KALAMAN SOYAYYA 100+

0
100+ SHORT LOVE MESSAGES
SAƘONNIN SOYAYYA 100+ 

Wasiƙun soyayya suna da matuƙar tasiri wajen Ƙara danƙon soyayya, wasiƙun soyayya suna da amfani ga rayuwar masoya budurwa da saurayi ko mata da miji. 

Gajeriyar saƙon soyayya na iya yin silar kara shauƙi a zuƙatan masoya, Gajerun kalaman soyayya Sukan bayyana tare da zayyana abunda zuciya take ƙunshe dashi zuwa ga masoyi ko masoyiya. Don haka idan kuna son nuna soyayyar ku ga masoyan ku, Yana da kyau kuna aika musu da wasu gajerun saƙonni na soyayya masu ban mamaki kuma na musamman!

Ga Mata: Munyi Wadannan kalamai ne bawai dan maza kawai ba, a'a ku ma mata harda ku, zaku iya canza shi zuwa yadda kuke so. Misali wurin da aka saka "Ke, ki" Sai ku canza zuwa "Kai, Ka". Da sauran su.


Gajerun Saƙonnin Soyayya:

01
Akan ki Na Cirewa Tsun-tsun Soyayya fuka-fukai dan Kada Ya Tashi domin bazan iya rabuwa dake ba.

02
A sanafiyar shigowarki rayuwata na samu farin ciki masu dinbin yawa wanda ko kudi nasa bazasu saya min ba. Ina Qaunarki.

03
Soyayya Sa'a ce, samun ki kuma dace ne amma shigowarki rayuwa ta rabo ne me wuyar samuwa.


04
Akwai tarin hikimomi da Allah ya ajiye wa dan adam acikin zuciyar shi, babbar hikimar da Allah ya bani shine na Samo Soyayyar ki.

05
Zuciya Bata da Qashi Akan iya tankwarata yadda ake so, amma Soyayyar ki baya canzuwa a zuciya ta duk tsananin rayuwa.

06
Zan baki duk abunda na mallaka amma banda raina, idan na baki raina taya zanyi rayuwa dake. Kece Burina.

07
Dake zan rayu har mutuwa ta, zan saka ki a zuciyata iya adadin yawan numfashina.

08
A yanxu ina rayuwa ne kawai dan Soyayyar ki, ki misalta idan babu ke acikin rayuwata ya zanyi?

09
Ina Sonki fiye da yadda naso ki jiya, kuma Soyayyar da zan miki gobe sai tafi ta yau.

10
Soyayyar da nake miki tamkar tafiya ce wacce bata da Qarshe.

11
Kece wacce tamin satar da bazanso a dawo min dashi ba.

12
Na 6ata a cikin Soyayyar ki, irin 6atar da ba mai iya samo inda nake.

13.
Duk iya kwarewata akan Soyayyar ki take aiki. Saboda Ke kadai kawai nake so.

14.
Murmushinki abun nema ne agareni, dariyarki farin ciki ne ta Musamman. Ina Sonki har abada.


15
Bana bukatar taimakon ko wace mace idan bake ba, naki kawai nake bukata.

16
Misalin Soyayya ta shine misalin ruwan teku ne, baya taba bushewa.

17.
Banda nunfashi kece abu na biyu da nake bukata domin nayi rayuwa. Sarauniyata!

18
Farin ciki kamar wani magani ne da baya lalacewa, kuma kowa yana da damar samun shi, misalin ni dake!
19
Kin dauke makullin shiga zuciyata, dan haka babu wata mace da zata samu damar shiga kece Sarauniyar Zuciyata.

