ABUBUWA GOMA DA MAZA KESO A SOYAYYA

0

  ABUBUWA GOMA DA MAZA KE SO A SOYAYYA


Abu ne na Yau da Kullum da kowa yake yi wato shine kaji ka ƙagu ka cika wani buri naka, ko ka samu wani abu da kake nema a Soyayya, kuma irin abunda kowa ke so.

Bayan Haka, Soyayya HaÉ—aÉ—É—en Abune, wanda kowa dake cikin shi yana da wani Burin da yake son cimmawa ko wani Mataki da yake son kaiwa wato acikin Soyayyar.

Amma Labari mai daɗin shine Yana Yiyuwa ka cimma abunda kake so, ko ka cikawa wanda ke sonka nashi domin yana ƙara danƙon Soyayya kuma yana sa Soyayya ta zamo cikakkiya.


Idan ke mace ce, Kuma kina jin kamar akwai wani Gibi da baki cike a wurin Masoyinki ba, Ko Kuma Kina son Sanin Abunda Maza Suka fi so a Soyayya, Cigaba da Karantawa.

1. Maza Na Son Girmamawa a Soyayya.

Girmamawa yana Nufin Amincewa da Karban Shawari, Hukunci da Kuma Doka ko Ƙa'ida. Yana Nufin Karki yi musu dashi, ko kiyi banza da maganar shi, ko kisashi yaji ya Ƙasƙanta.

Idan Namiji yaji ya samu Girmamawa, to yafi sakin jiki, Sannan zai baki farin ciki da Shauƙi, Kuma zaki zamo jigo a rayuwar shi. Wannan yana kaiwa Soyayya tayi nisa ta ƙara ƙarfi a tsakanin masoya.

Karanta: YADDA AKE FARA SOYAYYA DA BUDURWA

A ÆŠaya Bangaren, Idan Namiji Yaji Ba'a Girmama shi, ko Ana Mantawa dashi, Zaiji Baida Wani Tasiri a Soyayya. Zai na gefe gefe dake, zaiji bakida wani Amfani a gareshi ko a Soyayyar ku.

Wannan Yanayin zai samar da Fushi, Damuwa harma yakai ga Lalacewar Soyayya.

Dan Haka, yana Dakyau Masoya su sanya Hali mai Kyau wajen Yabawa juna da Girmama Juna, Sannan Su Zayyana Duk Wata damuwar dake cikin Ransu da Magana Mai Kyau mai daÉ—i.






You may like: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA

2. Goyon Baya ta Hanyar Rarrashi, Tarairaya ko Tausasawa.

Imagine Namiji ya dawo gida bayan kwashe tsawon lokaci, Da gajiyan Aiki, Jikinshi ya bushe ga Zafin kai. Babu abinda yake buƙata sai Hutawa, amma zuciyar shi na tinano mishi Abubuwan da zai fuskanta gobe.

Sai Matar shi ta tareshi, Ta Rungumeshi, tace mishi ya aiki da Sauransu. Sannan ya fara bata labarin abunda yayi yau, Sai ta Saurareshi, Taji Tausayin shi, Ta mai Kalmai Masu Kwantar da Hankali da Nuna Support.

Wannan Shine emotional support, Kuma Maza Suna Son Irin Wannan a Soyayya sosai Matuƙa.


Maza Basu Cika Nuna Damuwar su a fili ba, amma ba wai hakan na nuna basuda damuwa bane. Har ma, Maza Sunfi Yawan Shiga Damuwa fiye da Yadda mata Suke Shiga Damuwa. Suna son a Fahimce su, Jinjina Musu, Basu Kulawa musamman cikin Lokacin Matsi.

Emotional support yana Iya Zuwa ta hanyoyi da yawa. Misalin kamar Runguma ko Kalaman Tausayawa, ko Tattaunawa mai Tsawo akan damuwar da tinani mai kyau.

