SHAWARI GOMA (10) ZUWA GA MASOYA

0
SHAWARI NE GUDA GOMA GA MASOYA DOMIN TANTANCE SOYAYYA MAI TSAFTA.

Kafun ka fara soyayya akwai wasu abubuwa da yakamata ka lura dasu, kuma ka kiyaye su, mun kawo muku wasu daga cikin.
  • Na farko, kafun ka fara soyayya dole ne ya zamo kana da zabin irin mace/namijin da kake so domin ta haka ne zaka ji dadin gabatar da soyayyar ka, sannan samun wanda kake s0 zai taimaka maka wajen nuna tsantsar soyayya mai hade da shauki, ka lura da kyau domin mutane suna chanjawa, kowa ka gani halin shi daban.
  • Na biyu, kada ka fada soyayya da mutum wanda kasan bazai iya share maka hawaye ba, karka kuskura ka fara soyayya da wanda kasan bai iya soyayya ba, domin zaka sha wahala kafun ka koya mishi, (wannan akan wanda suke soyayya ta zahiri wato soyayyar aure).



Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA

  • Ka guji yin soyayya da macen da baka san asalin taba, ko namijin da bakisan asalin shi ba, domin hakan yakan saka fadawa hanun mutane kamar haka:
    • Yan Danfara
    • Mayaudara
    • Yan Secrete
  • Soyayyar social media tana da matsala sosai musamman ga wadan da suka sha giyar ta, ku guji yin soyayya a social media har sai ka tabbatar da hakikanin mutum, ba wai ganin hoto ko abunda yace ko tace maka ba.
  • Mu lura dakyau domin akwai yan ARO wa’yan da zasu nuna muku soyayya amma suna yi ne don su gwada ku, ko su gwada kansu abisa wasu dalilai nasu.


SHAWARI GA MASOYA
  • Ku kasance kuna yabon junan ku da kalmomin da suka dace.
  • Kada ku yiwa junan ku karya, kuna fadawa juna gaskiya.
  • Kuna nuna kishin junan ku a fili amma ta hanyar da ta dace.
  • Kuna yawan satar kallon juna.
  • Kada kuna jimawa wajen hira musamman a gida.
  • Kada kuna turawa juna Text na kalaman soyayya har sai soyayyar ku tayi nisa, (Har sai kunsan Komai game da junan ku).
  • Duk dadin soyayyar ku da mace, kar kace mata zaka hanata aikata wani abu bayan aure misali, aiki, yawan fita, zuwa gidan biki ko wani abu makamancin haka.
  • Ga mace, ki kasance mai bin umarnin wanda kike soyayya dashi, domin yana qara dankon soyayya.
  • Kuna yawan kyautatawa junan ku, misali Yawan Kyauta.
  • nuna damuwar ku a fili idan wani abu ya samu dayan ku.
  • Mata suna son kullum namiji yana zuwa mata da abunda bata zato na mamaki
  • Domin Samun Kalamai Na Musamman Ku Shiga Nan👉🏼 www.Qauna.com.ng 



ABUBUWA GOMA DA BA'A JUREWA A SOYAYYA


KARKA BARI ANA MAKA WAƊANNAN ABUBUWAN GUDA GOMA 10 A SOYAYYA

Ko cikin Nishaɗi ko ba cikin Nishaɗi ba, dole ne Soyayyar da kuke ta zama da farin ciki acikin ta, ba tarin zafin kai da Daƙushewa ba. Yawancin mutane suna yin Soyayyar da ba Soyayya acikin ta saboda kawai basa son ace musu basa Soyayya ko basa kula mata. Amma yin Soyayya mai daɗi mai cike da Nishaɗi duniya ce mai daɗi.

Kowa ya cancanci Girmamawa, Tausayawa da Nuna Qauna a Soyayya, amma idan masoyiyar ka bata baka waɗannan Abubuwan, to kana Buƙatar sake tinani dakuma sakewa Soyayyar ka Kwalliya da wata daban.

