HANYOYI 16 DA ZAKA SA BUDURWAR KA KO MATAR KA CIKIN FARIN CIKI.

0
HANYOYI 16 DA ZAKA SA BUDURWAR KA KO MATAR KA CIKIN FARIN CIKI

Hanyoyin da zaka bi domin saka burdurwarka ko matarka farin ciki, sannan idan kayi amfani da wannan Shawarin Ba kai babu damuwa aciki Zamantakewar ka da Abokiyar Rayuwar ka.


Idan kaje wajen ta ko ka shiga gidan Su ka ce 'Assalamu'alaikum.

Ka riƙa yawan bata labarai Saboda Allah (S.W.T) ya sanar da mu dan Adam yana son labari.


Ka zama mai yawan yabon ta musamman a wajen da ake kushe ta ka nuna 6acin ranka.

Ka zama mai yawan bata kyaututtuka domin Kyauta tana kara Danqon soyayya.

Ka share wasu daga cikin kuskurenta Ka nuna baka ma san ta yi ba sannan Kuma ka dauka a matsayin abin ya shude kar ka ajiye shi a kwakwalwar ka.


Ka nuna mata tausayawar ka gare ta a fili musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al'ada, ko Rashin lafiya.


Kada ka daukaka abokan ka fiye da matar ka, (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana'a sama da matansu).


Ka nuna mata babu wata budurwa dake gaban ka sai ita tare da nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurin ka.


Ka rika tunawa da ita a cikin addu'arka Hakan zai kara kauna tsakanin ku.


Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kyauta da kake mata kamar siyan abinci  Saboda daman hakkin ta ne ka kawo mata, sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.

Shaidan ne abokin gabar ka ba matarka ba dan Lokuta da dama idan mata da miji suka dan samu sa6ani har ta kai ana maida martani cikin fushi To ka tuna ba daga ita bane shaidan ne ke zuga ta Saboda shi yana mutukar son a yi saki Shi yasa Annabi yace "kada ku tsani shaidan amma ku dauke shi abokin gaba."

Ka dauki abinci ka saka mata a baki Annabi (SAW) Yace "abincin ba cikin ta kadai zai shiga ba zai wuce har zuwa zuciyar ta."


Ka kasance mai yawan yi mata murmushi fara'a domin Manzo (SAW) Yace,"duk wanda ya nunawa matar sa fara'ar sa to dai - dai Yake da yin sadaka."

Ka zama mai yawan neman shawarar ta (wasu suna ce wa ba'a shawara da mata) To ku sani cewa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matan sa.


Karka 6oye mata damuwar ka farin cikin ka ko bakin cikin ka, Domin ita magani ce a tattare da kai.


Kada kayi mata fada alokacin da tayi maka laifi, kabari sai kun samu nutsuwa.


Domin Ganin Post Na Gaba Sai kuyi subscribe, Sannan Ku kasance cikin wannan Page namu www.Qauna.com.ng Gobe Ma Akwai Wasu Zafafa..

Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)