Maza Suna Son Mace wacce Zata Sauraresu batare da ta Nemi dalili ba, wacce zata basu shawari ba tare da sun tambaya ba, wacce zata iya kwantar da hankali batare da Tashin hankali ba.

Karanta: HANYOYIN DA AKE BI A DAINA ISTIMNA'I (Masturbation)

3. Son Abunda ÆŠayanku Ke so

Duk Abunda Yake so kema kiso shi, yana Samar da Tushe na Soyayya mai zurfi. Kuso abu mai kyau, ku more tare, kuyi hira tare.

Yakan Ita Zama Soyayyar Yin yawo tare, ko na dafa abinci ko wani abu mai kama da haka.  Whatever it is, having a shared interest with your partner can lead to more meaningful conversations and experiences.

Karanta: ALAMOMIN KAMUWA DA SOYAYYAR GASKIYA

4. Maza Na Son Biyayya

Biyayya, acikin Soyayya, kamar Manne (Glue) ne dake Riƙe Abubuwa tare. Idan ana maganar abunda maza keso a Soyayya, Biyayya Shine a Sama Sama.

Idan kana Soyayya da wata, kuma ka kasa yarda da biyayyar su gareka, zai yi wuya kaji ka sake ko ka samu kwanciyar Hanali acikin Soyayyar. Yarda Shine Komai, idan Wani ya karya wannar Yardan, Tana É—aukar lokaci kafun ta haÉ—e.

So, idan maza suka ce suna son Biyayya a Soyayya, abunda suke shine suna son su gane cewa mace ta sadaukar da kanta garesu kawai, su kaÉ—ai. Suna son su samu farin zuciyar cewa Budurwar su bazata Ci Amanar su ba, ko Yaudaresu ba, ko ta Guje musu zuwa wurin wani.

5. Namiji Nason Yaji Ya Samu Karbuwa.

Idan kina zaune da namiji kuna Soyayya ki kasance cikin nuna masa cewa lallai ya sameki idan har kin tabbatar Aure ne ya kawo shi. Dan Kada ki barshi cikin Kokwanto da tinani na cewa anya ta karbeni kuwa?! Sannan idan kina sonshi to zako iya chanja wani abu da kike danshi zai sa yaji daɗi sosai. Idan har kuna tare da mutum wanda bakwa son zama dashi saboda wani dalili to ku sanar dashi wataƙila ya gyara.
Wannan dalili yasa Acceptance Keda Muhimmanci a Soyayya.
Idan Har kika Karbi namiji a yadda yake na hali ko wani abu daban, zai mayar dake Sarauniya, zai miko gata zai sanyaki cikin kogin farin ciki.

Karanta: YADDA AKE DASAWA MATA SOYAYYA A ZUCIYA

6. Namiji Yana Son Kina Gode Mishi.

Maza Suna son sanin cewa Gudummawa da Ƙoƙari tare da taimako har ma da nuna kulawarsu kina gani kuma kina nuna gamsuwa ta hanyar gode mishi.
Ko yayi wani abun taimakon Family, ko ya gyara wani abu a gida, koda goyon bayan ki yake yi kina nuna mishi godiyar ki a fili.

Idan Kika Godewa namiji zaiji ƙarfin guiwa na sake ƙara miki abunda yake na nuna farin ciki wanda haka kuma zai ƙara ƙarfin Soyayyar ku zuwa wani babban matsayi. Zai nitsuwa da girmamawa zai kara shiga tsakanin ku.

 So idan kina son namiji ya kasance cikin farin ciki always in a Relationships, kana kiyi masa rowan Godiya dakuma yabawa idan yayi miki abun da yakamata ki gode masa. Koda abun baikai na godiya a baki ba, zaki iya nuna mishi alamu na yawan Murmushi ko karya Murya tayi kalan shagwaba da Sauran su.

