YADDA ZAKI RUBUTAWA SAURAYIN KI KALAMAN SOYAYYA

YAU MUN TABO BANGAREN MATANE, DOMIN TAMBURAN SU NE YAKE TASHI, DAN HAKA KU MORE SOYAYYAR KU, YAYI DA ZAKU SAKA SAURAYI SHAUKI 

Wannan Kadan Daga Ciki Kenan, Zamu na Kawo Muku Update Akan Lokaci, Muna Godiya Da Goyon Bayan Ku garemu.


01
Kayi nasara wajen sace mini zuciya, gashi yanxu ka zamo wani ginshiki a rayuwata wanda bazan iya rayuwa babu kai ba, duk macen data samu miji irin ka tayi dacen da ‘yan mata da yawa basu samu ba, ka zamo fitilar dake haskaka min hanya, kaine ruwansanyin dake sanyaya mini zuciyata, yarda ta a gareka aminci ce, kulawar da kake bani soyayya ce, kaine sarki a fadar xuciyata, ka nuna mini soyayya ta gaskiya kuma na amana, kaine madubin dubawa na a kullum, Nayi zarra cikin mata da yin dace da masoyin gaskiya ina Qaunar ka Sahibin Raina kuma annurin zuciyata.


02
Nayi danasanin Rashin sanin ka a farkon rayuwata, zuciyata tayi rashin mai kwantar mata da hankali a baya, amma yanxu na samu haske daga Allah, shigowarka cikin rayuwata rahama ce daga Allah, Sirrin ka nawa ne zuciyarka mallaki n ace, rayuwar k aba taka bace ta mu duka ce, Qaunar da nake maka bakina yayi kadan ya furta irin shi, son da zuciayata ke nuna maka shine iya abunda bakina zai iya furtawa, amma zuciyata tana yi maka soyayya mai qarfi fiye da qarfin Aradu yayin da take tsawa, hakika kai masoyina ne, kuma zan baka zumar soyayyata. I love You!


03
Koda kowa zai Qi ka, ina tare dakai, bazan guje maka ba koda mutanen duniya zasu guje maka, ina tare dakai har abada, bazan juya maka baya alokacin da kake neman taimako na ba, soyayyar ka a zuciyata ko ruwan Acid bazai iya 6am6are shi daga zuciyata ba, zuciyata mallaki ce agare ka, kaine Zabin Zuciyata, ruhina dan kai yake a cikin jiki na, dan kai nake rayuwa, murmushina naka ne, kwalliyata farin cikin ka ne, tafiyata Qasaitar k ace ina maka gaisuwar ban girma the king of my heart.
Soyayya Text message04
Nayi mafarkin ni dakai mun zama mata da miji, wannan alama ce ta dorewar farin ciki a zuciyar mu, domin kaine zabin da nai wa zuciyata kuma nake son ka zamo uban ‘ya’yana, ka zamo wani girgije dake bawa zuciyata ruwan sanyi dake Kore damuwa a zuciyata, kaine duniyata kuma kaine lahirata, masoyina na sadaukar maka da komai dana mallaka, ka dauke ni a matsayin baiwarka, niko zaka sameni mai cikakken biyayya, lallai soyayya da akwai zaki nikam nayi dace, domin ka dandana min irin naka, dole nan ace maka masoyina, Ina Kewarka a Zuciyata.


05
Rabin jikina kake ka wuce raini, kaine zuciyata ta nuna min, duk wanda ya kushe mini kai ni dashi sai gaba har mutuwar sa, na saka ka a zuciyata kuma bazan cire ba koda duniya zata taru a kaina, kaine iidanuna suke kallo, kaine bangon jinginar xuciyata. Ina sonka fiye da yadda nake son kaina, zan kasance mai rikon amana akan soyayyarka koda bayan ran ka, banason damuwarka, mai son ganin damuwarka ma na tsane shi. Ina sonka!


Akwai Wasu Zafafa Masu Zuwa Ku Kasance Damu. Sannan Ku Tabbatar Kunyi Subscribe Domin Samun Sabbin Kalaman Soyayya a Email naku.


Previous Post Next Post