20.
Ana fadin dan adam yana yin gamo, ashe ni dake nayi gamo ban sani ba.

21.
Kece kawai zaki iya wadatar dani a duk fadin duniyar nan, ke rabin jiki na ce!

22.
Kamar yadda ake gane farin fulawa acikin jajayen furenni, haka Soyayyar ki take bata boyuwa a zuciyata.

23.
Ina son abubuwa uku agareki, idanun da basa kuka, bakin da baya karya, Soyayyar da bata mutuwa.

24.
Farashin dana dibarwa sonki a zuciyata tashi yake kullum, saboda bana son sayarwa kowa domin kin cancanta.

25.
Na baki mulkin abu uku, zuciyata, Raina da gangar jikina.

26
Bani da kamar ki a rayuwata, karki gujemin, ki kasance dani, zan zama garkuwa agareki.

27.
Na yarda dake, kuma zan zamo gatan ki a rayuwa, ina tare dake iya wuya.

28.
Rashinki maraici ne agareni, rasa ki kadaici ne masoyiyata.

29.
Aminan juna nake so mu kasance, ba abokai ba, domi  mu kasance da Soyayya ta har abada.

30.
Na tashi cikin Soyayya, gashi yanxu ina rayuwa cikin Soyayya kuma kece sila. Ina Son ki!

31.
Idan bakya tare dani ko bakya kusa dani, Koda yaushe kina a tinani na da zuciya ta.

32.
Dadi wuya ni dake babu batun fishi da juna, ko munyi ma mu zamu gyara kammu. Ina Sonki.

33.
Sirrina Naki ne Sahibata, ki kulamin da kanki yadda ya Kamata Hubby!


34.
Na yi miki alkawari zan kasance dake har iya tsawon da nunfashi zai zauna a jikina. Bazan yada ke ba!

35.
Sai dake rayuwa ta za tayi saiti, na gane sai dake duniya zatai min dadin zama.

36
Kin zamo jinin jikina, kece idanun ganina, wanda baya tare damu makiyin mune Hubby!

37.
Na sadaukar miki da rayuwata, kiyi mulkin zuciya ta, Nine gatan ki domin ina Qaunarki.

38.
Hankali na zai kasance a kwance ne ranar dana ganki cikin daki rufe da mayafin amarci, na kiraki da amaryata.

39.
Yau zanyi shela, duniya ta sani cewa kin mallaka min Zuciyar ki, Kuma nafi kowa farin ciki da murna, nagode Aminiyata!

40
Masoyiyata! Qaunata agareki Gaskiya ce, Kalaman dake fitowa a bakina Zahiri ne. Ki yarda dani!
41.
Sautin muryarki nake son nake ji a kullum domin yana sakani shauki, kuma yana sani qara sonki Matata!

42.
Ako wace safiya, na kanyi murna idan na tina cewa kina tare dani a cikin rayuwata.

43.
Ina Sonki, ina Mahaukacin sonki, da gaske nake sonki, zan cigaba da sonki har karshen rayuwata.

44.
Zan fafa ta da koma wanene indai akan ki ne, na bada rayuwa ta ta zamo fansa. Kece Duniyata!

45.
Nayi Sa'ar Samunki Masoyiyata, Ina Sonki Sosai!

46.
Bana Gajiya da ganin Kyawawan Idanun ki masu kama dana matan aljanna!

47.
Matata, ina Sonki, nagode da kika kasance a tare dani!

48.
Na makance akanki, har nakai matsayin da bana gane kowa idan bake ba, Soyayyar ki ta wuce kima a zuciya ta!

49.
Kamar yadda kike sakani farin ciki, dole ne na sakaki cikin aljannar masoya!

50.
Idan munyi Aure, bani da wata fargaba, domin naci zabe, mulki kawai zanyi domin saki farin ciki.

51.
Na kasance a cikin tinani, koda yaushe tinanina yaya kike, burina ki kasance tawa!


52.
Alkawarin mu na nan, ni dake, babu rabuwa, babu yaudara, babu cin amana, kullum Farin ciki Habibina!

53.
Wasu lokutan idanuna suna min gizo da hoton ki, amma nasan zazzafar qaunar da nake miki ne, saboda kece a zuciyata!

54.
Kin shigo rayuwata Yayin da banyi tsammani ba, gashi yanxu kin koyamin yadda zanyi rayuwa ina Sonki!

55.
Ke ta Musamman ce, kece annurin zuciyata, wani lokacin rudani kike dan kwarjini Ina Sonki da zuciya daya!

56.
Bazan gujeki ba, duk yanayin da kika samu kanki ina Tare dake, ki fahimce ni!

57.
Kina Kula dani Yadda ya kamata, shiyasa nake kara qaunarki a zuciyata, saboda haka na dasa ki a zuciyata.

58.
Ke nake so, ke nake Qaunar, Dake Zan Rayuwa, dake zan mutu, Alkawarina Shine Bazan canza ba!

59.
Zuciyata Ke kawai take muradin kasancewa da ita, hankalina Gabadaya ya karkato Gareki Jarumata!
60.
Duk abunda nayi akan ki ki fada musu, sumin uzuri, sonki ne ya janyo min, Da Raina Nake Sonki!

61.
Samun kwanciyar hankalina shine samun ki matsayin matata, nasan bazanyi kuka ba, domin kin zama tawa!

62
Kin zamo bugun zuciyata, bazan iya rayuwa babu ke ba, Zan iya mutuwa akan ki! 

63.
Babu wacce zan iya yiwa Soyayya kamar naki, domin ke kika koyamin yadda ake Soyayya ta gaskiya. Ina Sonki Shalele!

64.
Duk dacen da zuciyata za tayi, indai bata hadu da Soyayya irin taki ba to Qila-Wa-Qala ne!


65.
Allah Ne ya qaddara haduwata dake, babu wanda ya isa ya rabani dake sai Allah, Shiyasa Bana Wasa da Soyayyar ki!

66.
Nishadin zuciyata shine ke, bana iya kuka indai kina kusa dani, ko raina ne ya baci na tina dake Murmushi nake!


67.
Fuskata labarin Soyayyar ki take nunawa, Farin ciki na sonki, inata nishadi ina dariya, Soyayyar ki ta mantar dani quncin rayuwa!

