ABUBUWAN DAKE JAWO YAUDARA

0

 DAILILAN DAKE SA MATA DA MAZA YAUDARAN JUNA


Yaudara wani Abune wanda idan ya faru da wani yake jin ciwo sosai, harma takai wasu na iya samun cuta kala kala. Yaudara ba abu ne da Za'a iya Gane shi cikin sauƙi kafun faruwar shi ba, sai ansha wahala wajen bincike ake ganewa.

Wani Shi da Kansa yake jawa kanshi yaudara domin ya aikata wasu kura kurai. Wasu kuma Ƙaddara ce daga Allah Tasa ake yaudarar su ba tare da Laifin su ba kuma basu yi zato ko tsammani ba.

Akwai wanda suke yaudara saboda ÆŠaukar fansa saboda wani dalili nasu na an yaudare su ko wasu kuma suna yaudara ne dan kawai suyi NishaÉ—i wato saboda mugunta.

Dalilan dake saka Yaudara suna da yawa domin kowa da Kalar dalilin shi, Anan Mun tattauna akan wasu daga cikin dalilan dake saka yaudara amma waÉ—annan ba duk bane:

1. KwaÉ—ayi

KwaÉ—ayi wani halittace da Allah ya sakawa dukkan bayin shi na son yin wani abu, ko son Aikata wani abu ko son faruwar wani abu ta wata sigar da Mutum ke so da Sauran su. 

KwaÉ—ayi kala kala ne amma wanda muke magana shine KwaÉ—ayin KuÉ—i. Yau idan Kana da kuÉ—i to kai mata suke yayi. Za'a iya maka duk abunda kake so kuma kake kauna indai kana da kuÉ—i. 

Wannan dalilin yasa mata gujewa namiji idan baida kuÉ—i a hannu. Kai ko bakada kuÉ—i indai kana kashe mata abunda ke hannun ka ko yaya yake to kai take yayi.

Suma mazan yanxu sun fara Cewa sai ÆŠiyar mai kuÉ—i inda Za'a kashe musu kuÉ—i saboda surukuta.

Abokina idan bakada Sana'a to ka nema, domin mata Masu sonka duk yadda kake basu da yawa a wannan zamani.

Abisa wannan dalili Muke ganin Kwaɗayi na taka Muhimmiyar Rawa wajen Saka Yaudara a zuƙatan Mutane.

Karanta: YADDA-AKE-GANE-MATAN-AURE-MASU-BIN-MAZA

2. Zugar Ƙawaye/Abokai

Ita dai Zuga wata abace da Jinsin mutane Ke so. A zugaka ka aikata wani abunda baka da niyya ko bakai tsammani ba ko bakasan ma kayi ba.

Zugar Mutane mafi yawa yana Zuwa ne daga bakin Abokai da Ƙawaye, Musamman idan wani abu na shirin faruwa dakai na farin ciki to ana zuga take tashi.

Saidai Zugar wasu na yinta akan abun kirki ko na banza. Wasu su zuga mutum ya aikata Laifi ko ya Gujewa laifi ko ya Rabu da Wani abu da yake so saboda mugunta.

Zugar da Muke magana akai Itace Zugar ƙawaye da Abokai wanda suke saka mace ta gujewa saurayinta saboda baida kuɗi ko iko ko kyawu ko dan Taga wani.

Mafi yawanci idan mata na Soyayya da saurayi zugar ƙawaye nasa su guje masa saboda ƙawa tace mata akwai wanda ya fishi koda kuwa Soyayyar gaskiya suke. Domin ƙawaye a wani sigar Suna bada Gudummawa wajen raba kan masoya.

Karanta: ABUBUWAN-DA-SUKE-BATA-SOYAYYA

Idan Har zaka Ɗauki Zugar ƙawaye to Kana Ruwa. Shi zugar kawaye gani ake kamar yafi na kowa, idan Ƙawa ta zugaki sai kiji kamar tafi kowa sonki. Hankalin ki da Tinanin ki sune zasu tabbatar miki gaskiya idan har kina su kenan.

