HANYOYIN DA AKE MALLAKE ZUCIYAR MACE

0
DUK NAMIJIN DA BAI MALLAKI ZUCIYAR MACE BA, RASHIN CANCANTARSA NE SILA
SOYAYYAR ZAMANI
Wasu tambayoyi da ake yawan turo min da ke sa ni yawan nazari in aka yi min su daga ciki akwai :- ina neman shawarar  ina tare da budurwata amma ina son na mallaki zuciyarta ki taimaka min.


Daga cikin tambayoyin da nake yawan sha a hannun mutane musamman matasa da suke son mace amma kuma suke tunanin su mallake ta ko ta halin ƙaƙa. Babbar manufar a mallaki mace, guda biyu ce , imma dai a mallake ta don ta zame masa rakumi da akala a karshe ya azabtar da ita ko kuma ya mallaketa don yana kaunarta ba ya son ta zille masa.

Abin da ke janyo son dole namiji sai ya mallaki mace akwai :-




Rashin Yarda Da Kai:
Sau tari mutum kan nemi soyayyar mace amma ba tare da ya yarda da kansa ba. Wataƙil yakan fito neman soyayyar ne bai ma shirya ba. Rashin wannan tabbas din ne yakan sa mutum ya nemi asirin mallakar mace ko ta halin ƙaƙa don kada ta sille masa kafin ya gama saita zuciyarsa.

kwarya Ta Bi kwarya:
Wani lokacin neman zuciyar mace yana da kyau idan mutum zai yi, ya nemi zuciya dai-dai da shi, don kuwa in aka yi rashin sa’a bambancin matsayi na ilimi ko dukiya ko asali ya gifta, tunanin kai wa ga mallakar wannan zuciyar sai an shiga bin hanyoyi don a mallaki soyayyar mace ko ta wanne hali.






Son Maso Wani:
Da dama a cikin maza kan takura da son matar da suka tabbatar zuciyarta ba ta tare da su. Sukan yi tunanin suna da hanyoyin da za su bi don su mallaki zuciyar ko ta wanne hali. Sau tari ma suna da yaƙinin naci da wasu bin hanyoyi da za su iya tallafo musu zuciyar da koda ba so aciki a sannu ta koma soyayya.


BA DAN AUREN YA ZO BA:
Wasu kuwa kan zo ne da niyyar soyayya, da 6ata wa mace lokaci amma ba da niyyar aure ba, wannan ma yana sa wa a mallaki zuciyar mace don a dau lokaci ana jan zaren soyayyar kafin a watsar da ita. A cikin hanyoyin da namiji zai yi tunanin zai tsawaita zangon soyayyar akwai na mallakar zuciyar mace ta dukkan hanyoyin da ya samu sarari.


Yanayin Da Suka Hadu:
Sau tari namiji kan hadu da mace ba a waje mai tsafta ba, kuma ya san wadanda su ke tare da ita sun kai yanayin da ba za su kirgu ba, amma shi a tunaninsa ya na son ya tsamo ta, ya mallake ta shi kadai. ko kuma ta na cikin masoya; wataƙil ma tana ganiyar farin jini. Don haka ya ke son ya mallaki zuciyarta.


Karanta: YADDA-AKE-SA-BUDURWA-TA-KWAREWA-SOYAYYA


Soyayya Don Allah:
Akwai wanda kan zo neman zuciyar mace don Allah don soyayya marar dalili kawai yana sonta ne kuma ba ya son ta rabu da shi.

Wannan kason na karshe shi ne mai matukar muhimmanci kuma shi ne ya ke buÆ™atar yadda za ka janyo zuciyar mace don samun soyayya me tsafta kuma wadda za ta kai ga aure da samun zuriya ta gari. ÆŠan’uwa mai neman mallakar zuciyar mace ya kamata ka sani cewa ita zuciyar mace ba ta da wahalar mallaka don haka ma ake kwatanta zuciyar da rauni da saurin mallakuwa irin wannan laushin ne ke sawa sau tari ke kai mace ta baro. Babban burin mai son mallakar zuciya shi ne in har haÆ™ansa ya cimma ruwa ya samu:

  • Ladabi
  • Biyayya
  • Juriya
  • Rashin ganin laifi
  • Makahon so
  • Bijirewa kowa
  • Rabuwa da kowa

Da ma sauran damammaki kan wadda ake so na rashin juya baya ko sauraren wani. Wannan da ma sauran abin da zuciyar mai soyayya ke nema duk za su samu a ruwan sanyi in har ka bi wannan shawarar ba tare da ka bi wata hanya ta mallaka ba. Ko da kuwa za ka yi addu’a to bai wuce abin nan da Bahaushe ke cewa “In kana da kyau to ka kara da wanka” ire-iren wannan taimakon suna da tasiri ne don kariya da janyo alheri a zamantakewar.