Karanta: SIRRINKA 21 DAKE SAKA SOYAYYA KARFI DA JIMAWA  

7. Kina Challenging Nashi

Idan Aka ce Challenging ba ana nufin in a negetive way ba A'a Ana nufin in a positive sense, kamar arguing haka na wasa kamar faɗa faɗa duk dai a cikin wasa. Wasu daga cikin maza suna son macen da zatana musu Challenging domin yana ƙara Soyayya dakuma shaƙuwa sosai.

Wani Dalili kuma shine: Wani lokacin rayuwa nada gundura idan aka cigaba da maimaita abu É—aya Kullum, ana son koda yaushe ana Samun É—an Banbance Banbance kaÉ—a haka.

In a relationship where everything is too comfortable and predictable, it can get a little lack in interest. That’s why some men appreciate their partner who challenges them to try new things.

Karanta: ILLOLIN AUREN DA BABU SOYAYYA

8. Kina Bashi Lokacin shi. (Give hime space)

ÆŠaya daga cikin Abubuwan da maza keso a Soyayya shine samun sakewa. Wato suna son wani lokaci kina É—an Share su kaÉ—an kada kina Kunduran su kada kina takura musu yadda zaki fita a kansu. Bawai haka na nufin ki daina kulasu bane, Masu Iya Magana Nacewa FaÉ—a Masoya Hutu ne.

Munufar itace Maza Nason kaɗaici wani time ɗin domin suɗan sake. Duk yadda namiji ke sonki wataran dole yana Buƙatar yaji yaɗan yi nesa dake na wasu awanni har kwanaki amma kina nan a zuciyar shi.

Idan kina son kinaa bashi wannan damar abunda za kiyi shine idan kina yawan kiran shi Kullum to saiki ɗan daina na tsawon sati ɗaya amma kina tura mishi Love Text Message, koda yaushe koda sau ɗaya ne a rana. Sannan ko Ƴar Flashing karki nayi masa.

Samun Space Manufar shi yakan iya banbanta agun wasu mazan, sannan adadin time É—in da suke so Can vary.
Some men may need Æ´an mintuna ne, while wasu kuma suna son kwana É—aya or two to three days for their interest.

You may like: SIRRINKA 21 DAKE SAKA SOYAYYA KARFI DA JIMAWA

9. Maza Nason Kamalar Yadda

ÆŠaya daga cikin Abubuwan da maza keso shien secure partner. Wato macen da zasu iya yarda da ita akan komai.

Wato Maza nason mata masu confident, stable and self-assured. Wanda basa yawan nuna musu rashin yarda ko yawan zargi.

Also, a secure partner itace macen da bata yawan Buƙatar Attention ɗin namiji. Ina Nufin hakan zai baiwa namiji damar maida hankali wajen gina rayuwar da zasu ji daɗi nan gaba, batare da ya sanya tinanin yadda budurwar shi take ako da yaushe ba.

Karanta: ABUBUWAN DA SUKE BATA SOYAYYA

10. Namiji Baya Son Roƙo.

Duk kuɗin Namiji ko walwalar shi baya son mace me yawan roƙo. Shi namiji alamomi ake nuna masa a aikace ba ta hanyar faɗa ba.
Duk mace da take yawan roƙo namiji mafi yawanci Soyayyar su bata wuce wani lokaci. Domin acikin ƙanƙanin time zaiji Kin Isheshi, sannan Soyayyar da yake miki duk ƙarfin ta zaki iya neman kashi 50% ki rasa ina little time.
Ki kame kanki daga roƙon namiji idan har Kina sonshi. Yana daga cikin hanyat da maza ke gane mayaudaran ƴan mata shine yawan roƙo.

Daga Ƙarshe (Conclusion)

Fahimtar abunda maza keso in a Relationship is an important, kuma mataki ne na gina Soyayyar mai tsafta, sannan yana gina strong connection a tsakanin Partners. Duk da ko wani namiji daban ne, amma akwai Kamanceceniya wajen buƙatuwarsu a wasu Abubuwan da suka haɗu akai.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)