Mafita shine ki guji Ƙawa da Zata na kawo miki Shubuha akan lamarin rayuwarki. Ki Rungumi Ƙawar da take baki shawari na gari wacce take tayaki kuka da Farin ciki.




You may like: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAÆŠUWA

3. Hassada Don Ana Son Saurayin Ƙawa

Hassada Na Iya Sa Ayi Yaudara. Wata zata ga Saurayin Kawarta taji tana sonshi. Daga nan sai ta fara gujewa wanda take dashi. Acan kuma wajen ƙawar tata, shawari zatana bata gurbatattu kawai saboda ta rabata da Wannan saurayi itakuma tayi Wuff dashi.

4. Rashin Iya Soyayya

Rashin Samun Ilimin Ƙwarewa a Soyayya na iya Janyowa ayi yaudara. 

Kasan Damuwar Abokin Soyayyar ka, kasan me yake so, kasan abunda baya so, sannan ka guje ma abunda baya so, kana aikata abunda yake so.

Kasan hanyoyin da zaka ƙarfafa Soyayyar ka Irin Abubuwa na ban dariya dana Tayar da Shauƙi, Kalaman Soyayya masu Ratsa Zuciya.

Indai Kana Soyayya Kuma Rana zata Fito har ta Faɗi Baka Tankaɗawa Budurwar ka Ko Saurayin ki Kalaman Soyayya ba To Akwai Gyara a Lamarin Soyayyar ku Domin Yin Haka Na Ƙarawa Soyayya ƙarfi da Gujewa Barazanar Yaudara.

Karanta: KALAN-MAZAN-DA-MATA-KE-SO

5. Rashin Saka Iyaye Cikin Soyayya

Idan Zakayi Soyayya dan Allah To Ka tabbatar ka saka iyayen ka ciki don gudun yaudara. 

Wasu matan suna gujewa maza ne saboda basu da tabbaci cewa wannan saurayi zai Aureta ko A'a. 

Wata kuma gidan su ne Za'a ce ya turo amma sai yaƙi turowa, daga Nan Iyayen ta Zasu hanata kulashi koma su koreshi.

Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-DAWO-DA-SHAUKI-CIKIN SOYAYYA

6. Rashin Sana'a 

Idan Namiji Baida Sana'a Mata basa bashi Attention dama. Idan kaga mace ta tsaya maka alhalin bakada Sana'a To Ka binciki gaskiyar Soyayyar ta domin idan Ba Sana'a Aure Bazai zauna ba saboda Ita Yunwa batasan Menene Soyayya ba.

Duk Namiji da Baida Sana'a idan Har budurwar shi ta samu wani to Soyayyar su fa Sadai Kariyar Ubangiji Amma sai tayi Rawa da Tangal-Tangal. Kuma wataran saita Guje mishi.

Karanta: ABUBUWAN-DA-MAZA-KE-SO-JIKIN-MATA

7. Girman Kai

Mata masu girman Kai Suna Saurin yaudara Kuma Ana Saurin yaudarar su. Idan mace tana da Girman Kai Ko ta amshi Soyayyar ka bazaka ji daÉ—in yin Soyayya da ita ba domin ÆŠagawar ta zatayi yawa. 

Shi girman kai Idan yayi yawa Yana Bata abubuwa da dama sosai. Daga Cikin abunda girman kai ke janyowa Akwai Raini Duk Soyayyar da raini ya ratsata kuwa Bazata haifar da ÆŠiya mai ido ba.

Karanta: HANYOYIN-DA-ZAKA-NUNAWA-MACE-SOYAYYA

8. Ruwan Ido

Ruwan Ido a Soyayya musamman ga ÆŠiya mace matsala ce babba. Domin yana sanya mace taÆ™i Auruwa akan lokaci. Dalilin hakan kuwa shine Ruwan Ido Na Sanya Yaudara. 