1. MAGANA CIKIN RASHIN GIRMAMAWA

Duk wata Soyayya tana farawa ne da Girmama juna tare da Mutuntawa. Karka bari budurwar ka tana kiran sunan ka, tana maka magana cike da raini, ko tana sa kaji ba daɗi ta ko ta wani hanya. Koda kuwa faɗa kuke yi ba shine zai bata damar raina ka ba ko tayi maka magana cikin rashin ɗa'a dan Kawai bata iya Saita kalaman ta. 

Karanta: FARILLAN-SOYAYYA-GUDA-7

YADDA ZAKA MAGANCE MATSALAR RASHIN GIRMAMAWA.

Idan kana son ka Magance Matsalar Kalaman Rashin girmamawa da Raini acikin Soyayya, To da Farko Ka Fara Bayyana mata cewa baka son Raini Kuma Baka son Rashin Girmamawa. Duk wata matsala wacce baka so ka faɗe ta kuma ka Bayyana ta a matsayin abunda baka so.

Sannan idan kaga anyi maka magana ta raini ka Tambayi Meyasa akai maka kuma me ya jawo haka?.

Yana da wahala mata suyi tinani akan laifin su, amma idan ka Tambaye su dalilin aikata laifi zasu iya gyarawa kuma su bada hakuri harma su gina wata halayya mai kyau. Kuma duk lokacin da suka tina baka son Abu to zasu kiyaye.

Koda ka faɗa musu abunda baka son to ba lallai su canja ba. Wasu sai kace kana son a gyara ko a canja ko a daina sannan fa zasu daina. Kaima Kuma Ana son ka Girmama Kafun a Girmama ka.


2. YAWAN TAKURA DA MAƘALEWA

Idan Kana da budurwa wacce bata barinka kasha iska koda yaushe takura akan abunda bai kai ya kawo ba, to ka ɗagawa abun jar tuta domin takura ba abun bari bane. Yana da Kyau ka Kasa Jure Halin takura musamman mata wanda suke son sarrafa namiji da Soyayyar da yake musu

HANYAR MANGANCEWA

Ka Lura sannan ka gano ta ina budurwar ka tafi takura maka. Akan menene take takura maka. Ba lallai ya zama komai take takura maka akai ba dan haka shina maganin shi ku zauna ku Fahimci juna kuma ka tsawatar akan hakan.

Wasu matan ana Guje musu ne saboda sun fiye takurawa namiji da abubuwan da baya so.


3. RASHIN YARDA

Ƙarin Bayani Akan Girmamawa, Dole ne Yarda Ya Shiga Tsakanin ku a Soyayya in har kuna son tayi muku daɗi. Idan har ka kasa yarda da Masoyiyar ka, ko ka faɗa mata ko ka daƙile Soyayyar kafun Soyayyar tayi nisa. Dole ne dukkan ku kuji daɗi, Sakewa, Da goyon baya a Soyayya muddin Soyayya dan Allah kuke. Rashin Yarda yana kashe Soyayya har lahira Ƙurmus.


4. RASHIN DAMUWA DAKAI

Jin Kun damu da juna abune mai kyau a Soyayya sosai musamma idan anzo wurin taimakekeniya. Idan budurwar ka bata tambayar ka wasu abubuwan komin yawa da ƙanƙanta to akwai alamun bata damu dakai ba. Idan har kana son Soyayyar ku tayi tafiya mai tsawo to ku Nunawa junan ku cewa Idan ba Ɗaya To Ɗayan ma Babu shi. Koda Ba akoda yaushe ba.


HANYAR GYARA

Ku yawaita wasanni na Soyayya da tsokan da sauran su. Kuna nunawa junan ku Damuwoyin kanku. Kuna haɗa kai wajen MAGANCE damuwar da ta tinkaro ku tare. Wannan zai taimaka wajen gyara haɗin kan dake tsakanin ku sannan zai ƙara Soyayyar juna atsakanin ku. Zai sa kuna damuwa da junan ku musamman idan ɗaya baya kusa da Ɗaya.

Ku kiyaye Aibata Junan Ku, Kada ku bari wasu suna shiga Tsakanin ku.


