunta taku.


Kamar Haka:

1. Indai muna tare da juna, Zamu rayu cikin aminci, kasancewarki acikin Rayuwa ta ribace babba kuma wacce bata qarewa. Ina sonki Sosai.

2. Ina farin ciki dake, kuma kina sani Farin ciki, kin chanja min rayuwa, dole na fadawa duniya ke nake so, Na sadaukar miki da rayuwata.

3. Bazan Iya Fadan Lokacin Da na fada Soyayya dake ba, amma daga lokacin dana fara ganin ki nasan ke tawa ce, Ina Sonki.

4. Soyayya Na girma a kowace rana, Ke kika koyamin yadda zan gudanar da rayuwata, Soyayyar ki kamar haske take a samaniya idan kika fito kowa sai ya kalla. Ina Sonki.

5. Ganin ki yana Tabani a Zuciya, Haka Rashin ki Yana Tabamin Zuciya, ke wata kyauta ce da Allah ya Bani acikin duniyar nan. Ina sonki!



6. Idan na kalli cikin idanuwan ki akoda yaushe rikicewa nake, Hasken ki yana sa naji inada sauran rayuwa, ina son ki sani babu abunda zai Fansheki a wurina. Domin kin riQe zuciyata.

7. Akoda yaushe, a cikin ko wani hali, kece mai sani nishadi da farin ciki, ina sonki sosai har Zuciya ta, shiyasa bazan iya wuni guda ba tare dake ba.

8. Baki ta6a rabuwa dani ba, baki ta6a gajiya dani ba, Motsina, Murmushi na, Kuka Na, Muhimmanci na, Koda Yaushe kina tare dani, kina kula dani, ina sonki sosai!

9. Naga Haske a idanuwan ki, Yana haskawa tamkar taurarin dake samaniya yana haskamin haryar zuwa gareki. Ina sonki.

10. Kin san me kika mini. Kinsan me kika fada mini, kin gigice saboda ni! Ko YausheIna mamakin taya haka ta faru, inason ki sani kece mafi girman kyautar dana ta6a samu.

11. Kin fadi abunda nake son ki fada, kinyi abunda nake son kiyi, bansan taya kika aikata ba, amma ya burge ni, nagode da kika kasance cikin rayuwata.

12. Kin bani dalilin kasancewa a raye lokacin da nake cikin kadaici, Har yanxu kina sani sa rai anan gaba, kina nunamin bazan Rayu idan bake ba, me zan nema idan ba ke ba? Zuciyata Mallakin ki ce!

13. Kalaman ki da Dabi'un ki sun chanja ni, Naji dadi ke tawa ce, ni naki ne, wannan shaukin ne yake sakani farin ciki, Sahibata, kece Rayuwata!

14. Bazan manta dake ba, nayi rashin ki a baya, amma yanxu gani kusa dake, zuciyar mu ta zamo daya.


15. Ina Taskake Duk wani lokacin da muke tare, domin shine abun tinawata a Kullum, na ajiyesu kusa da zuciyata, Bazan taba mantawa dake ba.

16. Kin nuna min asalin ma'anar Qauna, yadda take,Da yadda ake jin ta. Ina Sonki!

17. Ranar dana Fara Ganin Ki, Zanen fuskar ki ta ya manne acikin zuciyata. Ranar da kika Fadamin, kina so na, Sunan ki Ya zamo dashe a zuciyata.

18. Bana Tsammanin zan taba iya fadawa Soyayya da wata, kamar yadda na fada Soyayya dake ba. Bansan me nayi na Chanchanche ki ba, amma na tabbatar Zan Bi dake ta hanya mai kyau. You are mine!

19. Nasan Ban Chanchanchi Soyayyar ki ba, amma kina sona, ban kamaci samun kulawarki ba, amma Yau gaki kusa dani kina kulawa dani, Ke Kyauta ce daga Allah. Nagode Abisa duk wata karrawa da kika nuna min.

20. Ana Cewa Ba'a samun abunda ake so, Amma ina jin dadi ina sonki, kuma na sameki yanxu, Soyayyar ki agareni ta wuce darajar Zinare.




21.
Sallama da fatan wanzuwar fariin ciki da annashuwa a tsakiyar kogon zuciyarki ya Zumar zuciyata, jindadi da walwala sune muradin da nake fatan bayyana su a taskar ruhinki, Alawar Qalbina.

22.
Kece daddada kuma zazzakar zumar zuciyata, wacce idan nasha zata haskaka zuciyata tayi fari na taho gareki ki lasa mini zumar kaunayya ko zan samu yalwatuwar farin ciki dauwamamme a cikin birnin zuciyata. 

23.
Bana bukatar komai a yayin da nakejin yinwa face murmushinki Hadi da Zafafan kalamanki kuwa sune ruwan shana Wanda idan nasha nakan rabu da kishin ruwan dake addabar zuciyata.