Ruwan Ido nasa Mace Tara samari Da yawa Sama da Guda ÆŠaya, Kuma duk bana Aure bane Kawai Ruwan ido ne da yayi yawa sai ta rasa waye zata zaba, Inda daga baya sai kaga duk sun guje mata.

Duk macen da take tara samari kuma anai mata kallon Ƴar iska saboda Macen Kirki An san Bata Tara Samari Da Yawa Haka. 

Duk Saurayin Da ya fahimci Budurwa nada Ruwan Idanu Indai Aure ne ya kawo shi To zai Gujeta daga Nan An shiga Layin Yaudara.

Karanta: YADDA-AKE-GANE-MATAN-AURE-MASU-BIN-MAZA

9. Æ˜arya

Ƙarya dai Koda Ba'a Soyayya bama tana zubar da mutunci balle kuma a Soyayya. Yin Ƙarya a Soyayya ya kasu kashi biyu.

Akwai Ƙarya Akan Abunda aka Mallaka misali: Saurayi yazo wurin ki ya ringa ce miki Yana da Mota shi mai kuɗi ne, yana da gidaje Alhalin Baida ko ɗaya daga cikin Abubuwan daya Faɗa miki.

Ƙarya Na Biyu Shine Ƙaryan Soyayya. Zaizo miko ne ta sigar yana sonki Amma kuma Ƙarya yake Yaidarace ta kawo shi. Duk wani Magana mai daɗi da kike son ji ya iyata bazaki taba iya ƙureshi ba saboda ya ƙware sosai.

Da zarar kin FaÉ—a Tarkon shi sai ya guje miki. 

Mafi yawa Ana Yiwa Mace Ƙarya ne idan Itama Ƴar Ƙaryar Ce.

Karanta: YADDA-AKE-SA-BUDURWA-TA-KWAREWA-SOYAYYA

10. Zargi

Idan Kuka Cika Zargi Acikin Soyayyar ku To lallai zata tsinka Gadar Soyayyar ku da Kuka ShimfiÉ—a. Domin zargi a Soyayya Matsala ce babba.

Zargi Shine Yawan Zato Akan Abunda Kake so Alhalin Ba Haka yake ba. Kuma ya Bata Aure Komin daɗewar shi. Yana saka Ƙin Yarda da Juna Dakuma Yawan Faɗa koda yaushe.

Idan Akace Kun samu waÉ—annan acikin Soyayyar ku to Zata Wargaje, Sai ÆŠaya ya Fara Zargin Cewa ÆŠayan ya Yaudareshi

Koma Menene Ya Janyo Yaudara Duk Dai Ba Daɗi. Ƴan Uwa mu Kiyaye Yaudara.


MANYAN ALAMOMIN SOYAYYA TA GASKIYA GUDA 6


Tun kafun a haifeka ake Mafarkin neman Soyayyar gaskiya. Hatta mutanen da basu yarda da Soyayya ba suna son Soyayyar gaskiya. Amma Saboda ÆŠaya daga cikin Burin ÆŠan Adam shine Samun Soyayya ba shine yake nuna Ansan menene Soyayyar gaskiya ba. Akwai Soyayya kala kala akwai na Kirki Akwai na Banza. Saboda rashin tabbas É—in samun Soyayyar gaskiya yasa wasu basa son ma su kusance ta.

Amma Idan har ka Samu wani wanda yake sonka da gaske, to karka bar Soyayyar Shi ta tafi a banza. Saboda haka, Kana Buƙatar koyon yadda zaka gane Soyayyar gaskiya. Idan kana daga cikin Mutanen dake tsoron Soyayya, to Zaka Samu Ƙarin Ilimi anan Wanda zai Chanja maka Rayuwa. Yana daga cikin Yin Rayuwa mai Ma'ana dakuma daɗi Shine ka samu Soyayya ta gaskiya mai Daɗi.