68.
Ina Tattalin Soyayyar ki, saboda ke kadai Allah Ya Bani, kuma bana son ki kubuce min!

69.
Kafun haduwa ta dake, idanuna ciwo suke, kallon farko da nai miki suka warke!

70.
Idan nayi rashin lafiya, jin sautin muryarki yakan zama kamar maganin waraka daga cutar, ina Sonki.

71.
Ina Miki kallon matata tun daga ranar dana yi miki kallon farko!
72.
Dake nake kwana, kuma dake nake tashi a zuciyata dake nake alfahari a bangaren SO da kauna bani da aiki a cikin rai sai na ya bonki.

73
Idan kika leqa Zuciya, zakiga ta cika da Qauna ki, bazan iya cireki a cikin zuciyata ba.

74
 Idan na kalli idanun ki, bana ganin komai sai Soyayya ta, ta mamaye ko ina a zuciyar ki, kin rikeni da kulawa, bazan gaza ba nima. i love you so much baby!

75
Kece zabin da nake bukata kuma nake so, kin sace Zuciya tuntuni, babu abunda kika bari balle wata ta samu.

76
Ina Sonki Sosai, Shine kawai abunda zan iya fada miki, kina sa naji nafi kowa a duniya, ina sonki.

77
Sonki shike yawo a cikin kowacce jijiya da qashin jikina, komai na kalla ke nake gani Soyayyar ki ta daban ce.

79
Kece Duniyata. Lokacina naki ne mallakin kine, ko wani lokaci na sadaukar miki. Babay na!

80
Idan zan iya baki wani abu a wannnar rayuwar, zan baki cikakken damar Auna Soyayyar da nake miki, kika yadda nake cike da shauki da Qaunarki. I love you!

81
Babu wani mai iya bani farin ciki kamar yadda kike bani, Kina Sani Shauki. Kece farin cikina Sahibata

82
Idan zan samar miki wani abu, to zan samar miki madubi domin ki leka cikin zuciyata, kiga yadda kikai juyin mulki acikin ta, kece bugun Zuciyata.

83
Naso ace inada wani qarfi domin tabbatar miki yadda kike ta Musamman a zuciyata, ke wata kalma ce wacce ke zane a xuciyata.

84
Inda Kika tsaya a gaba na, ji nake kamar na sungume ki na zuba a guje, domin Qaunarki.

85
Idanuna ke suke son gani, zuciyata ke take so, Hannaye na ke suke son Rikewa, hancina qanshin ki yake so, Baby, ke ta daban ce.

86
Lokaci idan Babu ke BaQo ne, Rayuwa mai dadi sai dake, zuciya mai zafi babu ke. Kece Sarauniyata.

87
Soyayya ta agare bata Kamantuwa, kalamai sun kadan su zayyana, kawai sai dai nace INA SON KI SOSAI!

88
Aiki na shine Son ki, nafi kowa dacen Soyayyar ki, dan haka bazan rike ki da wasa ba. I love you!

89
Murmushinki Yayi, dariyarki Ba'a magana, Kin iya tafiya, Komai naki mai kyau ne, ina fatan mu Kasance tare.
90
Idan aka bukaci nayi magana akan ki, zan cinye lokacin ina bayanin yadda kike a zuciyata, ina jin dadin a kirani Naki.

91
Kina da Kyakkyawar Zuciya, kinada hali mai kyau, kin cike duk wata qa'idar da takai a qaunace ki.

92
Kin sani jin dadin duniya, kin nuna min qauna, kin kula dani, me kuma zan nema? Bayan kinfi min komai.

93
Kinsa so ya zamo abu mai matukar sauki agareni ta hanyar bayyanar mani da cikakken ingantaccen so na hakika. Nagode my blood!

94
Wajen zubin kwalliya Ke gwana ce, kin cinye gasar kyau da zuciyata ta saka, Ina Mata suke, suzo su kalli sarauniya ta!

95
Ina Baki martaba da jinjina, domin isar darajar ki takai nace miki i love you!

96
Ina gwanin wani ga tawa, ke zan bugawa tambarin girma, domin ki bani sarautar zuciyar ki!

97
Kin saye zuciyata ƴar amana, duk sirrika na kin lamishe su, baki rage min komai ba sai zuciyar, dan Allah karki nisa dani!

98
Matata! Ke kadai nasa a zuciyata, domin ke kika dace da karbar sadakina, na amince a bani ke na bada komai dana mallaka!

99
Nayi mafarkin ni dake mun zama mata da mini, yayin da kike dandana min zumar qaunarki ta soyayya!

100
Rabin jikina! Yau nayi miki nadin sarauta A zuciyata, irin nadin da ba'a taba yi wa wata Ƴa mace ba!

101
Ina son na kasance a gefen ki kullum, domin na rinƙa sauraron sautin muryar ki mai kama da na kanari

, na ringa kallon murmushin ki kamar farin madara!

102
Soyayya ta bata buya, nayi miki alkawari kuma saina cika, ina tare dake sahibata!

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)