Soyayya Don Allah:
Duk lokacin da za ka fara son mace ka so ta don Allah kada ka hangi wani dalili wanda zaka so ta don shi. Misali namiji kan ga mace ya so ta, ko don kudinta ko na iyayenta ko asalinta ko don kyanta ko don shahararta ko ma wani dalili na daban. Na taba cin karo da wanda ya zo guna kan yana son mace amma hujjar son nata shi ne matar wane ce in har aka gansu tare suna soyayya to martabarsa za ta daukaka. Wannan ragon dalilin in har aka mallaki zuciyar mace a ciki karshe matar sai ta afka nadama. Amma so don Allah ba abin da ya fi shi saurin mallakar zuciya.


Kulawa:
Mace zuciyarta na Æ™aunar wanda ya kula da ita. Kulawar gaske ba irin kulawar nan da namiji kan yi ba lokacin da ya ke da bukatar mace ko kuma ya ke neman abu a gurinta. Akwai hanyoyi da dama da ya kamata ka nuna kulawarka ga mace. Fuskantar me take so ka kula da ita ta wannan bangaren yana kara sa wa ka mallaki zuciyarta. 

Misali in mai son karatu ce ya kasance kana kula da karatun har ma a kyautar ka akwai littafi a ciki. Haka dai za ka kula da abin da take so. Mace na kaunar wanda ya kula da ita a lokacin damuwa ko lokacin farin ciki wanda ya ke tsaye a kanta a kowanne yanayi. In har zuciyarka ta zama a haka to tabbas ka samu zuciyar mace sai dai a yi fatan ka yi mata adalci.




Kyautatawa:
Zuciya tana kaunar wanda ya kyautata mata. Akwai da dama na kewaye da mace wanda suke bukatar kyautatawa bayan ita wadda ka ke son. Kyautatawar nan ba fa tana da yawa hanyoyin da ake bi amma babbar kyautatawa ita ce ta magana. Zuciyar mace na son kyakkyawar magana mai taushi.

Kyauta:
Kyauta komai kankantarta ta na sa zuciya laushi, musamman daga hannun wanda ake so. Duk arzikinka idan har mace ba ta sonka to kyautarka ba ta da tasiri gunta to amma in har aka samu soyayyarta komai kankanta to anan kyauta ke da tasiri. Mace ba ta son marowaci , ita kuwa da ma rowa ba halin mutanen kirki ce ba. Yana da kyau a iya karfinka ka ke yi mata kyauta lokaci zuwa lokaci.




Mutunta Iyayenta Da ‘Yan Uwanta:
Zuciyar mace ba ta samuwa ita kadai har sai ka hada da samun soyayyar iyayenta da sauran ‘yan’uwanta. Don haka yayin da ka ke neman mallakar zuciyarta yana da kyau ka ke kyautatawa iyayenta da ‘yan’uwanta da ladabi da ja a jiki da kyakkyawar mu’amala.


Gaskiya:
Kuskure ne babba maza ke aikatawa lokacin neman aure ko fara soyayya inda za su fara da karya wai a tunaninsu mata ba sa bukatar gaskiya. Ba haka abin ya ke ba. A soyayya da ake son ta dore yana da kyau a gina ta a kan gaskiya don duk soyayyar da aka dora kan karya to ba ta karko sannan duk macen da ta lura an dora zuciyarta kan karya tana da wuyar juyowa bayan ta bijire.


Neman So Na Gaskiya:
Duk matar da ka nemi sonta ala tilas to fa da matsala. Idan har mace ta nuna ba ta son ka, abu mafi dacewa shi ne ka rabu da ita, don son da a ka neme shi ta kowanne hali, ba ya dorewa, domin ita zuciyar mace ba ta sauyawa a so, haka a ki.




Kowacce kwarya Da Abokin Burminta:
Akwai bambanci da ra’ayi da na matsayi da na zamantakewa da ma na al’ada wanda soyayya a irin wannan yanayi yana da wahalar sarrafuwa. Misali wanda ke rayuwa a cikin gari ya nemi soyayyar mace wadda ta taso a barikin sojoji wanda wannan sun tashi ne a mabambantan muhalli ko wadda ta taso gidan sarauta ko ma wadda ta taso gidan talaka kai kuma gidan masu hali samun zuciya a irin wannan mabambantan matsayi na hana mallakar zuciya cikin sauki.

A karshe ina ba wa maza shawara da su nemi zuciyar mace ta kyakkyawar hanya su so su don zuciyarsu na sonsu ta silar kyawawan halayensu da kulawarsu. Wannan soyayyar ita ke janyo ladabi da biyayya da yi na yi bari na bari har ta kai ka samu dacewa da son nan da Bahaushe ke kira So hana ganin laifi.

Source: Leadership Hausa




Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)