Zaka Iya Soyayya da mata da yawa a rayuwar ka, amma taya zaka gane wacce ke sonka da gaskiya? Ga wasu kaÉ—an daga alamomin da zakaa gane mai sonka da gaskiya.:

Alamomin Soyayyar Gaskiya:

1. Rashin Fargaba da Tsoro.

Daga cikin alamomin Soyayyar gaskiya akwai Rashin Tsoro ko Fargaban kada wani yayi maka shigan Burtu, ko tsoron Kada Wacce kake so ta yaudare. Idan Har Ka samu kanka a yanayin Da Komai ka Yarda da masoyinka Baka Tsoron zai Gujeka Ko Zai Maka wani abunda zaisa ka barshi, to wannan Na daga Cikin Alamun Soyayya ta gaskiya.

Karanta: AMFANIN SANIN ABOKIN SAURAYI

Duk Jinawar Da za kuyi da mace indai baka jin ta isheka, ko baka jin Soyayyar ta na raguwa daga zuciyar, Kullum saidai kaji Ƙaunar ta na Ƙaruwa Shauƙi Kullum na daɗuwa to wannan Shine ake buƙata. A Soyayya koda bakwa wasanni ko tsokana wa junan ku amma kuma kuna son juna kuna martaba juna kuna kiyaye haƙƙin Soyayya to Kuna cikin Soyayya ta gaskiya.




You may like: YADDA AKE FARA SOYAYYA DA BUDURWA


2. Koda Yaushe Kuji Kuna son Zama Kusa da Juna.

Idan Har Soyayya Tayi Ƙarfi kuma tayi daÉ—i, masoya suna mararin juna ta hanyar son Zama inda masoyi yake kuma suÉ—au Tsawon lokaci tare ba tare da Sun Gundiri juna ba, batare da ÆŠaya najin Haushin ÆŠaya ba, Sannan Duk jimawar da za suyi Zaka gansu cikin Murmushi da dariya, kuma Ba'a son Rabuwa, to wannan alama ce ta Soyayyar gaskiya. 

Karanta: YADDA AKE SOYAYYA DA QARAMAR BUDURWA

Duk Soyayyar da Kullum zaka ga Farin ciki na ƙaruwa ba tare da ya dishe ba, ko kaga duk irin Shaƙuwar da kukai Bakwa yin wani abu da zai bata Soyayyar ku to alama ce ta Soyayyar gaskiya.

Yana Da kyau kasancewa kusa da masoyin ka koda cikin taron Jama'a ne. Kawai kaji kai koda yaushe kafison zama kusa da budurwar ka, idan kun haɗu bakwa son rabuwa koda kuwa Kullum ne. Koda Zaka tafi wuri mai nisa duk Muhimmancin shi amma kaji kaifa zama kusa da ita yafi maka farin ciki da Shauƙi.

Karanta: ALAMOMIN KAMUWA DA SOYAYYAR GASKIYA

3. Kuji Kuna Son Juna Koda Halinku Ya Banbanta.

Ko wani mutum yana da wani halayya wani ya maida shi na daban acikin mutane. Sannan wannan halin kuma shine zaisa ba kowa ne yakeson zama kusa dasu ba. Misali, Kai mutum ne mai yawan Ɗaga Muryar idan Kana Magana, wannan wasu basa son haka, Abokan ka da ƴan uwanka ne kawai zasj iya zama dakai a haka. Amma zasu faɗa maka ka rufe bakin ka wato kana magana ƙasa ƙasa.

Karanta: GASKIYAR BAYANI AKAN FATALWA

Amma idan ana Magana akan Soyayya ne, wasu masoyan rabuwa suke idan rashin jituwa ya shigo. Idan Har ka samu masoyin gaskiya to duk yadda kake zaiji kawai ka masa a haka. Harma zaka ga masoyin naka shi zai taya ka ku gyara abunda kake batawa. Wannan Shine Soyayya ta gaskiya.

