SAKON BARKA DA SAFIYA

0
WASIƘUN SOYAYYA NA BARKA DA SAFIYA

❤Good Morning Text Messages❤

SAƘON BARKA DA SAFIYA MASU DAƊI

Aika Saƙon waya na ɗaya daga cikin hanya mafi inganci wajen saka budurwa shauki da nuna mata soyayya.


Ko wanne daga cikin waɗannan saƙonnin Mata suna son samun irin su daga wurin samarin su, kuma zasu saka mace ta gane cewa saurayin ta yana tinanin ta kuma yana ƙaunar ta.


01
Idan Na Kalle ki, Ni Nasan Me Nake Ji, domin Farin cikin da nake shiga, ina Qaunar ki.

02
Gari ya Waye, sabuwar rana ta fara, Ina Farin ciki da Nishadi saboda ina da ke a cikin rayuwata. Good morning dear.

03
Barka Da Safiya, Kyakkyawa, kin Sakaltani da Kulawarki, gashi Yanxu bana Iya rayuwa idan bake, Ina Ƙaunar ki Sarauniyata.

04
Babban Farin cikina Shine idan na Tina Cewa ke Tawa ce har abada, Nima kuma naki ne. Barka Da Safiya Hasken Rayuwata.


Kalaman soyayya na barka da safiya


Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 




05
Barka Da Safiya Buduwar Zuciya ta, Kawai Tinanin ki ne yake Haska min Safiyata.

06
Barka Da Safiya Zuwa ga wacce take sani farin ciki, Ina Godewa Allah da samun ki a rayuwata.

07
Ina jin Soyayyar ki Wata Kyauta ce agareni da ban taba samun kyauta irin ta ba a rayuwata, my super lady. Good morning!

08
Kyakkyawa Ta, kece Abu mafi kyauwun tinani dake zuwa mini a tinani na da zarar na farka daga bacci, kawai ina son nace barka da safiya gareki Duniyata, kuma farin cikina.

09
Abubuwa kaɗan ne suke da daraja a wurina cikin wannan duniyar, ɗaya daga cikin su shine Murmushi ki, my priceless gift.

10
Congrats to me, saboda na Samu Mafi kyawu, Kulawa da Yarinyar da take Saurin Fahimta ta, kuma kece, my love. Good morning!

11
Yau nayi mafarki, Kin kawo mini ruwa mai sanyi tare da wani a hannun ki, wannan abun kuwa shine soyayya ta dana baki, ki riƙe shi kada ki sake. Barka da safiya sahibata.

12
Da Farko Ina Miki Sallama Irin Wacce Na Saba Miki a Kullum, Sannan Ina Miki fatan Alkhairi irin wanda na saba a kullum, kin tashi lafiya, Ya zuciyar ki take? Ta kasance lafiya, ko ta kasance kullum cikin tinani na? Ba sai kin bani amsa ba, bugun zuciyarki zai sanar dani. Barka da Safiya!




13
Gari ya waye, hasken rana ya fito, nima kuma na fito domin cigaba da noma gonar soyayyarki dana saba a Kullum, ina fatan irin dake Zuciyar ki ya kasance dai dai da irin wanda nake shukawa, Domin samun yabanyamai albarka tsakani na dake, Soyayyar ki tasa ni yin hudar da ba tare da garma ba. Barka da Safiya.

14
Akan ki zan iya komai banda Mutuwa, domin ina Son na kasance dake har abada, Nayi rayuwa dake mai kyau mai tsafta, Ina Miki barka da safiya Tare da fatan Zaki Wuni lafiya tare da farin ciki, Ki sani Ina Tare dake kuma Ina Qaunarki.

15
Zuciya Tana son mai kyautata mata, ni kuma tawa zuciyar ke take son ki kyautata mata, ki bata farin ciki. Duk safiya Murmushinki ya ta dani daga bacci. Good Morning my Lady!

16
Gimbiyar Mata Sarauniyar Zuciyata Kin tashi Lafiya, Ina Fata kin tashi cikin farin ciki irin wanda ke saka Annashuwa, Duk da Kasancewar ki a nesa dani, Amma zuciyata ta Kasance a Kusa dake, naso ace duk safiya idanu na dake zasuyi tozali, naso ace Kece mai tashina daga dogon mafarkin dana fada, naso ace Sassanyar Muryarki Mai Zakin Nan Ce Farkon saurarona a ko wace safiya. Barka Da Safiya Shalele na!

17
Sahibata, Na Gwammaci Na Qare Rayuwata baidaya tare dake, Akan Na Kasance Kullum Cikin Kadai ci, yau wata rana ce sabuwa, kuma ina fatan ta Kasance Mai dadi agaremu Baki Daya. Ina Fatan Kina Lfy?




18
Kin Sakaltani Da Kulawarki, tare da Tausayawarki, gashi yanxu Bana iya wuni ban ganki ba, Zuciyata tayi sabo dake irin sabon da bazan iya yankeshi da takobi ba, Barka Da Safiya Qanqarar zuciyata.

19
Babban Burina a Duniya Shine ki kasance tawa, nima na kasance naki na har abada, Wannan ma kawai ya ishen rayuwa My love!

20
Ganin Kyakkyawar Fuskar ko wace safiya Shine dalilin Farin cikina a wannan ranar, Domin Kece Hasken Rayuwata. Barka da Safiya.

21
Ko wace safiyata Farin Ciki ne, saboda wata dama ce ta sake ganin Murmushinki, Da idanuwan ki masu daukar hankalina, da Kyakkyawar Fuskarkia mai sakan Murmushi, tare da sauraron muryarki mai sani Cikin kogon tinanin ki. Barka da Safiya

Saƙo mai dadi kawai wata hanya ce ta nuna soyayya acikin Alaƙa ko rayuwar masoya. Ko da yaushe kuna turawa junan ku.

Please, Subscribe, like, and share for more updates, thanks

Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 


Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)