24.
Kina da kyakkyawar kirar jikin da babu irinki, Kin iya kwalliya tamkar dawisu, Zakin murya kamar kanari, takawarki lafiya mai tafiyar Qasaita tamkar jimina kin isa ne dole ki yi domin duniya ban ga kamar ki ba ko kusa babu, ba aiba kuma ba za ai ba.

25.
Rayuwata, na dauki amanarki daga nan har izuwa ranar tashin alkiyama, Ke dai bari kawai ki sha kuriminki ni na ki ne ke tawa ce kuma mun riga mun yi alkawari, ni da ke jiki biyu ne muka zama rai daya zuciya daya, ba rabuwa har abada wannan shi ne alkawarina fatana ga mahalichchinmu ya cika mana burinmu. 

26.
Sarauniya rife bakinki ba sai kin ce komai ba zuciyarki da gangar jikinki da kyawawan fararen idanuwanki su riga sun sanar da ni irin tsananin son da kike min don haka kwantar da hankalinki ba sai kin fada ba na san ba zai kwatantu ba ke dai samu guri mai kyau a cikin zuciyarki ki kara boye ni kawai domin ni na ki ne ke kadai

27
Duk lokacin dana kwanta sai ina yawan ambaton sunan ki, tinanin ki yakan mamaye hankalina ya bar min sarari don numfashi kuma ina son shi haka. Farin cikin da na samu na tuna ki a cikin zuciyata ya ishe ni iskar oksiji a gare ni in tsira. An halicce kine dan ni kadai. Allah ya zabe ki don kin dace da sararin samaniya na kauna a cikin zuciyata. Yanzu na cika Mutum mai iko domin ina da ke.

28
Babu wata shakka a cikin zuciyata cewa ina Æ™aunarki Æ™warrai da gaske. Ina fata zan iya gina maÉ“uÉ“É“ukar da take zubar da Æ™aunatacciyar Æ™aunata domin ke don ki san irin Æ™aunarki da kimarki agareni. 

29


Qaunar ki a cikin zuciyata tana ƙaruwa a cikin kowane second na rayuwata. fuskarki kyakkyawa ce wacce idan zan ambata, kuma halayenki masu kyau ne idan Za'a bada labari, soyayya ce take sa ni murmushi a duk lokacin da na gan ki. Ina son ki zuciyata.

30
Sonki baya gushewa, ya ba ni mamaki. Na kasance ina mamakin wace irin halitta ce ta musamman da Allah yayi, Hanyoyinki suna da Kawu cike da ban sha'awa, tausayi, Burgewa. Dole ne in zama mafi sa'ar da na same ki.

31
 Ke tawa ce kuma babu abinda zai taba raba ki da ni. Kece farincikina, soyayyata da duk abinda yake sanyaya zuciyata. Ina son ku da dukkan zuciyata. A fuka-fukan kauna, ke tawa ce muna tashi tare kamar yadda tsuntsayen soyayya suke kaiwa zuwa matakin qarshe na Shauki inda muke morewa cikin soyayya da tausayi. Burina ya cika; kece farin cikin dana samu a rayuwata. Zo ki zauna da ni har zuwa karshen lokacin da Zanyi a Duniya. 

32
Kullum ina son kasancewa tare da ke a kowane lokaci. Duk lokacin da nake tare da ke, nakan fi dariya. Don Allah koyaushe ki kasance tawa, har abada don haka zan iya ganinki har abada cikin soyayya. Ina Sonki da tausayinki. 

33
Babu labarin soyayya da ya wanzu ba tare da zafin rai ya gauraye da farin ciki ba, muna iya yin rigima ko rashin fahimta da yawa amma hakan ba yana nufin ba za mu iya dawowa tare ba. Qauna ta gaskiya ba koyaushe take da laushi ba, amma duk da haka ba ta da tsauri. Baby, don Allah ki kasance tare da ni har abada. Ina son ki.

34
Ba zan iya tunanin yadda rayuwa za ta kasance ba tare da ke a rayuwata ba. Kin shigo rayuwata don tayar da ginshiƙan farin ciki a ciki. Tun lokacin da kika zama tawa, bani da wani dalili daya sa ni bakin ciki. Yanzu na fahimci irin sa'ar da zan samu wani abin almara mai kama da ke a rayuwata. Ina son ki babyna.

35
Babu wurin da zai rike sunanki har abada ba tare da an wanke shi ba. Na rubuta shi a yashi, an share shi, a kan dutsen har yanzu ban sake samu ba sai na fahimci cewa mafi kyawu kuma mafi aminci wurin rubutun sunanki shine zuciyata. Ina son ki Sarauniyar zuciyata!

36
Idan da ace ina son abu biyar, zan so kasancewa tare da ke har abada, ganin kina murmushi kowace rana, Ina fatan jin kasancewar ki a kowane minti na rayuwata. Ina so in taba ki in sumbace ki har abada kuma ina son in zama naki har zuwa ƙarshen zamani. Ina son ki.






Ku kasance cikin bamu Gudummawa muna godiya.



Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)