Karanta: YADDA AKE DASAWA MATA SOYAYYA A ZUCIYA

4. Kuji Kuna son ÆŠayan Ku Yayi Nasara.

Kaji kana son Masoyin ka Yayi nasara a komai da yasa a gaba don cimmawa. Kaji ka Æ™agu kana so, Zaka iya jin zafi idan baiyi nasara ba to wannan Alama Ce ta Soyayyar gaskiya. 

Idan har ka kasance Wanda yake son cigaban masoyin shi amma baka Taimaka mishi ta hanyoyin da suka dace to wannan ba Soyayya bace. Soyayyar gaskiya shine ka tallafawa masoyin ka wajen Cimma burin shi na rayuwa.

Karanta: HANYOYIN-MALLAKE-USTAZAI-MAZA-DA-MATA

Idan Har Kana Soyayyar gaskiya zaka iya yin duk abunda ya kama kayi wajen nemowa masoyin ka abunda ranshi keso batare da ka gajiya ba. Zaka iya sadaukar da naka farin cikin domin nashi.

Soyayyar ku zata Kasance Akwai Fahimtar juna, Akwai Goyon Baya, Sannan Akwai Soyayya daga Duka Ku Biyun. Zaku Girma tare Soyayyar ku Tayi Ƙarfin da Zaku kai ga Aure.

Karanta: YADDA-AKE-GANE-SIFFOFIN-SAMARI-MAYAUDARA

5. Jurewa Zafi, Damuwa, Ƙunci da Sauransu.

Mutane da Dama Yana wahala Su iya Fuskantar Damuwar su. Koda Suna Cikin Dangi Da Abokai. A Soyayya Ana Son ka zamo mai jurewa duk wata rayuwa ta wahala ko Ƙunci da damuwa.

Idan Har ka samu wacce kake so da gaskiga, za kana buÉ—e mata zuciyar ka, bazaka boye mata komai ba. 

Ba komai ake Boyewa a Soyayya ba sannan ka zamo mai Hakuri yana bawa Soyayya tasiri mutunci da Shauƙi.

Sannan bazaka na jin kunya ko Tsoron FaÉ—awa Masoyiyar ka damuwar ka ba, haka Itama bazata boye maka komai ba.

Karanta: YADDA-AKE-SA-BUDURWA-TA-KWARE-SOYAYYAR KA

6. Za Kana Mafarkin Rayuwa Mai Zuwa.

Idan Kana Yin Soyayyar gaskiya zakana Tsammani ko Rayawa a ranka cewa nan Gana Ga yadda zaka kasance da Ita, Sannan Zaka kana rayawa ga yadda rayuwar auren ku zai kasance. Sannan Duk wani Plan na Rayuwar ka zakana sakata a ciki. 

Idan Mutum biyu na Soyayya ta gaskiya, Baza suji kunyar yin Irin WaÉ—annan Tinanin ba. Da kanku zakuna gina irin rayuwar da za kuyi nan gaba ko nan da wasu shekaru.

Karanta: HANYOYIN DA AKE BI A DAINA ISTIMNA'I (Masturbation)

Rufewa

Soyayyar gaskiga wani abu ne da kowa ya samu yayi dace. Ba kowa ke samun damar kasancewa da Soyayyar ba. Sannan ba kowa ke son FaÉ—awa wani sirrin shi ba. Sannan akan iya rasa Soyayya gaba É—aya idan har bata gaskiya bace. Idan Har kana kokwanto akan Soyayyar ka karka bari shakka ya bata maka ita.

Yin Soyayyar gaskiya na Nufin son zama kusa da juna, son sanin komai akan wanda kake so, Son Cimma buri ko Son Masoyin ka ya samu abunda yake so, kayi sadaukarwa domin farin ciki. 

Kaso Wani abunda take so, Ka kauda kai akan halaye maras kyau. Kaso ku kasance tare A Lokuta masu zuwa. Kuyi aiki tuƙuru wajen cimma burin ku Tare.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)