5. BA'A SAKA SAHUN FARKO

Duk lokacin da kuke Soyayya da mace kana sonta kuma tana sonka amma duk abunda za tayi bata saka ka a farko, kokuma tana fifita abokanta sama da kai. To karka Jure irin wannan. Idan kuna Soyayya dole ne mace tana saka ka sahun farko a komai da zata yi, yana daga cikin Soyayya duk abunda za tayi zata faɗa maka ko yaya yake. Kai Sarki ne Ita kuma Sarauniya Yakamata A baka Girman ka.


6. ZARGI

Ba'a Soyayya ba ko a cikin aure zargi na lalata Aure. Duk lokacin da budurwar ka ta fiye jefa maka zargi da shakku a ranka to karka jure kuma ka takawa abun burki domin zargi mummunan abu ne. Komai zata maka sai tasa zargi a ciki. Komai kayi mata sai tayi wani zargi akai. To kai mata bayanin tun da wuri cewa baka so kuma ku tattauna dalilin dayasa take mata waɗannan zarge zargen. 


7. RASHIN TINAWA DAKAI

Budurwar ka itace silar farin cikin ka a Soyayya, akwai daɗi ace kana Soyayya da macen da ta sanya ka a xuciyar ta amma abun Akwai zafi ace mace bata tinanin ka, bata tina ka kullum saidai kai kana tinawa da ita. Idan kai mata magana sai tace ta manta. Karka jure Wannan domin akwai rashin Soyayya aciki. 

Mafi yawancin irin wannan yafi faruwa ne idan mace tana boye maka wasu Abubuwan na rayuwar ta. Da farko ka fara neman sulhu tare da sanin matsalar dakuma yadda zaka shawo kan lamarin.


8. RASHIN JI

Dukan ku zaku ji daɗi idan Kuna Tare da juna cikin farin ciki. Amma idan aka ce rashin ji ya shigo tsakani abun ba daɗi. Karka yadda kana faɗawa mace magana bata ɗauka musamman akan abun da zai amfane ku duka. Karka yarda da macen da bata jin maganar kowa sai zuciyar ta.

Duk time ɗin da Rashin ji ya shigo cikin Soyayya, To Gishiri ne yake yawa daga nan kuma sai Yaji ya ƙara yawa, ana cikin haka Soyayyar zata lalace.


9. RASHIN GOYON BAYAN MAFARKIN KA

Budurwar ka Yakamata ta baka goyon baya 150% idan ana maganar Burin ka na rayuwa da kake son cimmawa. Yana da kyau ka samu macen da zata tsaya tsayin daka wajen tayaka cimma burin ka na rayuwa ako wani irin mataki ne.

Duk wacce bata Supporting ɗin ka akan abunda kake so to bata sonka bata qaunarka, maybe kuɗin ka kawai take so ko wani buƙata tata.


YADDA ZAKA MAGANCE HAKA

Idan Har Budurwar ka bata Supporting ɗinka, kai sai kana Supporting ɗinta sannan kana Girmama nata dreams ɗin. A hankali zata fahimta kuma zata dawo maka da Supporting ɗinka.

Kuma kayi Ƙoƙarin gano menene matsalar daya saka bata Supporting ɗinka. Shin tsoro take ji, ko damuwa ce, ko tana kokwanto ne.


10. RASHIN ƊAUKAR WASU NAUYI

Na Ƙarshe, Yana da Kyau karka jurewa budurwar da bata ɗaukar nauyi wasu Abubuwan da kanta. Misali. Duk abunda zatai maka na Kyauta ko burgewa tace sai ka biya kuɗin ko tace idan baka bata kuɗi ba bazatai ba. Ko Tace sai kayi mata sannan itama zata maka. 

Dole ne mace ta zamo mai hakuri dakuma dangana da duk abunda yazo mata tayi Hakuri dashi komin yaya yake. Ba komai bane sai kaine zaka mata wani abun yakamata ace zata iya da kanta.

Rufewa (Conclusion)

Daga Ƙarshe muna sake Baku shawari da Ku kiyaye Wajen Ɗaukar wasu matsaloli amatsayin Ba Matsala ba, domin ƙaramin abu shi yake dawowa babba. Yiwa tifkar hanci zai taimata wajen Raguwar barna.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)